28

976 24 1
                                    

💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫

      

            ✍️ M SHAKUR



                        2️⃣8️⃣



FREE PAGE
Direba ne yace "Waleed kikeson gani Hajiya"? Gyadamai kai tayi hakan yasa yarike ma Ammi hannu yar aikin ma tarike ta suka dagata da kyar ta iya tsayuwa a feet dinta, mai gadi yacema yar aikin. "kawo mata mayafinta da jaka da takalmi" da gudu yar aikin tai sama dakinta ta shiga tadauko mata hadadden mayafinta da takalmin ta da jaka ta sauko kasa yafama Ammi mayafin tayi akan tsadadden lace din dake jikinta sanan tasa takalmin, ta karbi jakan dan tasoma dawowa daidai sukai waje da ita motar ta direba yabude ta shiga baya ta zauna suka rufe ta sanan ya shiga gaba yatada motar gateman yabude gate suka fice, suna ficewa motar Mom na sawo kai tabi motar Ammi da kallo daya wuceta da gudu yar aikin tafita waje taje wajen motar Mom cikeda girmamawa tace "sannu da zuwa Mom, Mom please jibi Hajiya, ankirata awaya bansan me aka fadi mataba amman saida ta sume kuma yayyafa mata ruwa ta farfado tace a kaita wajen Waleed agidan marayu yanzu sun tafi, please kibata I don't want wani abu ya saman mini Hajiya" cikeda tashi hankali Mom tace "karki damu bari na bita" kwana tayi da sauri tabi bayan Ammi itama.

Motar Ammi na zuwa gate kasancewan security sun santa suka fara ihu. "Hajiya Don come Hajiya Don come, open the gate" sukahau jin dadi dan bata cika zuwa gidan marayun ba but duk randa zatazo ruwan kudi take musu, dan yake ta musu ta saka hannunta cikin jakan da yar aikinta tabata rapas din yan dubu sababbi ta dauko guda biyu ta mikama babban su, ihu sukahau yi suna mata godiya direba yaja motar ciki, kafin su rufe gate saiga second Mom, dadi kaman yau ana baki itama kyautan tamusu mai tsoka sanan ta shiga ciki, har gaban office din Waleed inda yake parking motarshi direba yay parking, tsabagen yanda jikin Ammi ke rawa kasa bude kofan tayi saida direba yafito yabude mata tasa kafafunta tafito tana fitowa motar Mom na sawo kai wajen, parking tayo tafito da sauri tai wajen yayanta data tsaya chak tana kallonta tace "Adda meya faru?" kasa magana Ammi tayi tajuya kawai Mom biyeda ita, itama Mom ganin yanda mutane suka taru a tsakar wajen yasa taji gabanta yafara faduwa, ana ganinsu aka fara gaishe dasu. "Barka da zuwa Hajiya, barka da zuwa Hajiya" kasa amsa kowa sukayi Ammi tai gaban asibitin daidai Mama Iyami dake kuka sosai tafito tawani irin zube agaban Ammi tace "Hajiya ku shiga yana ciki, wayyo Allah na mun shiga uku, gatanmu na kwance a asibiti raga raga, rai na hannun Allah" tsallaketa Ammi tayi tasa hannu tabude kofan ta shiga ciki Mom biyeda ita, Nurses din data gani charko charko tsaye agaban reception din tawani irin dakama tsawa. "kuna kallo na bazaku gayamin inda d'ana yakeba" arude duka nurses din suka mata pointing dakin da aka rubuta emergency asama, yanda Ammi ke ihu yasa Mom takama mata kafadar Ammi alamun tai calming down, kabar da hannunta Ammi tayi tai hanyar dakin, tana zuwa batai watawataba tabude kofan tasa kanta ciki, Dr Kemi da Dr Ayo ne akan Waleed din dahar lokacin bai farfado ba, ancire mai riga da singlet, dagashi sai dogon wandon jikinshi da belt anmai dauri akafada ta wajen hammata an hade da hannunshi kaman wanda ya karye, fuskarshi tai jajajir, gefen idon damanshi dama idanun duk sun kumbura, gefen bakinshi ya tsage yanadan jini tsabagen marin dayasha na Arham, wuyan shi tsabagen matsan da riga da necktie din wuyanshi sukamai har ciwo suka jinmai jini nafita wuyan yay jajir kaman an zaneshi da bulalan inji.

