Twenty Seven- Idan Tayi Ruwa Rijiya

Start from the beginning
                                    

“Ina wuni Gwaggo,”

“Aha..”tace kawai saita soma bin Rumasa'u da mugun kallo.

“Gwaggo muje ɗaki na baki saƙon,”

Haka suka wuce har ɗaki zuciyar ta yana mugun tafasa dan takaici, tunanin yadda zata magance Rumasa'u takeyi domin taji sanyi cikin ranta. Suna shiga Salima ta haska mata mari kyawawa guda biyu. Haka Rumasa'u tana dafe kumatu domin zafi kuma hawaye suka taru cikin idanta

“Munafukan banza! Inace na rabaki dashi? Shine zaki ha'ince ni kina wani kulashi.” saita janyota tareda shaƙeta, “Yar banza harda masa kwalliya koh? Kin mance mena ce maki ne halan?”

Hawaye ne suka ciko idanun Kankana saboda wuya, numfashi ma da kyar takeyi saboda Salima ba ƙaramin chapka takai mata ba. Girgiza kai takeyi alamar a'a tareda nuna mata nadama ƙarara. Sai Salima ta ingiza ta saida ta bige a bango.

“Zamu haɗu,” tace tareda fita. Cupcakes ɗin yana hannunta bata ajiye ba. Duk daukarta Kankana tayi mashi liyafa, balle ta ganta fes fes cikin atampha.

“Sai anjima Gwaggo” Mahfooz yace sanda zata tafi. Bata amsa shiba saboda takaici. Fansa takeso ta ɗauka akan Rumasa'u.

Bayan awa uku da surgery ɗin Naseera, lokacin Labib ya tafi gida domin ya huta. Itama Anty Jawahir taje gida wajen yaranta sai aka bar wajen daga nurses sai Baba Abu. Yana zaune yana karanta magazine ɗin Forbes Naseera ta farka. Batace komai ba ta fara bin ɗakin da kallo tanaso ta gane meke faruwa. Har wajen mintuna goma sha biyar batayi magana ba kuma bata nuna alamar ta tashi ba. Baba Abu ne ya gaji da mujallar saiya kalle gefe wajen tabur ya ajiye, anan yaga hannunta yana motsi. Da azama ya miƙe yaje wajenta.

“Naseera Alhamdulillahi da kika tashi,” yace cikin farin ciki. Anan ta buɗe baki da kyar tayi magana.

“Ruwa.....”
“Me kika ce?” yace tareda riƙe mata hannu a hankali.
“Ruwa... Water,” ta sake faɗi.

Dispenser dake ɗakin yaje ya ɗebo mata ruwa daga ciki, baisan ko yaci ace ta fara ci ko shan wani abu ba. Abinda kawai ya sani shine ruwa rahama ne, kuma ya bata. Kurɓa uku tayi saita cire bakinta domin ta huta. Sai bayan ta huta ta sake kai bakinta domin ta sha. Daidai lokacin Nurse ta shigo cikin ɗakin, anan tace ma Baba Abu ya matsa domin ta duba ta. Tambaya tayi mata na sunanta da inda aka haifeta. Anan ta faɗa amma abinda zata iya tunawa kenan.

“Karka damu, zuwa gobe zata fara tuna sauran abubuwa. Kada a takura mata.” Nurse ɗin ta faɗa da harshen turanci.
“Nagode sosai,” ya amsa.

Daga nan Nurse ta canza mata ledan ruwa tareda kallon kanta da kyau taga ko yana jini, amma bata gani ba. Fita tayi tareda janyo mashi ƙofa ta rufe. Kirar Hajia Binti ne ya shiga tablet ɗin Baba Abu, ita dama duk ta ƙagara tayi magana da Naseera. Da azama ya ɗauka.

“Alhamdulillahi Anty, yanzu ƴata ta farka,” ya faɗa bakinsa har kunne.
“Toh Ma sha Allah masu ƴa, Allah ya ƙara mata lafiya.”
“Amin,” saiya ƙarasa inda gadon Naseera yake ya haska mata wayan a fuskan ta.
Naseera tana ganin Hajia Binti saita ganeta, “Ummaaa,” tace a hankali saita soma hawaye. “Me nakeyi a asibiti? Hope my baby is fine?” Tace tana hawaye. Umma taji daɗi sosai koba komai ciwon mantuwa bai kama Naseera ba kuma sauki ya soma zuwa in sha Allah.

“Dalla wawiya, kukan me kike yi? Shagwaba zaki min Baban ki yana kallon ki duk ki hanashi sukuni balle yaje aiki,” tace cikin barkwanci.

Shima Baba Abu ya ɗan dara, Naseera dai sake taɓe fuska tayi sosai bata ce masu komai ba. Tanaso tasan ko murna zatayi kokuma zata shiga kogin baƙin ciki.

“Umma....”

“Rufe min baki,” Hajia Binti ta dakatar da ita. “Ban san shiririta dan Allah. Bakisan wahalar da mukayi ba domin muga kin farfado, kada kizo kuma ki fara damuwa yanzu mu koma gidan jiya.”

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now