Twenty - Mijin Tauraruwa

Comenzar desde el principio
                                    

“Wallahi Hajia irin ɗinkin ki nakeso nayi,” Rumasa'u tace bakinta yana rawa. Tunda take bata taɓa haɗuwa da wanda ya fita bala'i ba. Gashi kuma ta kasa rama wa. Koda yake wannan ba irin wanda za'a yi hayaniya dasu bane a kwana lafiya.

“Fauziyya sarkin bala'i, kinji irin ɗinkin zatayi.” Salima tace tana dariya, “Karki damu zan ɗinka maki irin shi,” ta kalle Rumasa'u ta fada mata. Ita kam Fauziyya harara ta watsa masu, saita ɗauki grapes ta soma ci, kana ta cigaba da wayanta.

“Son, kace har yanzu jikin baban naku babu sauƙi.....” Fauziyya wayanta tayi na kusan rabin awa, idan sun haɗa ido da Rumasa'u ta zabga mata harara. Tsanar yarinyar ya dirar mata kamar an soka mata kibiya a kirji. Ita kuma Salima tace kada Rumasa'u ta damu. Duk me takeso za'a yi mata. Ƙara gargaɗinta tayi akan samari barkatai. Saita bata dubu biyar ta hau mashin. Ta gode mata sosai saita tashi ta tafi, taso tayi ma Fauziyya sallama amma ta watsa mata harara. Da sauri tayi hanyar ƙofa ta fita.

“Yar banza kawai! Ko uban me ta rasa da take biye maki oho!” Fauziyya tace. Dariya Salima tayi sosai bata ce komai ba, wannan ba matsalar ta bane. Anan suka canza maganar suka cigaba da hirarrakin su na aminai. Hajia Salima tayi zaman Kano kafin ta dawo Kaduna kuma makwabta ne.

Rumasa'u kai tsaya Abdallah Specialist ta wuce, anan tayi masu bayani akan abinda Dr Abdallah yace. Dama tun kafin ta isa yayi masu waya yace wata zata je ga abinda yakeso ayi mata. Bata isa gida ba sai wajen ƙarfe biyu na rana. Koda takai wajen wayam babu kowa. Mota yazo ya kwashe kayan su Inna sun tashi. Makwabta Rumasa'u ta shiga tana tambaya inda suka je.

mamaki ya kamasu, kawai dai suka amsa da sun koma gidansu mana. Koko ta mance ne. Ita harga Allah bata san da maganar tashi ba, saita tambaya gidansu a wani gari. Duk tsammanin ta tana ganin kamar haya suka kasa biya an koresu kauye yanzu zasu chan Zaria gidan gado.

Fauziyya dama biki ya kawo ta Kaduna, tana zaune saita tuna da yar uwanta Auta. Anan ta tuna abinda tayi mata lokacin haihuwan Al-amin. Koda yake ta saba shiga Kaduna, amma tanada hidima. Wannan karan ne dinner sai wajen bakwai na yamma. Sai tace ma Salima tana zuwa, direba tasa ya kaita chan gidan datake tsammani Auta take zama. Koda ta shiga bata ga kowa ba.

Haka ta tambaye wani yaro dayake wasa bakin gidan, nan aka ce ai an siyar da gidan kuma Mallam Salisu sun tashi. Tambayar sa tayi ko gidan kansu suka koma. Tana so taji ko Auta ta goge ko tana nan a matsiyaciyar data sani. Yaron yace bai sani ba, Saboda shi dai yasan Malam yana koyarwa a firamari.

Daga wannan kawai Fauziyya ta tabbatar da cewa Auta tana cikin talauci, abin kuma yayi mata daɗi sosai. Nan tayi mata fatan ta dulmiya cikinsa tunda ta sanya mata leshi da Atampha, balle akan zancen har mijinta Alhaji Sani yayi hushi da ita lokacin, kiris da aurenta ya mutu. Zata shiga motar ta kenan saiga Kankana ta fito daga makota jikinta a sanyaye. Kwata kwata batada tudun dafawa. Ga ƙawar Hajia Salima wanda bata ƙaunar ta balle tace zata gidan ta kwana, gasu Inna sun tashi sun barta. Bawai ma taso ta bisu bane. Sannan Dr Abdallah baya so ya karɓe ta.

Gaban Kankana ne yayi mugun faɗi, da sauri ta juya zata koma inda ta fito. Daka mata tsawa Fauziyya tayi yasa ta tsaya, “Dan ubanki ina zaki? Yar banza kawai ! Zo nan? Shegiya jibeta kamar ƙanzo sai warin talauci.”

Gwiwa babu ƙarfi Rumasa'u taje, harara Fauziyya tayita binta dashi kafin tayi tsaki, “Dan ubanki maimakon ki kama talaucin ki, ki rufawa iyayen ki asiri a'a kina chan kina bin Hajiyoyi saboda badala. Chan ne gidan ku?” ta kalle inda Rumasa'u tafito. Ita ta ɗauki alwashin saita kai ƙarar ta wajen iyayenta. Yarinyar ƙarama ce har tasan daɗin kuɗi tana bin Hajiyoyi.

“A'a wallahi,” Rumasa'u tace bakinta yana rawa. Duk ta muzanta.

Tsaki Fauziyya tayi sai ta kalle gidan su Auta, “Kinsan wanda ta tashi a gidan nan? Yar uwata ce nazo kuma ban gansu ba,” tace tana yatsina fuska kamar tanajin warin kashi.

DIYAR DR ABDALLAH Donde viven las historias. Descúbrelo ahora