Twenty-four Bazan Barka Ba

Start from the beginning
                                    

Wajen karfe biyu da rabi aka ɗaura auren Mahfooz Abubakar Gwaiba da amaryar sa Rumasa'u Salisu Bambale bisa sadaki dubu ɗari. Ko farin kayan daya saka da hula ranar tare suka je da Naseera NNDC mall dake Mohammadu Buhari Way suka siya. Yayi bala'in kyau a matsayin sa na kyakkyawa. Ba fari bane, baƙi ne sosai amma komai na fuskan sa yaje daidai dashi. Faash baije ɗaurin auren ba. Kwasan kayansa yayi ya wuce Abuja gurin babban wansu domin ya huce ma kansa takaici.

Har gida Mahfooz yazo tareda abokan sa da basu san kan zance ba, domin su gode ma Dr Abdallah akan karamcin dayayi. Sanda suka fito daga mota lokacin Naseera ta fito balcony, anan suka haɗa ido dashi. Kamar yadda ya saba mata haka zuciyar ta ya soma harbawa. Sanshi kuma yayita bin duk wani sansa nata. Ga kuma raɗaɗi cikin duk wani kursuwan zuciyar ta. Ji take kamar ansa reza ana farfarketa. Shi kuma yaga duk ta rame ta faɗa, tayi fari fat kamar fatalwa. Kana ganinta kasan bata cikin hayacinta. Duk wanda ya ganta saiya tausaya mata. Amma banda shi, yasan komai da takeyi kuma asalin macuciya ce. Harara ya watsa mata dayaga tana mashi murmushi wanda ita bata san tana yiba. Zallan daɗin ganinsa ne kawai ke ɗawainiya da ita.

Dr Abdallah bai nuna ɓacin ransa gameda abinda Mahfooz yayi ba ko kaɗan, yasan bada jimawa ba zata samu wanda zai so ta kuma ya mutunta ta. Naseera tanada shiga rai, ko baka sota domin komai ba zaka so ta dan kyawawan ɗabi'unta. Rumasa'u anci kwalliya kamar za'a fashe dan kyau, tanajin cewa Mahfooz yana gidan haka babu kunya taje falon, kuma ga abokan Dr Abdallah duk suna ciki an dawo daga ɗaurin aure.

“My husband...”tace saita rungume shi ta baya. Kunyar duniya yayi ɗawainiya da Dr Abdallah da shi kansa Mahfooz ɗin. A hankali ya ɓanɓare kansa saiya dawo da ita ta gabansa. Magana ya soma mata ƙasa ƙasa amma taƙi ganewa. Sarai taji amma bazata biya mashi buƙatar sa ba. Saida ya canza fuska sosai ya sake magana.

“Wai meye haka a gaban mutane muke mana, baki ga abokan Dr bane?”

Fari tayi da idanu tana ɗaga kafaɗa, zatayi magana sai taji muryan da bazata taɓa mancewa ba. Muryan iyayenta abin ƙaunar ta. Wanda bazasu taɓa rabuwa da ita ba. Dafa kai tayi saboda ganinsu ya haifar mata da ciwon kai.

Inna ce ta ƙarasa wajen fara'a akan fuskanta. Rumasa'u ta canza mata kuma tayi kyau sosai, kamar ba yarta ba wanda ta haifa. Tabbas babu abinda zai raba alakar da suka riga suka ƙulla. Itace tayi ma Rumasa'u magana wanda batada niyyar gaida ta.

“Ruma amarya yarinyar Inna kece kikayi kyau haka?” tace cikin barkwanci. Sekeke ta tsaya batace komai ba, Mahfooz ne wanda baisan ko waye ba ya rinsina.

“Ina wuni, barka da zuwa...” Ya faɗa a ladabce. Sai Inna ta kalle shi sosai, tabbas shi ta gani gefen Naseera rannan. Anan ta kawar da tunanin dake bijiro mata. Dukan su biyun yaranta ne, bai kamata ta nuna bambanci tsakanin suba. Ya kamata tayi ma Rumasa'u farin ciki, kila wannan ne sanadin shiriyan ta.

Hajia Binti ne ta hango Inna shine ta ƙarasa wajen, Mahfooz ya gaida ta saita amsa mashi a dikilce. Haushi yake bata ba kaɗan ba. Balle bata yarda da cewa Rumasa'u yarta bace. Tana taya Naseera kishi sosai, kuma tace sai an sake DNA test, bata gayama kowa ba. Zata jira a bude lab ɗinsu na Abdallah Specialist sai ta ɗauki sample ɗin Rumasa'u domin ayi bata sani ba. Idan ya fito eh ɗin ita ce yarsu lokacin zata koya ma zuciyar ta santa, amma yanzu tukun dai.

“Hajia har kun iso?” Hajia Binti tace

“Eh dama Malam yace na bari a ɗaura sai yazo ya taho dani, na same ku lafiya? Ya taro?” tace mata yayinda suke wucewa saman bene. Lokacin shima Mahfooz ya ƙarasa wajen dasu Dr Abdallah suke domin a gaisa. Rai baiso Rumasa'u ta koma ɗakinta tana huci. Wayanta ne yayi ruri sai taga sunar Hajia Salima ɓaro ɓaro ya bayyana. Bata ɗauka ba tayi burus da ita. Yanzu batada amfani wajen ta. Ta riga tayi aure kuma babu yadda zatayi da ita. Ita kuma Latisha ce ta gaya mata ta gani a wani status na ƴan kungiyar One Love wai Rumasa'u tayi aure.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now