Thirty-one- Miscreant

Start from the beginning
                                    

Kuɗin dake wajen Kankana dubu biyar ne, tasan bazai isheta ba amma haka ta haƙura tace saita je domin kada a raina ta. Duk kayan data saka sai taga baiyi mata ba, haka tayita canza kaya saida ta saka wani Off shoulder riga da skirt. Abin ya zauna ɗas a jikinta. Haka ta sheƙa kwalliya a fuska tareda shaka eyelashes. Saita ɗauko wani siririn mayafi ta haɗa dashi. Atamphan mai kala da yawa ne, saita ɗauki yellow jaka da kuma jan takalmi duka zai shiga dashi.

Mahfooz yana daga bakin varanda abin duniya ya ishe shi, neman hanyar da zaiyi ya bar Kankana yakeyi. Baya ƙaunar auren kuma ya dauki alwashin saiya rabu da ita. Duk runtsi saiya nemo yanda iyayen sa zasu aminta su yarda ya saketa. Kamshin turaren ta ya dawo dashi daga kogin tunani wanda ya shiga. Tayi kyau ainun amma wannan ba kalar kwalliyar data dace yar musulmi tayi idan zata fita bane. Uwa uba matar aure. Tabbas Rumasa'u ta maida shi baho sai yanda tayi dashi.

“Ina zaki?" yace mata fuskansa babu alamar wasa a cikinta.
Harara ta watsa mashi tana tura hanci saita ce, “Baba inda ka aike ni," saita soma tafiya.
“Dan rashin mutunci abinda zaki ce min kenan a matsayin mijinki.”
Cak ta tsaya ta fara dariya. Hannunta ta soma tafawa saita ce," miji? Wannan ne miji? Idan maza sun tsaya ka isa ka fito? Ka ajiye wuya tsololo kamar mariƙin lema,"
Shiru yayi jikinsa yayi mugun sanyi, wai Rumasa'u wanda tayi komai domin ta aure shi shine take zagin sa kamar sa'anta. Ita kam wucewa tayi ta tare napep ta nufa inda zata.

Duka ƙawaye dake wajen sai kallonta akeyi, ta rasa meyasa suke ta mata kallo. Sai tace "Wai lafiya kunata bina da kallo haka?"

Miemie ce tace, "Naga kamar a napep kika zo, ke kam ba kiji kunya ba. Kina auren Qwaro babban dan kwallo amma bakida mota.”

“Yana wajen gyara ne,”

Tayi masu ƙarya, saita soma tunani. Tabbas ta bada mata kuma ta bada bariki. Meye amfanin kana bariki bakada motar kanka. Dabara ya faɗo mata akan ta tilasta Salima ta siyan mata koda 206 ne kokuma taje gidan radio tayi shela tace ita yar madigo ce wanda ke bin yara ƙanana.

Anata ci anata sha kowa sai gatsa yakeyi saboda ƙoshi, bayan nan suka kunna shisha sunata busa wa. Mazan su da matansu anata hutawa ana chilling hankali kwance anyi hotuna sosai kowa yanata roƙon Kankana tayi tagging ɗinsa idan ta watsa. Tunda tafi kowa yawan followers.

Kafin su tafi Halimomo ta ce an fito da ankon ta dubu saba'in ne. Anan kowa ya soma zare ido suna cewa gaskiya yayi tsada. Ita kuma tace bazata rage ba. Wanda zata aura yana aiki a oil and gas ne kuma bata san ƙaranci. Yin anko shine katin gayyatar ka. Ko maza su siyan ma yan matan su ko kanne.

Gaban Kankana ya soma duka uku uku, abin duniya ya soma yin mata yawa. Ga zance mota data ke so, sannan kuma gana anko. A wajen Miemie ta tura ma Halimomo dubu hamsin. Tayi sabon saurayi dake ji da ita. Kowa daga bada 20k sai 30k. Kankana ne kawai bata bada ko sisi ba. Duk taji babu daɗi. A hankali sunata gaya mata magana wai tayi baƙi ta soma lalacewa. Anan tace tayi barin ciki ne yasa haka. Jaje akayi mata ana mata addu'a.

Halimomo ta rage ma Kankana hanya, tunda ita a NDC take zaune, ita kuma ta dawo gida zuciyar ta duk ya jagule. Bataga Mahfooz ba. Taɓe baki tayi sai ta wuce kitchen domin tasha ruwa.

Shi kuma wajen la'asar Daddyn Faash ya kirasa domin yana san ganinsa, anan ya samo dabara akan cewa zaiyi karyan zai bar gari zashi Arsenal kwallo. Yasa gwara ya sake Rumasa'u kafin ya tauye mata hakkin ta. Tun daya shiga falon yaga fuskan Mommy akwai damuwa. Hajia Fati tana bala'in tausayin Mahfooz, amma zaman aure takeyi kuma bazata iya yin ma mijinta musu ba. Saidai tabbas bata goyon bayan abinda Daddy yake so yayi.

Mahfooz yana zaune saiga Faash ya shiga, dukansu sun zauna sunyi shiru. Shi karin kansa Daddy yana jin nauyin abinda zai faɗa masu. Jiya wani tsohon amininsa ya nema alfarma wajensa. Kuma da farko yace zaiyi tunani akan zancen. Amma yau ya kira sa akan cewa matarsa ta rasu. Abin ya razanar dashi, idan ya kasa biyan masa bukata zai zama kamar yayi masa butulci ne.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now