29

968 29 0
                                    

💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫

      

            ✍️ M SHAKUR



                        2️⃣9️⃣


FREE PAGE
Hayaniya da zata iya cewa tunda take a asibitin bata tabajin irinshi ba, hayaniyan ya mugun cika mata kunne yasa tabude idanunta ahankali tana kallon dakin, idanunta sunmata shegen nauyi sabida bacci bai isheta ba, sosai kirjinta taji yana wani irin faduwa, ward din datake gabaki daya ta kalla babu kowa cikin ward din sai ita kadai dake kwance akan gadon an lullubeta da bargo sanan anmata parking gashinta gabaki daya anyi mata parking na ponytail, ihu dawani irin masifa dataji yana sauka akan kunnenta yasa ta yaye bargon jikinta ta tashi zaune dagakan gadon tana kalle kallen dakin, ihu da hayaniya da masifan da akeyi jitake kaman a brain dinta akeyi, sakkowa tayi dagakan gadon tazira pink slippers dinta dake wajen sanan tadau Teddy dinta ta kankameshi akirjinta ta shiga tafiya ahankali kaman ana kiranta, hannu tasa tabude kofar dakin datake tafito tana tafiya dogon jelar gashinta na lilo tana kankame da Teddy ta kaganta kaman kasace ta kagudu, tai bala'in kyau doguwan yarinya da ita, batada wani kiba tana sanye da gown din asibiti daya wuce guiwanta da kadan, batada wani cikan kirji sosai, kirjinta moderate yan daidai irin na yaran larabawan nan, kanta an mata parking an daure da ribbon gashin na lilo, tundaga nesa take hango su Ammi, Mama da Mom na hayaniya dayasa ta tsorata tasake kankame Teddy gam gam idanunta na kawo kwalla dan tsoro taji sun bata hakan yasa ta shiga waige waige tana neman Waleed, fitowa tayi daga corridor ta shiga tafiyanta kaman bana mutum ba a reception din su Mom ko kadan basu lurada itaba, tunawa da ranan Waleed yayi kofa da ita yafita da ita yasa tai wajen kofan da sauri tana cikin tafiya kaman ance ta kalli glass din kofar emergency ta hango Waleed kwance kan gado fuskarshi a kumbure yasa tai dakin da sauri, hannu tasa tabude kofan ta shiga duksu Ammi basu lurada itaba, maida kofar tayi tarufe, ganin ciwo ajikinshi yasa tawani irin saki Teddy ta akasa tai kanshi da sauri, hannayenta tadaura kan cikinshi tabude bakinta tana kokarin ma magana takasa sai kawai tasaki kuka sosai tahau jijjigashi, amman bai motsa ba, kai hannunta tayi ta daura kan gefen idanunshi daya kumbura suntum ta taba tana kuka sosai tanaso tai magana tama kasa, bama tasan sunanshi ba amman sotake yabude ya kalleta, girgiza shi tayi tace "ahhhh, Umm mm" kafadarshi mai lafiya ta bubbuga tana kuka da kyar bakinta ya iya furta. "you, youuuuuuu, yo.....u" tasaki kuka sosai kaman zata mutu saikuma tadaura kanta kan kirjinshi tahau kuka tana jijjigashi tace "youuuu" sosai take kuka, takai kusan 5min ahaka tana kuka tana jijjigashi sanan tadago kanta ahankali ta kalli fuskarshi saikuma tajuya ta kalli TV dakin dake aiki da babu kara ko kadan dan anyi muting television din, tashar AIT ke aiki suna wani series na Korean film.



Daidai wata yarinya tashigo dakin wani namiji mara lafiya tana kuka tana zuwa kawai ta duka ta daura bakinta kan nashi sai saurayin ya farka, tana ganin haka da sauri tana kuka ta kallai, kafin ahankali tana kuka sosai takai fuskarta saitin nashi tana kallon fuskarshi yana mata wani irin kwarjini ta kafe pink lips dinshi da ido kafin ahankali ta saukar da bakinta kan nashi, tasaka all his lips inside her tiny mouth  tai shiru tana kallon idanunshi ita adole tana jira yabude ido shima kaman na film hawaye na zuba daga idanunshi.

