Fifteen - Ƙarfi Yaci

Comincia dall'inizio
                                    

"No besty, bazan saka rayuwar ki cikin hatsari ba. Kinsan ana kidnapping koh?" ta faɗa damuwa ƙarara a muryanta. Takaici ne ya kama Rumasa'u, ina ruwan Latisha da lafiyar ta. Meye takeso ta hanata zuwa wajenta? Ita tace zata ai, balle kuma ita datake kaiwa war haka a waje tareda yan kungiyar One Love.

Tana cikin tunani sai Latisha ta sake magana, "Bari na aiko maki driver da wasu abubuwa ba yawa,"

"Kai Besty amma nagode sosai," ta faɗa da karfin gaske cikin murna. Ji tayi dama tasan Latisha tun muddin rayuwarta. Amma ko yanzu ma bata ɓaci ba, zasu iya zuwa a haka.

Ba'a yi minti talatin da wayar ba saiga mai gadi yana iso da Rumasa'u, koda taje miƙa mata kaya yayi ninkin ba ninkin ta wuce tana murna. Cupcakes pcs shida ne daya sha icing da pancakes sai roban ice cream biyu. Ba abinda Kankana taso gani ba kenan, Anan ta duba kayan tas bataga kuɗin ba.

Rahina ce ta shiga ɗakin a natse, daga ɗakin mamanta take wanda yanzu nan tafi zama. Tazo ta haɗa kayan da zatayi amfani dashi gobe ne. Koda ta buɗe durowa bataga kuɗi ba. Hankalin ta ya tashi saboda kudin mutane ne, shiru tayi tana so ta tambaye Rumasa'u ko ta tayata gani. Amma kuma tana ta fargaba, domin Rumasa'u batada mutunci ta gaya mata babu daɗi.

A hankali tayita bin durowa tana dubawa babu kuɗi babu dalilin su, har kusan sha biyun dare lokacin, sarai Rumasa'u tasan me take nema amma tayi banza da ita. Roba biyun na ice cream ta shanye sai taci cup cakes hudu da pancake biyu. Yanda take ci kamar mai cutar yunwa. Koda ta gama jacuzzi ta shiga ta sakar ma kanta ruwan zafi, data fito saita ɗauki wani night gown ɗin Rahina wanda ta mayar nata tun zuwan ta gidan ta saka.

Malalewa tayi akan gado bayan ta ƙara sanyin AC, anan barci ɓarawo yayi awan gaba da ita. Ita kuma har lokacin Rahina bataga kuɗi ba kuma ta kasa tambayar Rumasa'u, anan ta yanke shawara gwara tayi mata magana idan tasan inda yake ta nuna mata. Saboda yau barci zai ƙaurace mata idan bata gani ba.

Da sanyin jiki taje jikinta yana rawa ta tsaya gefen Rumasa'u dake munshari, a hankali ta taɓata tana mata magana, "Rumasa'u !" ta kira sunanta a natse. Ta farka amma bata tanka ba saida Rahina ta sake.

"Menene ?" tace cikin faɗa.

"Dan Allah kiyi haƙuri, ina neman wasu kuɗi ne shine nace ko kin tayani ganin su?"

"Shine kika tadani cikin dare?" ta soma masifa, sai kuma ta tuna cewa ita ta ɗauka gwara ta kwantar da kai.

"Ni na ɗauka nayi amfani dasu, gobe zan baki idan na samu wasu kuɗi danake jira," tace tareda komawa. Idan ran Rahina yayi dubu toh ya tashi. Rainin wayon nan bazata taɓa dauka ba. Rumasa'u tana wuce gona da iri kuma daga yau bazata barta ba.

"Wai meyasa bakida mutunci ne? Duk abinda nake maki baki gani? Wallahi kiyi maza ki fito min da kuɗina koh nayi maki rashin mutunci." tace tana huci gabanta sau bugu yakeyi jirgi.

"Jar uba ! Uban me kika taɓa min ?" Rumasa'u tace a hasalce, "Ni kike zagi akan abin duniya? Kinyi asara Bulala... Kinyi asara!!" tace tana watsa mata mugun kallo, "Koko sacewa nayi, rance ne fah kuma zan biyaki,"

Rahina runtse ido tayi saita sake budewa, takaici ke dawainiya da ita, tasan tunda kuɗin ya shiga hannun Rumasa'u ta lashe. Amma saita ta koya mata darasi.

"Koki bani kuɗina ko yan sanda su shiga tsakanin mu, kinji na gaya maki," tace tana nuna mata yatsa tareda jijiga duk wani sansa na jikinta, tana watsa mata harara.

A fusace Rumasa'u ta ɗago tareda sauka daga gadon, kiris ya rage mata data saka ma Rahina hannu, "Yo kutumar ubanki Rahina! Nace bura ubanki! Naci banza!! Nace naci banza dan ubanki!!! Ni har zaki nuna ma yan sanda!!! Babu wanda ya isa ya kamani duk faɗin Najeriya. Kinsan dawa nake harka kuwa?" anan ranta yayi sanyi data tuna amintan ta Latisha.

