Twenty-one - Annihilation

Start from the beginning
                                    

"I wish yarinyar mu will be as kind as asalin mai sunar,” ya faɗa. Kwalla ne ya gangaro mashi daga idanu. Yana kewar Zanira ba kaɗan ba. A layin su ya saka anyi borehole, idan an ɗiba ruwa ladan yaje wajenta. Koda yaushe yana ƙokarin yaga yayi mata sadaka domin shi kaɗai ce kaunar da zai nuna mata.

Naseera ce tayi hamma sai ya kalle agogon dake bango, 3:05 ya nuna. Sai ya umurce ta akan suyi koda raka'a biyu ne kafin su kwanta. Haka kuwa akayi, sai suka saka waya a charge suka bi lafiyar gado. Shidai bai kashe wuta ba, har yanzu da ƙaramin tsoro a tare da shi.

Da Naseera ta tashi sallan asuba gabanta ne yake ta mugun faɗi, ita dama haka take. Tanada strong clairvoyance, idan abu mara kyau zai faru da ita gaba daya ranar ta rinƙa jin sukuku babu daɗi a jikinta. Yau ma banda istigifari bata komai, koma menene tana fatan yazo mata cikin sauki.

Ta kasa samun natsuwa har gari ya soma wayewa, saita wuce kitchen domin ta taimaka ma Barira koda da hira ne. A lokacin harta fere doya domin zasuyi yam balls. Naseera da kanta ta wanke saita ɗaura akan gas. Saita wuce freezer ta ɗauko kayan miya attarugu da tattasai, tayi blending sama sama. Daga nan ta yanke albasa manya guda biyu. Duk su kayan kamshin ta yana gefe ta fito dasu sai sardine dake gefe shima.

A natse tayi yam balls ɗinta tana yi tana istigifari har lokacin, abinda ta kawo ranta shine zaman Rumasa'u. Babu kuma mamaki ƙila itace yarinyar Dr Abdallah. Sap ɗin Acha tayi bayan nan saita kai dinning table ta ajiye. Ɗakin Dr Abdallah taje, a hankali ta kwankwasa inda yayi mata iso ta shiga. Hajia Binti ta gani cikin ɗakin. Su biyun murmushi sukayi mata.

Anan suka gaisa saita ce masu abincin ƙarin kumallo yayi. Wani iri Dr Abdallah yaji, nanda sati uku duka wannan ɗawainiya zata daina zata koma yinma mijinta.

“Zauna mana !” ya umurce ta.

Babu musu ta zauna akan wani one seater dake ɗakin. Su dukan sunyi shiru suna so su ji abinda Dr Abdallah zaice. Gyara murya yayi saiya ajiye jaridar dake hannunsa. Hajia Binti ya fara kallo kafin ya mayar da idansa kan Naseera.

“Abu ɗaya nakeso ki sani Naseera, you're the daughter I prayed for. Koda babu jinina a tareda ke wallahi ban damu ba. Bana san kowace yarinya ko yaro bayan ke. Ke na sani kuma zan cigaba da zama da ke muddin rayuwa na... Yaushe ki kayi DNA ɗin?

Ajiyar zuciya tayi, kallon Hajia Binti tayi wanda itama ita take kallo. Da ƙaramin murya ta soma magana, “Sanda za'a yi maka bone marrow transplant... Lokacin... Lokacin...” saita fashe da kuka. Bata taɓa sanin ana haka ba, wai yaro ya tashi amma iyayen ba nashi bane. Da sauri Hajia Binti taje wajenta ta rungume ta, itama hawaye ta soma. Farad ɗaya rayuwar su zai canza. Sun saba kiran kansu The Three Musketeers, na labarin Alexander Dumas wanda aka wallafa a 1844.

Yanzu kuma wai za'a ce ga zance ga magana, eh sunji babu jinin Naseera a tareda su amma suna santa. Ƴace tamkar dubu. Balle ai babu laifin su, kowa yasan Hajia Binti ta ɗauki juna biyu. Sannan ta shiga Labour, yanda aka canza zuwa Naseera Allah kaɗai yasan abinda ya faru. Yanzu haka sun yafe Allah ya amfana.

“Babu wanda zai maye gurbin ki, Amaryar Mahfooz,” Hajia Binti tayi mata ba'a tana dariya duk da akwai hawaye idanta. Tare suka soma dariya su duka. Haka suke abin su, koda cikin tashin hankali ne sai sun nema yadda zasu mayar dashi wasa. Basa tsawwala komai, sun riga sun fawwala ma Allah wanda ke jagorantan su.

Sai Dr Abdallah yace ma Hajia Binti cikin satin zasu fara zuwa shaguna dasu stores domin aga abinda za'a siya. Hajia Binti wanda daren jiya ta kwana a Instagram, duk mai kayan kitchen dana gado tana following ɗinsu tanata bincike mai zata siyan ma yarta tilo.

A tare suka fita suka wuce falo, anata raha gwanin ban sha'awa. Suna saukowa daga bene sai Rumasa'u ta fito. Baƙin ciki mara mitsaltuwa taji ya mamaye ta. Dafa da ita za'a yi wannan hirar. Sannan kuma da ita ce zata rinka sauka daga bene.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now