1

3.7K 94 6
                                    

_💫TWO DIFFERENT WORLD💫_

_*DUNIYA BIYU MABANBANTA*_

_BISMILLAHI RAHMANIR RAHEEM_


               ✍️ M SHAKUR


                         1️⃣

FREE PAGE           
Ahankali yake saukowa daga stairs katafaren falon dako gidan shugaban kasa sai haka, yana sauka ahankali yana gyara zaman necktie din wuyanshi da hannu daya kasancewa dayan hannun na rikeda wata briefcase brown, daidai lokacin wata babban mace da a kalla zatai 57 tana sanye da shiga na alfarma tabude kofar wani daki wanda ga dukkan alamu kitchen ne sabida kamshin girke girke daya cika ko'ina tafito bayanta kuma wata maid ce dake sanye da uniform din masu aiki tana rike da babban warmer da alamu abinci ne aciki ta tsaya a bayan matan ganin uwar dakin nata ta tsaya itama, ganin matashin yasa batare data kalli maid dinba tace "kai kulan dining Shafa" sanan tacigaba da tafiya daidai matashin yakarasa saukowa daga stairs yakaraso gabanta, kafinma yay magana ta mika hannunta takai kan necktie din dayaketa fama dashi da hannu daya ta shiga gyaramai, dan murmushi yasaki cikin wata yar karaman natsassiyan murya yace "Barka da safiya Ammi" batare data amsashi ba ta sauke hannayenta kasa ganin tagama gyaramai ta kalli fuskarshi damuwa karara ya bayyana akan fuskarta amma saitai shiru batace mai komiba, kallon datake mai yasa adan shagwabe yace "Ammi, menen.....?" wuceshi tayi tai dinning taja kujera tazauna tadau mug tareda bude flask ta tsayaya ruwan zafi sanan ta waigo ganin har lokacin yana tsaye inda ta barshi yasa tace "anan zaka tsayane kana kallona ko ba break zakayi ba?"




Ayanda tamai maganan yasa yagane fushi take dashi kuma yasan dalilin fushin, karasowa yayi yaja kujeran gefen ta ahankali ya ijiye briefcase din hannunshi kan dayan chair dat is next to him sanan yazauna ahankali, mug din shayin dayasha kayan kamshi ta turomai gabanshi cikeda fushi tadau plate mai kyau fari kal kal ta debamai soyayyan Irish sanan ta kallai babu alamun wasa akan fuskarta tace "pepper soup ko ketchup? Wanne zan samaka?" murya chan kasa yace "ketchup" daukan bottle din ketchup tayi tabude tazubamai a gefen chips din dayawa dan tasan Allah yazubamai son ketchup sabida shi kadai agidan nan takesa ayo cefane harda na ketchup dan shi kadai kesha ita haryau abin baimata bane ko dandane batayi. Turamai plate din tayi gabanshi zata zare hannunta daga jikin plate din yakama hannunta yarike hakan yasa tadago idanunta ta kallai, dan shiru yayi yana kallonta sanan yadan sauke ajiyan zuciya asanyaye, murya chan kasa yace "I promise bazan dade ba kinji Ammi please" dan lumshe ido tayi cikeda takaicin shi sanan tabude su, batason tamai masifa hakan yasa ta sassauta murya tace "gobe fa bikinka haba Waleed bazaka iya daukan break kahakura da zuwa aikin nan ba, yakamata kaje kaga Ilham ko, you suppose kaje kaganta kaji medame dame take bukata, yaufa dinner ku mesa kake hakane? Kai baka gajiya da aiki, safe aiki, rana aiki dare aiki dukkai kadai bakagajiya?" tai maganan sounding a bit harsh sanan tai shiru tana kallonshi, ahankali ya saukar da kanshi kasa kaman bazaiyi magana ba saikuma yace "am doing all wat am doing for Dad Ammi, I'm doing it for him" yay maganan tareda dago kanshi ya kalli mahaifiyar tashi sosai yaga jikinta yay wani irin sanyi, hannunta takai ahankali ta shafa full sajenshi dakeda mugun laushi yana kyalli sosai tace "Waleed, Boy listen" tai maganan ahankali tace "I know u are doing all this for your father and trust me, I know duk inda mahaifinka yake he is proud of you cus he gave birth to such eloquent hard working youngman da burinshi shine yataimaki Al Umma, but in this Life Waleed you need to balance somethings, bazaiyu kullum aiki aiki aiki ba, u are needed awasu wajajen, za'ayi bikinka but bikin baya gabanka kwata kwata kabar su Khaleel da Hammad sumaka komi that isn't right kagane?" gyadamata kai yayi ahankali, sanan tace "abinda nakeso dakai yanzu, I know how much this work means to you dan haka bazan hanaka zuwaba, kaje but ana tasowa daga sallan juma'a kadawo kazo kafara shirye shirye, take a break of 2weeks aure zakayi kaji" gyadamata kai yayi amman harga Allah yasan yanada rai da lafiya bazai iya yaki zuwa wurin aiki harna tsawo kwana goma shahudu ba but bazai iya gardama da Ammi ba. "now eat karkai latti" maganan Ammi ya katse shi hakan yasa ya karbi fork din datake bashi ya shigacin Irish din yana dangwalawa a ketchup, yadanci badayawa ba yadau shayin ya shanye sanan ya goge bakinshi yatashi yana kokarin daukan briefcase din yace "ina Mum Ammi? Naje dakinta bata ciki" murmushi Ammi tayi tace "Mum dinka nachan ana harkan biki, ni banmasan ina tanayi ba, wuce katafi sabida kadawo dawuri" gyadamata kai yayi yadau briefcase din yafito waje, babban compound ne mai bala'in girma sai amsa gaisuwan masu aiki yake, gaban wata jeep yayi da wani mutumi katoto ke tsaye agabanta yana sanye da bakaken suit, yana ganinshi yabude mai baya hakan yasa ya shiga ya zauna, yamaida kofar ya rufe sanan yawuce ya shiga mazaunin direba ya kunna motar aka budemusu Gate suka fita.




DUNIYA BIYU MABANBANTA (TWO DIFFERENT WORLD) Where stories live. Discover now