Twenty-nine - By Whatever Means Necessary

Start from the beginning
                                    

Yana shiga cikin falon sallama yayi kamar kowane musulmi na kwarai sai ya nufa hanyar ɗakinsa. Tun randa tace mashi ɗan wahala ya dawo daga rakiyar ta. Yana mugun jin haushinta, duk wani bege ko ɓurɓushin soyayya dayake tunanin da yana mata yanzu babu shi cikin jikinsa. Salap yaji yake ci kamar ruwan rijiya.

“My husband ka dawo?” tace tareda tashi tsaye.

Yi yayi kamar baiji ba saboda duk me take neman sa dashi yau bazata samu ba. Shi ya riga ya ɗauki kaddarar sa. Da sauri ta karasa inda yake tana magana, “My Husband tun ɗazu nake jiranka, har girki nayi maka,”

Cak ya tsaya yana mamakin abinda yaji. Saiya kalleta yana ta tunani, daga nan ya kalle gefen wajen dinning area. Kuloli ya gani jere wanda ya gasgata mashi abinda yaji.

"Da gaske nayi maka abinci my husband, zo muje.” saita janye mashi hannu suka nufa wajen. Bai hanata ba ya bita domin ya gani. Haka ta matsar masa da kujera domin ya zauna. Duk abinda takeyi mamaki yakeyi saboda bai taɓa samun wannan daga gareta ba.

Macaroni ta soma zuba mashi cikin plate, fari ne ba'a yi mashi wani kauɗi ba. Ba abin azo a gani bane amma wanda zai hau sama ya hau leda ai yayi kokari. Data ɗauko kwanon miyan mamaki yayi yanda bai soma jin kamshi ba, saidai yayi hak'uri yaga kila sai an zuba zai ji. Anan yaga ikon Allah, manja yaga yana saka mashi akan macaroni.

"Keh meye haka?” yace cikin takaici.

“My husband wallahi ina cikin aikin ne na lura babu kayan miya, shine nace bari nayi mana garau garau,” tace tana washe mashi haƙora.

Tsaki yaja saiya miƙe tsaye, saiya tafi ɗakinsa. Binsa tayi amma ya rufe a fuskanta. Anan ta tsaya sororo tana mamakin zafin daya keyi akan abinda bai taka kara ya karya ba. Yasa kwata kwata bata san mashi abin arziki, namiji ba ɗan goyo bane kuma ta ɗauki alwashin bazata taɓa mashi girki ba.

Haka ya rufe ƙofar ɗakinsa saiya zaune a bakin wajen. Ɗakin akwai duhu wanda ya kashe fitilar kafin ya fita kuma bai kunna yanzu ba. Nan ya rakuɓe yanata tunani, sai wayansa ya soma ruri. Daga aljihun rigar sa ya fito dashi, anan yaga wannan number dinne. Tsaki yayi saiya ajiye gefe yana ajiyar zuciya. Zuciyar sa yayi mashi baƙi kamar ɗakin dayake ciki.

Anan yana cikin tunani saiya mirgina ya soma barci, wajen ɗayan dare saiya soma mafarki. Wannan mugun mafarkin nasa ya somayi wanda yake ganin kamar ana shaƙe mashi numfashi. Da sauri ya farka yana salati ga zufa yana ƙaryo mashi. Rabon dayayi wannan mafarki tun ranar da ya kusan kashe Naseera a rugar su Musa.

Kankana idanta biyu lokacin tana chatting da yan One Love amma tayi burus dashi. Yana jin tana burutun ta fito shan ruwa. Abin yayi mashi mugun ciwo, amma ba wannan bane damuwar sa. Yanzu dawowar wanna bakar ciwon yake cin masa tuwo a ƙwarya. Haka ya kunna wutan ɗakin guda biyu na duka bangon. Sannan ya kunna recharageble lantern domin yaga haske. Amma yana rufe ido saiya buɗe, wani firgici da ruɗani yake mamaye shi.

Haka yayita rawar ɗari yana kwance akan sallaya, duk wanda yaga Mahfooz a wannan lokacin dole ya tausaya mashi. Baiyi barci ranar ba kuma bai bar firgita ba har asuba. Da kyar ya tashi ya iya zuwa bayi domin yayi alwala. Da kyar yake tafiya wanda ya hanashi zuwa Masjid. Ranar a ɗaki yayi sallah abinda bai saba ba. Duk runtsi duk ruwa yana kokarin yaje masallaci.

Salima da Nurse Jamila ranar bayan Asuba suka tasa driver ya tuƙa su suka nufa hanyar Kano. Ranar komai zai fito, ita Jamila batasan cewa akwai tsohuwar kiyayya da Fauziyya da Mahfooz ba, kawai zata je ne domin ta tada hankalin Rumasa'u tareda iyalan Dr Abdallah. Duk wani halarci da sukayi mata ta watsar a kwandan shara. Ta riga ta ɗauki alwashin sai Zubaida ta shiga gidan Mahfooz.

Koda isan su Kano kai tsaye gidan Alhaji Sani suka wuce dake Rijiyar zaki. Gidan ya canza masu saboda anyi sabon fenti tas, yanzu ruwan ganye ne da kuma ruwan hoda. Gashi ya watsa interlocking concrete tiles a ƙasan tsakar gidan. Sannan ya canza gate daga mai turawa manually zuwa electric. A bakin ƙofa sukayi ma Fauziyya waya domin tayi masu iso.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now