Sai a lokacin Salima ta lura cikin dare data buƙaci Rumasa'u ta tura mata hoton tambaɗa taga kunshi irin na amare jikinta, kawai dai tasha Rumasa'u tana san gayu ne. Tayi kira biyar Rumasa'u bata ɗauka ba. Aikam nan ta tura mata da saƙo tana gargaɗinta.

“Nasan abinda kikayi. Ko ki ɗauka ko naci bura ubanki. Karamar yar iska nafi ki bariki.”

Kiran daya sake shiga cikin wayanta ta ɗauka da sauri babu arziki, ita taso tayi ma Hajia Salima kora da hali ne.

“Dan ubanki ni Salima zaki gwada ma bariki?" sai kuma ta bushe da dariya. Mamaki takeyi yar ficika kamar Rumasa'u zata gwada mata tsiya.

“Bari na baki labari tsohuwar budurwa ta data fiki kyau ta fiki komai haka taso tayi min, na rantse maki acid na watsa mata kowa ma ya rasa. Babu wanda nake tareda ita data isa tayi aure. Butan Shayi!" tace tana ajiyar zuciya.

Ita kuma Kankana hankalin ta ya sake mugun tashi, jikinta ya soma rawar ɗari. Da sauri ta wuce bayi domin ta samu suyi magana.

“Wallahi Hajia ba haka bane, na rantse maki auren dole ne. Karki watsa min acid. Dan Allah nake roƙon ki Hajia.” Saita fashe da kuka wiwi.

“Rufe min baki munafukar banza! Auren dole shine baki faɗa min na samo mana mafita ba? Ba saina ɗauke ki ba mubar gari. Yanzu zaki kawo min zance, Inace gidan da kike ciki nice na taimaka maki? Toh wallahi saina fasa kwai, karyan iskanci kike. Yanzu kike shigo bariki......” haka tayita zagin Rumasa'u babu kakkautawa, ita kuma banda yi haƙuri Hajia bata cewa komai. Kuka takeyi sosai cikin bayi duk make-up ɗinta ya chaɓe harta tsige eyelashes ɗaya. Kaico da wannan hali tayi, ta samu Mahfooz ya aureta yanzu kuma za'a rabasu. A yanzu taji ɗacin da Naseera taji sanda aka rabasu. Kuma tabbas Mahfooz yaji saiya saɓa mata, gashi kuma Dr Abdallah zai sallame ta. Su Inna data raina zata koma masu.

Harta fito daga bayin Hajia Salima bata haƙura ba, tace yadda taci amanar ta saita rama. Tunda bata san darajar soyayya ba. Sanda ta fito ta riske Inna cikin ɗakin, suna haɗa ido sai Rumasa'u ta fashe da kuka. Tunda take bata taɓa jin daɗin ganin Inna ba kamar yau. Tabbas uwa uwa ce kuma soyayyar ta daban yake. Zuwa tayi ta kwanta jikinta ta barke da kuka.

“Inna ki tayani da addu'a, rayuwana zai ƙare. Na janyo maku magana kamar yadda na saba....”sai tayi shiru saboda kuka dayaci ƙarfin ta. Da babu Inna da babu wanda zata kai ma kukan ta, batada ƙawayen kirki wanda zasuyi deep talk dasu. Gashi Hajia Binti Mommy ɗinta bata sake mata fuska. Inna dai data raina Inna ce kaɗai ke santa duk faɗin duniya. Buga mata baya Inna ta somayi, bata san me tayi daya firgitata haka ba, kuma ba ƙaramin abu ne tunda harya sakata kuka.

Hajia Salima tayi alwashin cewa duka hotunan da Rumasa'u ta tura mata na badala zata watsa kafafen sada zumunta. Sannan kuma zata haɗa dana jiya wanda rabin sansan jikinta a bayyane. Haka Inna tayita mata Nasiha akan koma menene ta tuba zuwaga Allah, Allahu gafurun rahim. Kankana ta shiga natsuwa sosai, kuma koba komai duk runtsi tanada waje a zuciyar Inna. Bayan Inna taga ta natsu, saita soma mata faɗa akan aure. Tayita jaddada mata cewa aure haƙuri ne, yi nayi bari na bari. Shawara kala kala tayita binta dashi.

Ta fannin Naseera kuma hayaniya ya soma yawa, mutane sun soma hallara babu laifi. Sai tace bari taje gidan Anty Jawahir zuwa dare idan an kai amarya saita dawo. Abaya ta saka kalar toka saita yana kanta da baƙin mayafi. Da laptop ɗinta da waya ta ɗauka, zata je koda karatu tayi yafi mata zaman tunani. Tunda ta samu HIV tanata research kala kala akan ciwan, tanaso taga ko za'a dace da samun maganin sa.

Ta shiga motan ta zata fita, har an buɗe mata gate sai ga wani mota ta danno kai. Motar taki bama Naseera hanya wai dole Naseera ta koma baya idan ta shiga saita shiga. Abin ya bama Naseera takaici saita fito domin taga waye zai mata gadara da gidan ubanta.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now