Fourteen - Rarrafen Carpet

Start from the beginning
                                    

“Yaushe zanzo na gaishe da Daddy,” Rumasa'u ta gayyace kanta gidansu Latisha domin ta lura an shawaba ta. Duk zance tana faɗin Daddy ɗinta bata dai faɗi sunan maman ta ba.

“Ai baya nan amma nan da jibe zai dawo, yana Amsterdam yanzu,” tace damuwa cikin muryanta. Daga dukkan alamu tana kewar daddy ɗinta.

Anan suka gama zance su kala kala, Rumasa'u ta riga ta ɗauki alwashin dole ta ƙulla aminta na haƙiƙa da Latisha. Ta lura yarinyar batada matsala kuma bata gaji tsiya ba kamar Rahina. Abin da yafi bata takaici da Rahina taga alert ɗin dubu ɗari ya shigar mata waya. Shine tace ta ranta mata dubu hamsin domin tanaso tayi ankon wata sabuwar aminiyar ta. Amma Rahina ta hanata domin baƙin hali.

Tasan tabbas da Latisha ne bazata hanata ba. Sai yanzu da gane mutane kaɗan ne idan suka bar talauci suka koma arziki suke barin tsiyar dake jikinsu. Koda yake su Rahina basu taɓa talauci ba, dama aji ya hada su Islamiya kuma duk makaranta akwai yaran talaka dana masu kuɗi.

Kashe gari Latisha ta saka wani hoto tana zaune akan dinning table da kofin shayi. Track suit ne wanda ya tsaya dai dai cibiyar ta sai dogon wando, shi amma ya rufe cibiyar. Dayake tanada yalwataccen gashin kai haka ta ɗauki hoton babu kallabi, saita saka caption "I miss Paris"

Rumasa'u batayi wata wata ta ɗauki hoton ta saka a nata shafin, anan Latisha ta bita private tana gode mata.

"Haba besty, babu damuwa mun zama ɗaya yanzu,” tace tana washe baki. “Saidai rigar ki tayi min kyau,” ta sake faɗi.

“Ai ba tsada, $100 na siya a Walmart. Ba wani designer bane. Gucci ne gama gari,” ta faɗa cikin ko in, “kalar ce tamin yasa na ɗauka. Idan kinaso zan ajiye maki.”

“Kai besty harda dawainiya,” ta faɗa kamar bata son rigar alhalin shoki ta miƙe tanayi.

“Ina da wannan abubuwan, kuma bana fita balle na saka su. Gashi kuma banida ƙawaye da zanba.... Idan kina so akwai jakar Alexander Mc Queen duka saina haɗa maki dashi, saidai kiyi hakuri baida wani tsada shima $800 na siya,”

Nan take Rumasa'u tayi fito saboda jin daɗi kuma kamar ta ɗuka tayi sujjada dan murna. Soyayyar aminta ta da Latisha ya shiga ranta kana haushin Rahina takeyi. Jibe rannan danta saka mata abaya shine ta kanne fuska.

Bayan sun gama wayan sai Rumasa'u ta kwanta tana tunani kala kala yadda zata kwakule Latisha. Yarinyar akwai sangarcin ga rashin wayyo. Ko maganar ta cikin shagwaba takeyi kamar zatayi kuka. Anan Rumasa'u ta ɗauki alwashin zata koya mata darasin da bazata taɓa mancewa ba. Zatayi mata welcome to Nigeria inda bazata sake yarda da kowa ba.

Anan dibara ya faɗo mata, saita saka "Goodbye fans" a status ɗinta. Latisha wanda koda yaushe batada aiki tana online har cikin dare saita bita private domin taji dalili.

Sai Rumasa'u tace wayanta yana bata matsala, haka kurum sai tayita kashewa na rashin dalili. Gashi kuma tanada issue da account ɗinta balle takai gyara,”

Latisha bata kawo komai cikin ranta ba, tace mata nawa ne gyaran. Anan tace dubu dari da ashirin ne. Yanzu tanada cash 20k a hannunta. Latisha tace kada ta damu zata bata kuɗin.

Anan ta soma bata labarin wani saurayin ta data tsana. Jiya yazo ya bata dubu dari biyu, abin yayi mugun ɓata mata rai saboda ya raina ta. Ita sanda take Paris bai kai kuɗin datake gyaran gashi ba. Harda hoton sabbin yan Naira dari biyar ta tura mata ta gani.

Da rawar jiki Rumasa'u ta kirata a waya, haƙuri ta soma bata. Ita kuma Latisha sai masifa takeyi, tanata cewa bata san raini. Ita ba abin wulakantawa bane da zai miƙa mata 200k. Sai tace idan ta fita zatayi ma Rumasa'u deposting cikin account ɗinta. Ganin kuɗin cikin gidan yana sakata ruɗani da tashin hankali. Rumasa'u taso tace mata zata je ta karɓa, sai kuma ta tuna abin babu aji. Gwara ta haƙura har a saka mata kafin Latisha ta gane akwai tsiya tareda ita.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now