_ZAIRANA_

A sashen gimbiya Zubaina Sadauki ne ya hada kayan wanki kamar yanda ta bukata ya tafi bayan sashen ta yafara wanki duk da bamasu yawa bane amma jiyayi kamar sunkai kala hamsin baisaba da wahala irin wannan ba amma haka.m yasama kanshi jajir cewa ya fara dikar wanki kamar ba gobe bai daurayi kaya sai ruwan yakoma fas sannan.....Zubaina ba ma'abociyar zuwa bayan gida bace amma saboda ta dinga ganin wulgin Umar tana jin dadi shiyasa ta zagayo baya ta zauna anata yimata tausa amma baki daya hankalin ta na kan Sadauki koda ya karasa wankin ko kallan inda take baiyi ba ga gifta ta gefenta yayi shanya....ita kuma duk sadda Umar yaki yimata magana ba karamin bata mata rai yakeyi ba acewar ta ai bawan ta ne dole yaimata biyyayya shikuma baisan yawan magana shiyasa ko sun hada ido yake nuna kamar baisan da itaba bayan tagama shan yarshi ya hada kaya zai tafi aiko ta kirashi....."Umar tsayawa yayi yakai sakan shabiyar kafin ya juya a miskilan ce tahowa yayi inda take kamar baisan  taka kasa, kallan shi kawai Zubaina keyi koda ya iso mai makwan ya duka a tsaye ya tsaya yace mata gani, tunda ga sama har kasa ta kalle shi a dage sannan tace haka ake girmama mutane a garin ku? yi yayi kamar baisan da shi take ba, saida fadila tace mashi kaduka sannan ya duka a nutse, amma yaki kallan fuskar gimbiya Zubaina......"Umar meyasa baka girmama na sama dakai?kallan da ya watsa ma gimbiya Zubaina nane yasata faduwar gaba, "bangane me kike nufiba? Baki daya kwarjinin shi ya hanata magana saidai kallan sa takeyi....."Hmm kinyi shiru karfa kimanta Umar nike kuma bawa marar yan'ci taya zanki mutun ta mutane, bayan kullun Abba Ado saiya fadaman waye ni da matsayina nidai kawai bansan shiga rayuwar mutane balle waanda suka fi karfina, karki manta ke uwar dakin Umar ce, kada kiga inayi maki magana ba yanda kike soba, nasan a sannu da koyi komai, nabarki lafiya gimbiya Zubaina.....Tunda taji Sadauki ya ambace sunanta saitaji kamar yafi kowa iya fadan sunan batasan ya tafi ba, saida ta dawo daga tunanin ta sannan taga bainan a sanyaye ta tashi suka mara mata baya takoma dakinta tarasa meke damun ta gamida Umar gashi koda batasan soyayya ba tasan ba son shi takeba,  dan tasan ba haka so yakeba, itadai kawai Umar na birgeta amma aiba abinda zatayi da bawa...... Mardiyyah ce zaune a cikin gidan yarin gilba ta rasa meke mata dadi tun tana kuka har ta dangana izuwa yanzun duk tayi baki ta rame kamar ba itaba, duk da tasamu labarin mijinta  bai mutu ba amma bai hanata shiga damuwar rabata da dan'ta ba, labari ya samesu Barde yaima Yusrah fyade,taji dadi matuka,amma bataji dadiba da Yusrah ta rasa ranta ba, duk da suna gidan yari daya da Juwairiyyah amma ta rabu da haduwa da ita sau biyu a sati ake fiddo su asasu aikin wahala toh nan ne suke haduwa da yarta, danko waziri Basheer ko futowa baa ba rinshi yayi, tsaro ake bashi bana wasaba, yaudai nadaga cikin ranakun da Hamza yaba Hajara damar ganin mahaifinta saida aka caciketa tas sannan ta shiga koda ta isa sashen shi ba karamin kuka tashaba dan mahaifinta ya lalace ko magana bai iyayi sosai tsabar azaba shiko koda yaga yarsa murmushi kawai yakeyi na murnar ganin tilan yarsa, saida ta duba taga ba kallan ta sannan ta saka hannu a iner dinta ta fiddo daurin fira taba mahaifinta ya shanye ta dauko wata ledar da ruwa ta kara bashi ya shanye sannan ta sake ledojin ba karamin dadi waziri Basheer yaji ba nan ta fadama shi ranakun da zata dinga zuwa ta duba, nan ta fada mashi yanda sukayi da Hamza ya tsorata yana shakkar su Hamza kum baisan yaga abinda zai taba mashi iyali suna cikin ganawa akace mata lokacin su ya cika nan tayi sallama dashi ta tafi

Safiyyah ce kwance magashiyan yau kimamin kwanan ta bakwai tana labour amma haihuwa taki kowa ya fidda rai ba irin maganin da basu bata ba amma ba amo ba labari duk ta kumbure ta suma har kabari angina mata amma saita farfado raban da gimbiya Kursiyyah tayi bacci harta manta danko Goggo saidai tayi gyangyadi daga zaune, amma tunda gimbiya Masau'da tazo dubata sau daya ba takara bi ta kansu ba, koda ta kawo masu maganin nakuda tana tafiya suka yarda shi acewar su karta cutar masu da diya....

'''Haka rayuwa take duk abinda keyi haka kake ma kowa kallo ga rashin yarda da kowa, aibaaima Allah dubara kaidai ka kamanta gaskia komai kankantar ta, Allah na tareda mai gaskia'''

SADAUKIN BURHAAN CIGABAN IZZAH KO MULKIWhere stories live. Discover now