Hawaye ne suka cika idanun Ammi takasa rikesu suka shiga zubowa har zafin dukan takeji ajikinta tsabagen tashin hankali, tunda ta haifi danta incident makamancin hakama baitaba samun dantaba, daidai Dr Ayo yagama gyara jinin wuyan yajuyo ganin Maman Waleed yanda jikinta ke rawa tana kuka yasa yace "calm down ma, bawani abu babba bane kashin kafadarshi tadan goce ta sanadiyan buga bayanshi da akayi da bango, saikuma bruises din wuyan nan dakuma na ido, dan jini yataru acikin idanunshi but with time zai washe, calm down Hajiya, nan da dan anjima kadan danki zai farfado" da sauri Dr Kemi data karaso wurinsu itama ta gyada kai tace "yes ma calm down please Ma" sukabi ta gefensu suka fita daga dakin, wani irin juyowa Ammi tayi cikeda wutan bala'i, da kunan rai da tsantsan bakin ciki ta kalli Mom sanan tanuna mata Waleed dake kwance kan gado da hannu tace "kinga abinda Arham yama d'ana ko? Kinga abinda Arham yama d'ana ko, kina gani daiko, yaron da dama kece tun day one kikai approving friendship dinshi da yaron, left to me yarona ya rayu ahaka baida aboki I his mother can be his best friend and his everthing aman kika nace saina barsu sunyi abota, dan haka karma naji kinhanani dauka hukunci dan wlh wlh bazan yarda ba" tai maganan tana dauko wayanta daga cikin jaka da sauri Mom tace "Adda kinga calm down yanda kike tafarfasan nan bai kamata kidau hukunci ba, dan Allah kiyakuri Adda" da wayan hannunta tanuna Mom tace "Zainab ki shiga taitayin ki, na rantse miki da Allah yanda Arham ya jima d'ana rauni ko kwana baza'ai ba shima sai anjimai, wlh saiyasan ya buganmini d'a, shidan ubanshi ubanwa yataba dukanshi haka? Waleed dakoni bantaba daga hannu na daka bane wani kato zai dokanmin wlh wlh saina ramamai, wlh kuwa kinji na rantse miki" Ammi tai maganan tana bude kofa tafita daga dakin tana dailing number Maman Arham.




Ringing daya Mama tai picking call din ganin kira daga Ammin Waleed, kafin ma Ammi tai magana cikeda fara'a tace "Assalamu Alaykum, barka da yamma Hajiya" ko amsa sallamarta Ammi batayi ba cikeda bacin rai tace " please kome kikeyi kibarshi kisamemu a orphanage na Waleed yanzun nan kizo, ina jiranki yanzun nan" tana kaiwa nan ta katse wayan jikinta na vibrating, Mom ma takasa cewa komi tazama yar kallo matsalan yayarta kenan intai fushi batada hankali, kuma bataji bata gani barin ma when it comes to Waleed matter.

Gaban Mama ne ya yanke lokaci guda ya fadi, tunda tasan Ammi tsawon shekaru kenan  bata taba tamata irin wanan kiran ba saiyau, tomeya faru? Allah yasa alkhairi ne, ahankali tafara  karanto innalillahi wa innailaihi raji'un kota samu natsuwa cikin zuciyarta, dan batada natsuwa ko kadan sabida  zuciyarta wani irin mummunan faduwa kawai yake.



Hijabi kawai ta dauka ta zira akan kayan dake jikinta, ta kwalama diyar kanwanta kira tace "nafita yar albarka saina dawo, ki daura abincin dare" daga ciki yarinyar ta amsa da "saikin dawo Mama" fita tayi daga dakin ta kwalama driban ta kira yafito, mota ta shiga tace yakaita orphanage dinsu Waleed ya amsa mata da to, yatada motar yafita daga gidan.