Kaman acikin mafarki yaji saukar wani tattausan lips kan nashi, bude bakinshi kadan yayi yay grabbing those soft tender lips yashiga kissing dinsu kaman zai cinye bakin, yatura tongue dinshi cikin bakinta yana lasowa kasa daurewa yayi yamika hannunshi trying to grab something yaji yakama mutum, ahankali yashiga bude idanunshi dasukamai nauyi kaman banashi ba, dishi dishi yake gani saikuma idanun suka washe tarr, ido da ido yayi da Widad da bakinta ke cikin nashi har lokacin bai dena kissing dinta ba idanunta sunyi jajir tsabagen kuka tana kallon idanunshi kuri kaman wata mayya, wani irin sakin lips dinta yayi da sauri yacire lafiyayyen hannunshi daga bayanta yaja jikinshi yakoma baya da sauri yana kokarin tashi zaune yana kallonta still, mikewa tayi itama tsaye takai hannunta kan idanunta tana share hawayen daya kasa dena zubowa sanan ta taho da sauri tazauna kan gadon tafada jikinshi ta rungume ta hanyar daura kanta kan kirjinshi tana kuka sosai, rasama mezai mata yayi hakan yasa yakai hannunshi mai lafiya yadaura akan bayanta yadan bubbuga alamun tai shiru sanan yatureta daga jikinshi ta tashi, hannunta ahankali takai ta daura kan wuyanshi dayaji ciwo tana turo baki kafin ahankali bama tasan tayaya maganan yafito daga bakinta ba tace "so....ry" gyadamata kai yayi cikeda dauriya, sanan ya tsareta da idanu, saikuma yace "who thought you how to do that"? Yanuna mata bakinshi, juyawa tayi kaman wata yar yarinya ta nunamai TV da yatsan ta hakan yasa ya kalli TV, Korean film yaga anayi yasan tunda ta nunamai wajen yasan anan tagani, shiru yayi yana kallonta, muryan Ammin shi dayaji yasa ya kalli kofa da sauri, faduwa gabanshi yayi, hakan yasa ya kalleta, dagata yayi tamike tsaye, anatse sabida tagane cikin harshen turenci yace "inaso kidauki Teddy ki ki koma dakinki kinji Saheeba, anjima kadan zanzo wajenki, now be a good girl and listen to me and go" makemai kafada tayi tafashe da kuka, girgiza mata kai yayi kaman zaiyi kuka yace "please Saheeba kitafi, yanzun nan zanzo kinji" sake makemai kafada tayi tana kuka, ahankali yasanya hannunshi ya jawota jikinshi rungumeta yayi tareda bubbuga bayanta a kunnenta yamata whispering yace "listen to me, please Pretty go, I don't want Ammi to see you here, please pretty go" yay maganan tareda dagota ahankali, fuskarshi ta kalla ya gyadamata kai hakan yasa ta sauka ahankali daga kan gadon, daukar Teddy dinta tayi sanan tajuyo ta kallai shima kallonta yake kaman yau yafara ganinta, ahankali tasa hannu tabude kofar dakin tafita tamaido kofar tarufe yana kallonta, ta glass din kofar yacigaba da kallonta ahankali take tafiya ta kankame Teddy ta, tai corridor dazai sadata da ward din da aka kwantar da ita. Ajiyan zuciya ya sauke tareda lumshe ido yadaura hannunshi kan fuskarshi kafin yasauke hannun kan bakinshi yay shiru yana tunanin what just happened.




*******



Within 30min IGP yayi deploying police zuwa address da Ammi ta tura mai. Knocking Gate din gidansu Arham one of the police men yayi, fitowa daga daki maigadi yayi yaleko, ganin police ne yasa yace "bayin Allah wakuke nema"? Wani daga cikinsu ne yace "Goodday please we are looking for Mr Arham" mai gadi da tuni jikinshi yahau bari ganin yan sanda yasa yace " yes gidan nan ne gidan Mr Arham" daya daga cikinsu policeman dinne yace "is he in"? Ware ido mai gadin yayi dan baigane turencin ba hakan yasa daya daga cikinsu yace "yana nan? Da sauri yace "yes.....eh,yana nan, yanzun nanma ya shigo gidan" "kaimu wurin shi" da sauri yajuya yay gaba suna biyedashi abaya har flat dinsu yabude kofa yashiga suma haka, a palour suka sameshi ya daura kafa daya kan daya yayi resting head dinshi a kam one seater kujeran dayake zaune akai hannunshi rikeda chilled maltina, jin mutane akanshi yasa yadago yana kallonshi, babban su ne yace "good-day  Mr Arham we are here to invite you to our office for some questioning" yana gama maganan yafito mishi da ID card dinshi ya nunamai, bin ID card din yayi da kallo sanan yatabe baki yamaida kanshi kan kujeran yana girgiza kafa, kara maimaita mishi maganar sukayi but no response still saima maltina shi daya cigaba dasha, mai gadi ne saya gama tsurewa yace "Alhaji dakai fa suke" dago kanshi yayi ya musu wani irin kallon banza yace "what questioning"? Cije lips policeman din yayi yace "when you reach our office you will find out" "and where is your office located at"?

Shiru police din yanasa baicemai komiba dakin ya tsit, maigadi dake shirin sakin fitsari yace "Alhaji kabisu kar su maka wani mara kyau, kagan sunata binka ahankali tun dazun, kawa Allah kamike kabisu"  y
policeman dinne ya juya ya kalli wasu manyan officers guda biyu da sauri sukai heading directing to kujerar da Arham yake zaune. "Sir you are under arrest" fisgoshi daya daga cikinsu yayi ya tayar dashi tsaye Arham bayyi wata wata ba ya dauke policeman din da mari mai kyau, bai ijiye hannun kasa ba yaji saukan mari to ko'ina akan fuskarshi dayaji yaji kwakwalar warshi tajuya abaibai.

❤❤❤

DUNIYA BIYU MABANBANTA (TWO DIFFERENT WORLD) Onde as histórias ganham vida. Descobre agora