Twenty-two - Pound Of Flesh

996 188 55
                                    


In retrospect, kowa ya tsane Mahfooz. Shikenan babu wanda yake ganin nashi perspective ɗîn? Kanjamau fah aka ce, aids mai karya garkuwan jiki? Shine kuka zauna kukayi ta tsine ma Mijin Tauraruwa baiji ba bai gani ba. Especially yan Taskar Dimples kamar yayi maku wani gagarumin laifi. Anyway team Mahfooz dumu dumu, yan baƙin ciki su koma gidan Fauziyya da zama, ehe! #FullyDimplated

Tuƙi yakeyi zuciyar sa yana mugun tafasa, baya ko ganin gabansa. Saura ƙiris yayi arangama da motoci da suke lodin pasinja. Haka suka watsa mashi zagi sosai suna tsine mashi tareda kiransa ƙatan wawa. Bai ko kulasu ba ya danna motansa ya wuce. Sanda ya fito daga motarsa, bai samu damar ya rufe ƙofar ba, da sauri ya wuce cikin gida.

A hanyar ɗakinsa wanda suke kwana shida Faash ya iske Hajia Fatu Maman Faash, a gurguje ya gaida ta saiya shiga ciki. Wani zugi kansa ya soma mashi. Anan ya ɗauko ƙanƙara dake gefen gado ya saka a saman kanshi, har lokacin bai bar ganin dishi dishi ba. Nan take ya yanke shawara akan ya kashe wutan ɗakin, babu duhun daya wuce abinda yake wakana a rayuwar sa yanzu.

Yana san Naseera, tabbas yana santa. Amma ta cuce shi, ta ɗane shi da dafin da baya zaton zai iya warkewa daga gareshi. Bai taɓa soyayya kamar nata ba, kuma baya tsammanin zai taɓa irinsa. Ta gurɓanar da zuciyar sa. Ya sakankance akan soyayyar ta. Amma ashe duk yaudara ne, tayi komai domin ta cuce shi saidai kuma ta Allah ba nata ba. Ba dai mutum ba saidai Allah.

Tunani ya somayi kala kala akan yadda zai ɗauki fansa a gareta, shi baida zuciyar mugunta. Amma yanaso ya koya mata darasi, bama ita kaɗai ba duk matan duniya masu mugun hali. Yanaso ta zama ishara akan masu tunanin aiwatar da irin abinda tayi. Idan ya gama da ita, ko ruwan kwata zai fita daraja.
Anan dabara ya faɗo masa, nan take ya soma murmushi daga nan abin ya girma ya rinƙa babbaka dariya. Haka yayita ƙyalƙyatawa yana tafa hannayen sa.

“Qwaro kenan, hanjin jimina, an buga an barka.” Yayi ma kansa kirari.

Ita kuma Naseera tana kwance a gefe, har Rumasa'u taso tayi mirsisi ta tafi. Saita tuna cewa idan aka ga Naseera a mace gagarumin matsala zata shiga, gashi bataso ta sake komawa gidan yarin da aka kaita. Kallon gefe tayi hagu da dama, sai taga butan da ake bama furanni ruwa a gefe. Da sauri ta ƙarasa wajen, saita wuce famfo dake garden ta ɗebo ruwa. Kusan rabi haka ta cika, sannan taje inda Naseera take kwance rai hannun Allah. Gaba daya ta sheƙa mata tana zare ido, nan take Naseera ta soma tari a hankali kafin kuma abin ya tsananta. Buɗe idonta tayi tana ajiyar zuciya, duk ta birkice kamar gashin tsohuwa.

Tana zaune zaman dirshan a wajen, kallon gajimari takeyi, sai komai ya soma dawo mata. Cikin ƙanƙanin lokaci duka rayuwar data ke mafarki zatayi da mijinta ya ruguje. Akan wani dalili? Na ƙauran baki kokuma na gulmar Rumasa'u? Menene tayi ma Rumasa'u a duniya datake neman ta raba ta da duk wani farin ciki nata? Da farko ta dawo wajen Dr Abdallah, yanzu kuma Mahfooz.

Kuka ta fashe dashi data tuna cewa Mahfooz ya saketa. meyasa ya wurgar da soyayyar su ba tareda da bincike ba. Dama soyayyar dayake ikirari kenan duk baida zurfi. A fatar baki ne bai kai zuciyar sa ba. Yanzu akan wannan magana har ya danƙara mata saki. Idan baiso wani alaƙa ya shiga tsakanin su, ita taji ta gani zata iya jurewa, zata iya zama dashi a haka saboda tana bala'in sanshi. Sannan kuma idan da za'a juya lamarin zuwa gareta, tasan bazata guje shiba. Tare zasu magance kowane matsala saboda sun riga sun zama ɗaya. Amma kuma ashe iska yana wahalar da mai kayan kara ne bata sani ba.

Banda Alhamdulillahi rabbil alamin, Rumasa'u bata faɗin komai cikin ranta saboda tayi mugun jin daɗin sakin da akayi. Cikin sati kusan uku yau yana ɗaya daga cikin ranakun data ambaci sunan Allah. Idan tace ta mance yadda ake sallah babu mamaki. Babu mai shiga harkan ta, itama sabgar gabanta takeyi. Babu kuma wanda zaiyi tunanin zata iya aiwatar da gurmutsun kafirci. Sau ɗaya ta karanta Fatiha, wani rana datayi mugun mafarki, à firgice ta farka tana neman ceto shine tayi addu'a ta kwanta.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now