Ko cikakken 15min direban bai daukaba yakaita orphanage din, tana fadin mahaifiyar Arham ce ita aka barta ta shiga dan ta taba zuwa sau daya suka shiga ciki, kirjinta bai kara faduwaba sai dataga ma'aikatan orphanage din carko carko a tsaitsaye ana tattaunawa agaban clinic, parking direba yayi tabude kofa tafito daga motar kirjinta na bugawa, wayarta dake hannunta taciro tanemo layin Arham ta hau kiranshi danta tambayeshi maiya faru, wani abu yafaru ne amman har wayan ya katse bai dauka ba, hakan yasa tai dialing number Ammi, ringing daya Ammi ta dauka, ahankali Mama tace "Hajiya na iso" cikin muryan Ammi dabata fita sosai tace  "kishigo asibitin muna emergency" shine kawai abunda Ammi tafadi mata ta katse wayan, sosai Mama taji kirjinta na bugawa yanda Ammi kemata magana, hakan yasa ta daga kafarta tana kallon mutane ta shiga tafiya harta karasa gaban asibitin tasa hannu ta bude kofar ta shiga ciki, kasan cewan emergency din asibiti bata boyuwa yasa tana ganin dakin tagane batare datama tambayi nurses din dake wurin ba tai wajen kofan, ahankali ta murza hannun kofan dakin tashiga ciki, Ammi da Mom tagani zazzaune, Mom kan kujera Ammi kuma kan gado gefen kafar Waleed, Waleed kuma kwance kan gadon asibiti, ansa mishi drip, fuskarshi tai jajir ta kumbura wuyanshi ma haka, hannunshi adaure daurewan irin na karaya dinan, wani irin mummunan faduwa gabanta yayi karfin hali tayi tadaga kafarta ta karaso cikin dakin ta tsaya gefen Waleed, bakinta har rawa yake tace "Ha....Hajiya meya sami Waleed? Meya faru? Meyasame shi"? muryanta na breaking sosai tayi maganar hankalinta a mugun tashe, dagokai Ammi  tayi tazuba mata jajayen idanunta sanan ta tashi daga kan gadon tace "biyoni" da sauri Mom ta tashi tana girgiza ma yayarta kai amman Ammi ta dauke kai kaman bata ganta ba tabude kofa tafita Mama biyeda ita, itama Mom tabisu wajen, tsayawa sukayi a reception premises din cikin fushi Ammi tamata pointing dakin da Waleed yake ciki tace "wlh mutuncin ki danake ganine yasa nakiraki dan kizo kiga abinda yafaru da idanun ki, kinga Waleed dina, kinga yanda yake akwance agadon asibiti, kinga yanda yadawo, dan iskan danki ne ya mishi haka, Arham ne yama Waleed dina haka, jibi yanda yama d'ana dukan dakoni dana tsugunna na haifeshi bantaba mai irinshi ba, kitayani tambayan Arham da ina labo yazo yatayani nakudar d'ana ne dazai kamamin shi ya daddaka haka"? mamaki ne ya mugun cika Mama kaman wacce ke koyan magana tadafa kirjinta tace "Arham! " tana kwalalo idanunta waje tsabagen mamaki, cikeda masifa Ammi tace "duk abunda Waleed yama Arham da abunda zai saka mishi kenan, Waleed ko agogo nasaimai bayi karba saina sayo biyu nashi dana Arham, komi shida Arham, amman yau Arham ne zai kamashi yama wanan shegen dukan toh wallahi bazan yarda ba, wlh, bazanji kunyarki na cuci kaina ba, wlh wlh bazan yarda ba yanda yama yaron nan shegen dukan nan sai shima anmai irin ta, mai rabani da Arham sai Allah don saina yagashi, saina sa anmishi x10 abunda yama Waleed wallahi wallahi bazan yarda ba" Mom dai batace komai ba kuma batayi yunkurin hana Ammi fadan ba saboda zata iya komawa kanta, ita kanta abin ya daure mata kai har lokacin yanda Arham yakama Waleed ya daka haka. Numfasawa Mama  tayi ta goge hawayen daya zubo mata tace "Hajiya kima Arham kome kikaga dama, karki barshi kisa shima amishi fin haka, fin dukan dayama Waleed ma dan abinda yayi bai daceba nabaki goyon bayan nan dan inbama kisa amai hukunci ba ni wlh sainasa" wayan dake hannun Ammi tabude takira inspector general of police na tafada mishi komai sannan tace mishi atabbatar ankarya ma Arham hannu da kafa kafin dare da toture na police, tana katse wayan ta shiga turama inspector address din gidansu Arham.

❤❤❤

DUNIYA BIYU MABANBANTA (TWO DIFFERENT WORLD) Where stories live. Discover now