Chapter 8

173 26 0
                                    


Wa zai gani sai mallam ja'afar Juyawa yayi har ya kusa fita kofar gidan mallam ja'afar yace tsaya jallal akwai maganar da nakeson yi dakai ran shi ya Kara baci Juyowa yayi ya kalle shi yace bana

Jin zan iya tsayawa muyi magana dakai bayan duk abubuwan da Kayi mana nan take idon jallal ya

Kada yayi ja. Wanda aka Kira da mallam ja'afar yace nasan abinda nayi ban kyauta ba nayi nadama shiyasa nazo don Neman yafiyar Ku abinda ya faru ya Riga ya wuce

Wani irin kallo jallal ya masa yace "kana tunanin zan manta abinda Kayi mana nida mahaifiyata ko

kadan ban manta ba for all these years irin wahalar da muka sha duk Baka sani ba saida muna
zaune lafia shine zaka zo wai kana Neman yafiyar mu"  bai jira maganar sa ba ya fice ya bar gidan

Inda ya bar abokinsa Yusuf ya Nufa ya mika masa kudin Yusuf ya lura da fuskan jallal ba kamar yadda ya gansa dazu ba.

"Lafiya kake kuwa Man." Cewan Yusuf. jallal ya Kakaro murmurshi  "Ba Komi muje shagonka."

Ta bangaren mallam ja'afar kuma tunda jallal ya tafi bai motsa ba gaba daya jikinsa ya mutu shi kanshi yasan abinda yayi bai kyauta ba kakarsu ce ta fito wato mahaifiyar mallam ja'afar daman so

take ta barsu suyi magana taba shi tayi a shoulder tace nasan da wuya amma ka dan bashi lokaci

nasan zai sauka girgiza kanshi yayi alaman tohm yace hajia zan tafi kudi ya ciro ya mika mata tace "Aa ja'afar ka aje kudinka bazan karba ba."  ta juya tayi shigewarta ciki. Shima ya juya ya tafi ransa ya nai masa zafi

Jallal ne zaune da Yusuf a shagonsa jallal kamar karya fada ma Yusuf amma yaga idan ya fado shi ko zai Samu sauki a ransa da ke masa zafi yace "Yusuf yau baba Yazo." ido Yusuf ya zaro babanku!

Jallal ya ce eh ya basa labarin maganar da Sukayi Yusuf yayi ajiyar zuciya yace

"jallal shawaran dazan Baka shine ka sake tunanin kan maganar nan tunda ya gane kuskuren sa har Yazo Neman yafiyar ka koma meye ka tuna mahaifinka ne" ya dafa shi a shoulder Sannan ya tashi ya je saida ma customer Abu

Mallam ja'afar mahaifin jallal ne suna zaune a garin kaduna shida matarsa Fatima suba masu kudi bane amma suna da na rufin asiri anan ne aka haifi jallal lokacin daya kusa kammala secondary ne aka Haifa kanwarsa wato Noor suna zaune abinsu cikin kwanciyar hankali wani lokacin mahaifinsu Yazo musu da albishir Akan ya Samu sabon aiki a garin Kano sunyi matukar

farin ciki har babansa yace idan ya gama secondary zai kaisa university BUK jallal yaji dadi
lokacin kuma Noor na yar shekara daya.

Watan da mahaifinsu  ya fara aiki yana zuwa weekend yana dubasu in Yazo Friday ya koma Sunday haka dai suke zaune cikin kwanciyar hankali da son juna.

After 3months abu suka chanza sai ya daina zuwa saidai ya turo kudi daga baya ma ya daina turo ma insun Kira numbarsa baya shiga. Daga baya ma dasuka nemashi suka rasa suka daina. nan ne Suka shiga cikin wahala dan aiki ne jallal yakeyi bayan ya dawo

makaranta su Sami na ci maman ma dan kudin da take dashi ta fara saida Kayan Miya suna dan
samun naci Shima dan kananan aikin daya keyi yake dan Samu ya kawo ma mahaifiyarsu
abokinsa ma nadan taimaka masa ba laifi Yusuf abokinsa ne tun suna yara

Wani rana mahaifiyarsu ta tashi da wani ciwo dan Chanjin dake hannunsa ya nema napep ya ka ita asibiti nan ma akace baza ayi mata treatment ba sai ya kawo kudi gashi kudi Mai yawa ba laifi

haka jallal ya dinga rokon doctor yana kuka ga Noor itama tanayi amma Ina da sauri yaje gida ya

duba dan asusun sa dayake dan tara kudi dubu 5 kawai yasamu gidan kakarsu ya je mahaifiyar
mallam ja'afar ya zayyana mata abinda ya faru da sauri ta mike taje wurin neighbor dinta rancen
kudi nan tace bata da shi duk inda sukaje basu Samu ba wasu dan Kayan dakinta ne taje ta saida

Suka Nufa asibiti Suka Bada kudin aka fara mata treatment jallal yayi trying numban babansu amma bai shiga

Bayan an bata gado Likita ya kirasu ya fada musu matsalar ta cewa ta kamu da hawan jini nan
take hawaye Suka Zubo masa aka rubuta musu magani Suka siya da Chanjin daya rage

Bayan kwana biu har ta samun sauki Suka koma gda duka harda kakarsu ranar mahaifiyarsu na

zaune a daki da Noor jallal yaje makaranta kakarsu kuma taje makwopta dan Nokia dake hannunta

tayi dialing numban ja'afar taci sa'a ko ya shiga saida ya kusan katsewa akayi picking muryan

mace Taji tace inason magana da ja'afar ta wayan tace baya nan matarsa ce Fatima Taji kamar an

watsa mata ruwan zafi kasa magana tayi Anata hello hello Ina tayi nisa wani hawaye ne ya fara

Zubo mata nan take ciwon ta ya tashi ta fara numfashi sama sama daidai lokacin jallal ya shigo

yaganta a kasa tana numfashi sama sama ya fara kuka yana kiran sunanta in healer ta ya dauko ya

kare gaba daya ya rude ya fara kuka umma ki tashi ya daura kanta kan cinyarsa yace umma Bari naje na siyo magani zai tashi ta rike masa hannu tana magana dakyar tace jallal akwai abinda Zan

fada maka yace umma ki Bari idan na dawo saiki fada mun tace ka kulada kanwar ka jallal Komai ya faru dakai ka tuna mutuwa duniya nan ba komai bane mahaifinku..... maganar da bata karasa ba kenan tace ga duniyar Ku wani ihu jallal yayi yana umma karki tafi ki barmu Noor ma kuka

takeyi daidai lokacin ne kakarsu ta shigo salati ta farayi itama tana kukan

Bayan rasuwar mahaifiyarsu Suka Yanke shawaran Barin garin Suka kwashe kayansu wurin

kwashe Kayan ne sukaga wayan umma jallal ya kunna ya ga last call dinda tayi kafin ta rasu

numban mahaifinsu sai ya Kira muryan mace yaji yace dan Allah inason magana da ja'afar Matan

tace Kai waye yace ni Dansa ne yaji tana cewa gashi wai danka keson magana dakai yace nayi

latti kice ya Kira anjima ita ko ta fadi abinda yace mata idon jallal ne ya kada yayi ja yanzu abinda

mahaifinsu zai saka masu kenan sai ya tura text kamar haka : Salam baba daman inaso na fada

maka cewan umma ta rasu sanadiyar ciwon zuciya kuma zamu bar garin mu Ina fatan sakon nan

zai ISA gareka yayi kuka sosai

Bayan sun koma Abuja ne Suka dan Samu gidan dan madaidaici nan ne ya fara Neman aiki

yanayi har ya karasa secondary sa kuma yasa sister sa a nursery a hakane yayita struggling har ya
kamalla degree sa gashi da kokari ko da ya gama ma saida yayi one year a gda kamin ya sami aiki a bank Dinsu Jidda har kanwarsa ta Kai University wannan kenan

* *

*

*

*

*

Jidda ce kwance kan gadon ta tana chatting da kawarta Maryam take tambayanta ya mutuminki

Jidda tace ke kam Maryam kinada naci muna Hiran mu kinzo kin sako wani ni Ina mantawa cewa Akwai wani jallal Maryam tace hmm... Fadi gaskia Jidda ta tura mata da wani gaskia zan fada maki Banda abinda na fada maki ni kinsan ma chatting din ya gundure ni am off.

Maryam tace "Haba mana friend daga magana kuma." yarda wayan tayi gefe daya ta kwanta ta lumshe idon ta tuna abinda ya mata tayi sai ta kara jin wani haushinsa a ranta da kudirin saita rama abinda ya mata. Bata gama thinking  ba Taji wayarta na Kara kamar bazata dauka ba saida ya kusa Katsewa ta duba taga mallam J sunan da tayi saving

tayi picking ta saka a kunne batayi magana ba maganarsa da Taji gabanta ya fadi yace hello tace

yes me ya faru daman na Kira ne na Sanar maki cewan bazan Sami zuwa aiki ba ran Monday

without knowing Taji tace meyasa ? Yace inason nayi dan tafiya ne tayi murmurshi ta gefe tace

hmm zanyi deducting one day absence din from your salary bata jira maganarsa ba ta katse wayar tana Mai tunanin abinda zatayi.


**
Toh readers ya kukagani. Kuna jindadi labarin kuwa? Don't forget to Vote and Comment.

Ma'assalam.

Jidda Da JallalWhere stories live. Discover now