Chapter 11

196 23 2
                                    

Jidderh ce ke shirin zuwa office ta Warke amma dukda ciwon kwana biu ne tadan rame data gama shirin ta sauko parlour ta gaida mom dinta Sannan ta Nufa dinning ta hada tea Mai kauri Tasha

Sannan ta ma mum sallama ta wuce yau range rover ta fita dashi don Dayan na wajen gyara Mai gadi ya bude mata gate data zo wucewa yace Ina kwana ta amsa masa ba wata masifa ta wuce har mamaki Mai gadi yakeyi don shi duk sanda ya gaida ta bata amsawa

Tana tukinta cikin natsuwa tayi so quite har ta isa wurin aiki ma aikatan wajen suna gaidata da

far'anta ta amsa suma mamaki ne ya cikasu wai yau Jidda ta amsa gaisuwa ba hade fuska

Tafiya take abinta cikin natsuwa har ta iso side Dinsu jallal nan ma Suka gaidata ta amsa musu

Sannan ta shige office dinta bata ma gama hutawa ba Taji knocking tace come in jallal ne rike da file a hannunsa yace good morning ba tare da ta dago ba tace morning yace ya jiki da yace mata Ya jiki sai Taji wani dadi a ranta wanda bata San dalili ba. sun danyi shiru na dan lokaci Sannan jallal yace "daman file dinda zakiyi signing ne na kawo" sai ta karba tace "ok amma zaka dan dawo anjima zan dan huta"

baice komai ba ya fita yana mamakin yau Jidda she's so quite ba masifan nan da take masa idan ya shiga office murmurshi yayi Sannan ya koma mazauninsa ya cigaba da aikin da yakeyi

Jidda saida ta dan huta Sannan tayi signing da kanta ta tashi ta Kai files din wani jiri ta fara ji jallal yayi noticing hakan kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru

Da ta koma office dinta ta zauna amma har yanzu tanajin dan jiri saita Dora kanta kan desk din na

dan wani lokaci kafin ta dago kan tasa hannu akai me yasa kwana biu nan kaina sai ya dinga ciwo

jakanta ta bude ta ciro maganin ciwon Kai ayukan sunyi yawa haka Shima jallal ga mutane masu shiga da fice a bank din

Drivern ta Kira Yazo ya kaita gida dan bazata iya driving ba between 45mins ya iso ya kirata tace masa gatanan zuwa mi kewa tayi ta kulle office din nata Sannan tafito batama yi glancing wurin su jallal ba ta fita sai gda

Jallal yaga wucewarta kwata kwata yau batayi wani hayaniya ba tohm meya sameta ko haryanzu

bata jindadi ne gashi batamayi mun magana ba duk wannan maganar tashi a zuciya yakeyi ba

amsarsu ajiyar zuciya yayi yace "I hope dai nothing is wrong" sai ya hada kayansa ya wuce

Bayan su Jidda sun isa gda ta Shiga parlour kenan ta hango mum da sahla zaune ta gaida mom Sannan tayi hanyar dakinta Jakarta kawai ta ijiye ta kwanta ko ciwon kanta zai dan ragu

Mom ce ta shigo dakin dan ta lura da Jidda ta shigo batayi wani magana ba, ba lafia kenan ta tasheta "Jidda my baby jikin ne har yanzu" Jidda ta shagwabe fuska "eh mum kaina ne kedan ciwo"

"Kinsha magani"

"eh nasha"

"tohm tashi kiyi sallah sai kici abinci ki kwanta in yaso gobe sai muje asibiti tace tohm kamar yadda mom tace ta tashi tayi sallah taci abinci Sannan ta kwanta

Mom ne ke waya da dad kan cewan ciwon kan Jidda haryanzu yace "kunje asibiti?" tace gobe zasu

"Allah Kara sauki gobe Nima insha Allah zan dawo" bayan sunyi sallama ta tashi sahla Wanda bacci ya kwasheta tana kallon film

**
Jallal ne a dakinsa tunani fal a ransa da thoughts yanzu wani Hali take ciki wayarsa ya dauko

kamar ya Kira kamar karya Kira sai ya jefar da wayar mtsww why do I care ne meke faruwa danine kwanan nan whenever I see her I can't concentrate meyasa ? Sai kuma ya dauko wayar yayi dailing number baiyi sa'a ba wayar a kashe sai yace to fa I hope lafia

Washegari Jidda sunje asibiti ganin likita yace stress ne da rashin Samun Hutu yayi prescribing masu magani Suka siya Sannan Suka tafi basu je gda ba Suka biya gidan kanwar mom hajia Khadijah sun dade a gdan Sannan Suka Kara biyawa gidan Kanin dad nan ma sun dade don Kanin dad yanada manyan yara age mate din Jidda sunsha hira har Jidda Taji dadi saboda a gda she's alone. ba kowa ni lokaci suke tareda sahla ba sai wajen magrib Suka dawo gda a gaje Jidda ta Baje a kujera sahla ma haka baifi 30mins ba sukaji salamar dad Suka masa Sannu da zuwa mom ta karbi Jakarsa ta Kai daki Sannan aka kawo masa abincin sa yaci ya koshi

Jidda ta tashi zata tafi daki yace "Jidda zo inason magana take"  zama tayi a hankali.

"naji wai dalilin ciwon kanki so na Yanke hukuncin zan saka sabon manager ke saiki huta for sometime"

Kai ta dago ta kalli Dad ido a zare

***
Too fa readers kuna tunanin jallal ya kamu da son Jidda ne (in my opinion Ina ganin ya folla�)

Jidda Da JallalWhere stories live. Discover now