"Wallahi ko ki bani kuɗina ko ki wahala," tace cikin masifa.

"Me zakiyi? Nafi karfin ki Rahina wallahi zan nakada maki kashi cikin daren nan,"

Mamakin karfin halin Rumasa'u tayi, wai ta sace mata kuɗi tana zagin ubanta. Wayanta taje saman mirror ta ɗauko, bafa yan sanda zata kira mata ba. Saboda tasan cewa zata tozarta su Inna idan tayi haka, itama bazata so ayima iyayenta haka ba. Kawai zatayi wayar ƙarya ne. Ita kuma Rumasa'u tana ganin haka tazo da sauri ta fizge wayan ta ratsa a ƙasa tana huci.

"Muga tsiya," tace.

Wayan dubu ɗari uku sai gashi a ƙasa screen ya tarwatse, aikam nan Rahina ta ɗauketa da mari. Nan take dambe ya kacame masu sukayi ta bugun juna.

"Shegiya yar matsiyata, yau saina hallaka ki," Rumasa'u tayita nanatawa tana dukan Rahina. Dayake Rumasa'u tafi jiki sai ta fi samun galaba kanta. Aikam anan Rahina tayi zuciya ta fizgo igiyar laptop. Nan ta zabga ma Rumasa'u mai kyan gaske a bayanta. Nan ta dare baya, ido ya fito ta soma ihu. Daga nan Rahina ta soma cin wasan, lailaya ma Rumasa'u jiki tayi sosai ta bulala. Duka baƙin cikin data ke kunsa mata yau ta fansa.

Yan gidansu Rahina ne suka faɗo da sauri suka raba su, sai a lokacin bakin Rumasa'u ya dawo, "Ku barni da ita na koya mata bariki," take cewa a bayan mai aiki.

Rahina fita tayi tabar ɗakin, batayi hawaye ba banda kukan zuci. Rumasa'u ta gama ƙure ta. Harta kai corridor saita dawo, "Ki kwashe kayanki ki tafi gobe," tace mata tana nuna yatsa. Dama taso tace ta tafi yanzu amma ta tausaya mata.

Tsaki tayi mai bala'in ƙara, "Banza tafi nono fari," tace sai taje ta ɗauki iPhone 11 ɗin Rahina wanda take amfani dashi a matsayin nata. Nan tayi ma Latisha saƙo ta WhatsApp domin tazo ta ɗauketa daga wannan kazamin gidan. A lokacin Latisha minti uku kenan da saka status na ƙafanta wai ta saka sagem. Saƙon Rumasa'u yana shiga sai ta sauka.

Rumasa'u tana kiranta kuma taji wayanta a kashe, bata kawo komai ranta saboda babu mamaki tana gama saka status ta kashe waya tayi barci. Haka Rumasa'u tayita haɗa kayanta cikin daren. Itama idan Rahina bata sani ba ta gaji da zama cikin gidan.

Koda asuba yayi ta gama kwashe kayanta tsab, har lokacin number ɗin Latisha bai shiga ba. Haka tayita fita da kayanta tareda taimakon masu aiki. Bata sake ganin Rahina ba tun sanda suka gama dambe. Dama tace saita koya ma Rahina darasi, anan ta kwashe turare uku masu tsada, saita haɗa da abaya ɗaya. Sannan ta shiga bayi ta kwashe shampoo da shower gel ta tafi dasu.

Data zo daukar jakarta na karshe, sai taga zanin gadon Rahina yayi mata mugun kyau, balle purple ne kuma kalar ta. Nan ta yaye shi tas da pillow case tayi gaba dasu tanayi tana Allah yayi wadai da Rahina.

Gidansu Inna ta koma kai tsaye kafin anjima Latisha ta farka daga barci domin ta zo ta ɗauketa. Sanda ta isa Mallam yana sanye da wani sabon ɗinkin sa dayayi, rabon daya dinka kaya shekara biyar kenan saidai a bashi. Fari kayan ɗinkin simple yayi kyau angon Inna.

Suna zaune dukansu akan tabarma harda Aliyu, Fa'iza ta haɗa masu ruwan shayi sannan ta soya kwai suna ci da biredi. Ga kuma raguwar shinkafa da wake da kayan ciki ragowar na jiya Inna tana ci saboda bata fiye san shayi ba. Itama Fa'iza haka take bata wani damu da shayi ba, Indomie ne ta dafa tana cin abinta.

Kankana ne ta shigo a hargitse kamar an haƙota daga yaƙin badar, kallon mamaki take masu yanda suke liyafan abinci hankali kwance.

"Sun koreni saboda rashin mutunci," tace tareda fashewa da kuka domin su tausaya mata. Yadda taga suna annashuwa dole ta ƙulla makirci kafin su baranta da ita.

"Na shiga uku ni jikar Habiba!" Inna tace cikin takaici tana tafa hannayenta.

Shikam Mallam ko ɗagowa baiyi ba balle ya kalle ta.


Wannan kenan !

#Naseera
#Rumasau
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated

Ainakatiti 💫

DIYAR DR ABDALLAH Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora