Chapter 1

1.1K 49 0
                                    


Bismilahir-Rahmanir-Rahim

_*TSOKACI*_

"Wannan labarin 'kir'kirare ne ban yishi dancin zarafin kowaba nayishine don nishadantar daku da kuma fad'akar daku da fatan zakuji dad'in labarin nan kamar yadda nakejin dad'in typing d'inshi

Allah ya bani ikon kamala shi AMEEN.

**
Sau'kowa takeyi daga stairs d'in jirgi sanye take cikin wata ba'kar jallabiya mai tsada yasha decoration gata fara kamar baturiya yasa kayan ya kara mata kyau da bakin vogue glass data sa, tachi uban makeup da karamin lips dinta dayasha Red velvet tafiya take dai dai cikin ji da isa wajen wata mota ta karaso Mercedes-benz G class 2017 da kaga motan kasan da tsada.

muryan wani mukaji yace barka da dawowa hajia wanda aka kirada hajia ko tanka masa batai ba

kofar gaba ya bude mata ta shiga sannan ya sa trolley dinta a booth ya shiga wurin tuki ya tada motan.

wata unguwa suka shiga gate d'in wani makeken gida yayi horn aka bude gate din, gidan ya hadu iya haduwa babban gida ne sosai ga motoci manya manya irinsu BMW i8, Range rover sentinel, maybach 625.

Parking yayi a parking lot ya kuma zagayowa ya bud'e mata kofa wata farar mata ta fito daka ganta kasan mom d'inta ce don suna kama

"welcome my baby" ta fada,

wanda aka kirada baby itama sai faman murmushi takeyi wanda ya kara mata kyau.

Cikin wata sweet voice tace

"I really missed you alot mum"

wanda aka kirada mum tace

"I missed you too" shiga sukayi cikin parlour very cool ga ko'ina yasha decorations ga kujerun masu tsada.

"my jidda yanxu kije ki watsa ruwa sai kizo kichi abinci na dafa fav d'inki" cewan mom

jidda tayi dan murmushi tace

"wow mum youre the best love you"  ta haura sama toilet ta fad'a ta watsa ruwa ta fito. Trolley ta ta'bude ta d'auko wata purple material mai tsada yasha dinki ta saka gashi ya kamata amma bataji komi ba wurin mirror taje ta yi shafe shafenta creams masu tsada da perfumes masu kamshi tadanyi simple makeup ta saka purple lipstick batama yi sallah ba.

Saukowa tayi ta zauna a dinning abinci kala kala aka jera a dinning pepper chicken,yam bons,shawama da sauransu ga drinks kala kala sai wanda ta zaba dandanawa ta farayi daya daya tofarwa tayi tana hura bakinta tana 'kiran sunan mum mum da karfi mum da sauri ta fito tace

"What happened why are you calling me like this" Mom tambaya cikin damuwa.  cikin shagwaba tace

"Mum abinci is too salty ga yamballs dinda yaji mum bazan iya ci ba" da sauri ta haura sama ta tafi room d'inta.

Mum ta kira masu aiki cikin rawan jiki duk suka karaso cikin tsawa tace

"Waye yayi yam balls dinnan"

shiru sukayi saida ta sake ihu "bada ku nake magana ba wanda ake 'kirada Halima cikin rawan jiki tace

"hajia nice"

"bakida hankali ne kobance ki kula sosai wurin yi ba amma saida kika bata ma yata rai ko?, abinda nakeso dake shine ki kwashe ina da inaki ki bar min gida na sallame ki" ta fada da tsawa.

Halima wacce idanunta suka cika da kwalla tace

"Hajiya kimun afuwa bazan sake ba"saurin katseta Mum tayi.

"Rufemun baki banason inji wata kalma daga bakinki," ku kuma tana pointing sauran

"Wannan ya zama muku darasi don duk wanda ya sake bata ma 'yata rai sai nayi dealing dashi mtsww" ta fice ta barsu anan wa'inda gaba daya jikinsu ya mutu.

Dakin jidda ta shiga ta ganta a kwance kan gado tana kuka cikin tashin hankali mum ta zo ta sameta.

"My jidda me yasameki kike kuka ko baki jin dadi ne" jidda ta d'ago kanta ta kalle ta

"Mum ba abincin bane dakeda yaji bakina duk yaji" ta fada tana tabe baki, ajiyar zuciya mum ta saki.

"Ki kwantar da hankalinki na sallami mai aiki yanxu tashi muje in dafa maki wani" da shagwaba tace

"Aa mum bazan ci ba ni icecream nakeso" murmushi mum tayi

"Tohm shikenan bari insa a kawo maki yanxu dai ki tashi ki wanke fuska kinga yadda face dinki yayi looking pale" tashi tayi ta shiga toilet ta wanke fuska.

**
Kwance take  kan lallausan gadonta tana dannan waya numban friend d'inta tayi dialing

ringing biyu ta amsa

"Hello jidda how far"  amsawa tayi da  kalau kamar wanda akasa dole

"kinsan na dawo Nigeria"

"serious?"

"Kwarai kuwa" ta amsa a takaice

"Wow so nice na dauka zaki dam kara hutu ne a Canada"

"Kinga ba surutu yasa na kiraki ba kinsan me zanzo anjima sai muje ko"

"Haba jidda keda kika dawo yau kidan huta mana kwana biu" cewar kawar nata.

"Kekam idan bazaki ba shikenan let me be zan tafi ni kadai" ta fada cikin chanjin murya

"Haba jidda kinsan bamu hakadake yanxu dai idan kin shirya saiki biyo mu tafi"

**

So ga first Chapter nan.
Shin ina jidda zata da kawarta? ku biyoni danjin yadda zata kaya.

Wannan labarin na rubutashi da dadewa, amma ban samu posting ba a wattpad kasancewar losing dinshi da nayi, amma na samu wata ta tura mun zan cigaba a inda na tsaya insha Allah.

Jidda Da JallalOnde histórias criam vida. Descubra agora