Chapter 15

173 27 0
                                    

Karasowa tayi ta zauna kusada mom gabanta na fadi dad yayi gyaran murya yace "wannan shine sabon manager bank din sunansa haidar" Wanda aka kirada haidar Sai wani Smiling yake

Wani kallo jidda ta watsa masa tace "Sannu"

"Yawwa sannu" ya fada yana mata wani irin kallo.

dad yace "Zaki iya tafia daki muayi magana gobe" tashi tayi ta harari haidar don yadda taga yana kallonta taji wani iri

dakinta ta shiga ta aje jakarta kan gado abinda jallal ya fada mata ta tuno wani murmushi ta saki har mai aikinsu azumi ta shigo bata sani ba saida ta taba ta.

"Anty" sannan ta dawo daga duniyar tunaninta sai ta wani hade rai

"meya faru?"

"Mom ce tace in kiraki kici abinci"

"Toh aninan zuwa" da sauri azumi ta bar dakin

jallal kam tunda ya koma gda kwata kwata ya kasa sukuni sai tunanin amsar da jidda zata bashi. Dakin kakarsa yaje suyi hira ko hankalinsa zaidan kwanta

jidda data fita parlour dinning ta nufa ta zauna tafara serving ma kanta abinci kadan ta deba a plate ta fara ci kadan kadan kamar wanda aka saka dole a haka ta dinga ci harta gama tashi tayi taje tayo alwala daman lokacin magrib tayi sannan tayi sallah tana idarwa ne ta kwanta
kan gado tadan lumshe idonta ringing din wayarta taji daukan wayan tayi ta duba wake kiranta

Wani murmushi ta saki saida wayar ta kusa katsewa sannan tayi picking

"Hello"

Ta bangaren jallal shima murmushin yakeyi "Dafatan kin isa gda lafia" cikin siririyar muryarta ta amsada "Lafia lau"

"Kinci abinci kuwa?" Mamaki ne ya cikata wai ita ke magana da wani babu zagi ba fada.

"Eh naci dazu na gama ci"

"Shine baki ajemun nawa bako" dariya ne ya kauce mata.

"Au dariya kikeyi ko dagaske nake fa tace karka damu za ajema next time" sun sha hirarsu har kusan isha'i kafin sukayi sallama murmushi jidda ta sakin ma kanta.

tana gama wayar ne azumi ta shigo wai ana nemanta.

"Anty ana neman ki a waje" jidda da mamaki ya kamata. Wa kuma zaizo nemanta.

"Waye ne?"

"Nima bansanshi ba"

"jeki ina zuwa" cewan jidda

ajiyar zuciya tayi tace kodai jallal ne yazo bai fada mun ba tashi tayi ta saka hijabinta ta fesa turare ta fita

data fita harabar gdan da murmushi a fuskanta karasawan dazatayi taga ba jallal bane illa haidar.

guntun tsaki taja ta karasa wajen shiko sai wani washe baki yakeyi.

"Kaine kake nema na" yayi murmushi "eh nice gimbiya jidda" kallonshi tayi sama da kasa.

"Mallam ni ba gimbiya bace ka kirani da sunana jidda ka gane" ya sake washe baki

"duk yadda kika ache"

kallonsa tayi "To ka aika a kirani meya faru?" sai ya fara sosa keya

"Baa fada maki ba"

cikin rashin fahimta jidda tace "baa fada mun ba"

"Dad dinki ne ya bani dama inzo mu fahimce junan mu kuma ni kinmun magana ta rage naki"

wani kallo ta watsa mai direct tace "ni kuma baka munba ba ni inada wanda nakeso saboda haka karka bata lokacin ka" bata jira maganarsa ba ta wuce ciki
tana shiga parlour ta hango mom a zaune ta karasa wurin 

"mom wai yaushe dad yace
mutumin nan yazo mu sasanta?" Tana fadin maganar tana yamutse fuska.

Gyara zama mom tayi "na ma manta dazu yace in fada maki zaizo ina fatan dai kun dadaita" tsayawa Tayi tana kallon mom "mom meyasa" dagowa tayi ta kalli yar nata

"ban gane meyasa ba bazakiyi aure bane ko kuwa kinfi so ki zauna muyita zuba maki ido" kamar zatayi kuka

tace "mom..."  katseta tayi "inafatan dai baki masa rashin kunya ba dan na sanki" bata bari ta amsa ba tace

"wuce dakinki dare ya riga yayi"

juyawa tayi ta wuce dakinta ta kulle zama tayi kan gado wato abinda dad keson mata kenan
yanason ya hadata da wani girgiza kai tayi thats not possible ajiyar zuciya tayi ta kwanta text ne ya shigo mata daga jallal dubawa tayi taga goodnight text ya mata murmushi ta saki wanda ya kara fito mata da kyanta




**
hello readers kuyi hakuri page din gajere ne hakan ya faru ne sakamakon matsalar da wayata tasamu. Ina fatan kuna jindadin labarin nan. Na fara sabuwar littafi mai suna "Rayuwar Abida" kuyi adding to library dinku kada ku bari a baku labari.

Sai kun jini😉

Jidda Da JallalWhere stories live. Discover now