Chapter 3

269 22 0
                                    

washegari misalin 10:00 na safe jidda sai sharara bacci take mum ce ta sa mai aiki ta kirawota

koda mai aikin ta shiga ta tada ta jidda ta fara zagin ta

"ke mahaukaciyan inace kina ganina ina bacci zakizo ki tadani how dare you" tanata masifa itadai mai aiki shiru tayi dan tasan idan tayi musu zata iya rasa aikinta saida ta bari ta gama masifan ta sannan tace

"daman hajia ce tace in kiraki breakfast is ready."

wani tsaki taja tohm.  "kice ina zuwa." tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka ta dauko wata shegiyar jeans da shirt ta saka

bayan ta gama ta yafa dan karamar gyele batamayi makeup ba amma dukda hakan tayi kyau

saukowa tayi ta nufi dinning don ci breakfast ga abinci iri iri kan dinning sai wanda ta zaba tea tahada mai kauri tace."mum ina bread ne?"

mum da mamaki tace "bread kuma? Keda bakicin bread"

cikin shagwaba tace "mum shi nakejin ci"

Kwada ma kande kira tayi wanda aka kirada kande da sauri tazo

"Gani hajia." Ta fadi cikin ladabi  "Dauko ma jidda bread." itama kanta kande tayi mamaki dan tasan jidda batacin bread baifi 2mins ba ta dauko ledar bread din ta ajiye tayi gaba abinta

jidda ko taci rabin bread din mum tace "Jidda na lallai yau kina craving for bread yadda naga kinci shi sosai." murmushi tayi ta tashi ta haye sama

*

*

*

*

*

"Abokina yane naga kwana biyun nan duk ka chanza me ke faruwa ne." wanda aka kirada aboki yace.

"kaide bari yusuf wata stupid girl na hadu da a hanyar dawowata daga kasuwa mashin dita ta bugi motarta waima Allah ya taimaken banji ciwo ba waima kaji rainin hankali itace at fault amma data fito instead ta bani hakuri ta soma masifa tana zage zage naso yin hakuri in barta tunda naga mace ce amma naga tayi crossing limits dinta nima na buda mata wuta na zazzageta na wuce".

"haba jalaluldin bai kamata kana tada hankalinka akan maganar nan ba, toh ita din wacece? yar gdan wa?" Cewar abokin nashi.

jalaluldin yai tsaki "ina na damu da yar gidan wacece nidai tamin na rama i don't care amma da ganinta kasan irin yaran masu kudin nan ne da suke bata 'ya yansu mu bar magana thinking of it yana sake bani haushi." Ya fadi yana fusge iska.

" wai ya  maganar job dinka ne?"

Ajiyar zuciya yayi. "jiya mukayi interview sunce zasu kiramu yanzu dai ina jiran yusuf."

"Toh Allah bada saa."

"Ameen, bari in tafi nasan kakata tana jirana zatace ban dawoba." Cewar jallal. sukayi sallama ya wuce

*After 1 week*

jidda sanye cikin wata lace dinta gazner mai tsada yasha dinki  taci makeup kamar ba ita ba. saukowa takeyi cikin taku daidai taga masu aiki sai aiki sukeyi mum ma kanta tana kitchen zuwa tayi ta tsaya kofar kitchen tace

"mum meke faruwa ne naga sai aiki akeyi."

"kekam jidda kinako da mantowa kin manta cewa yau sister ki da dad dinki zasu dawo."  lebe ya ciza

"Oh na manta mum yanzu suna ina?" Ta tambaya

"sahla ta kusa sauka don dazu ta fada mun nasan by now ma ta iso dad dinki kuma wai flight din dare zaibi so yanzu zakibi driver ne ku daukota ko kuwa."

"Eh mana mum yadda nayi missing dinta am eager to see her."

komawa tayi tadau handbag dinta da phones dinta ta dauko wani black spec ta saka ta fito yau da range rover sentinel suka dauka gdan baya ta zauna ta wani hade rai kamar wanda bata
taba dariya ba har suka isa Airport basu wani jima ba jirgin su sahla yayi landing. Sahla ta hango sistan ta da sauri taje ta rungumeta.

"I really missed you lil sis me too kinga yanda kika girma kin kara kiba." Cewar jidda tana pinching cheeks dinta.

"Da gaske sis."

"eh mana"

suka shiga mota suna hira irinta yaya da kanwa jidda tace "ina fatan kin taho min da tsaraba ta ko"

"eh mana sis na isa you will surely like the gift." saida suka biya ice cream shop suka sha ice cream sannan suka wuce gda

sahla tayi hugging mum dinta

"ya karatu?"

"Alhamdulillah mum wash mum I'm very tired where is my food?."

mum tayi murmushi "sarki abinci gashi a dinning kije kici ki koshi sai kiyi wanka ko"

"Okay  mum"

sahla ta debi abinci cikin plate taci hadda kari sannan ta wuce dakinta already an gyara mata dakin toilet ta fada ta watsa ruwa bayan ta fito ta saka doguwan rigarta na atampa ta fada gado sai barci

**

da sallama ya shigo gdan. gida ne dan madaidaci bai zarce ko ina ba sai dakin kakarsa ganinta yayi a zaune tana linke kaya har kasa ya duka ya gaida ta  "sannu da aiki kaka na dawo." Ta far'anta ta amsa masa  "yawwa sannu da na yanzu nake shirin in kiraka a waya naga baka dawo ba" yayi dan dariya da ya kara masa kyau

"gani na dawo kaka." zama yayi kusada ita yana tayata linke kaya yace "kaka bai kamata kina aiki ba abinda ga Noor nan zatayi."

"Aa jalal ina dan motsa jikina ne na zauna haka bana komi ita ke linke mun na aike ta makwobta ina linkewa."

suna cikin magana ne suka jiyo sallamar Noor ta gaida yayanta  kaka tace "jeki kichen ki dauko ma yayanki abincinsa" haka ko akayi ta dauko masa dambu ne yaci yace

"kaka hala ke kika girka wannan abinci?"

kaka tace "me ka gani?"

"naga yai dadi sosai kuma nasan noor bazata iya mai dadi haka ba" kaka ta dan rankwasheshi "me ka maidata ta iya mai dadi"

"kai kaka amma girki yayi dadi ur food is the best" duk sukayi dariya

After some hours

dad dinsu jidda ya dawo duk a gajiye saboda tafiyan dare dayayi saida yaje massalaci yayi sallar isha'i sannan ya dawo ya nufi part dinsa wanda ke kunshe da parlour, room, da toilet mum ta kai masa abincinsa bayan yaci ya huta su jidda da sahla suka zo suka gaida shi har zasu tashi dad

yakira jidda akan zaiyi magana da ita.

zama tayi tana jiran abinda dad dinta zaice gyaran murya yayi yace "jidda yanzu dai kin kammala karatunki ya kamata ki fara aiki. Na rigada nayi picking position maki  zuwa monday zaki fara zuwa office a bank dina a matsayin manager banason wasa ki rike bank dina da amana kuma zaayi hiring new employees banason inji wani problem kinaji ko. so monday zaki fara zuwa zaki iya tafiya"

jidda ta so ba yanzu zata fara zuwa office ba taso tadan huta amma ya ta iya dole tabi decision din dad dinta.

Jidda Da JallalWhere stories live. Discover now