Nine - Mabuɗin Zuciya

1.1K 182 24
                                    

Rumasa'u babu tsoro cikin ranta. Abinda ta sani shine ba wanda zai hanata zuwa gidan su Rahina. Idan su Mallam da Inna nada tausayi zasu kyaleta domin taje taci arziki. Zasu barta taje ta samu gatan da suka kasa bata.

Zasu barta taje ta samu rayuwar dayafi dacewa da ita, sannan kuma rayuwar data daɗe tana burin samun irin shi. Koda ta isa gida Fa'iza ta gani tana wanke ma Inna da Mallam kayan sawan su, sannan gefe nata ne idan ta gama ta haɗa tayi.

Bata ko kalle Fa'iza ba, wucewa tayi ɗaki tareda ledan dake hannunta. Dankalin turawa ne da kwai wanda tayi ma kanta takeaway. Sam bazata iya cin abinda suka dafa ba. Inna tana zaune a ƙasa tana tsinci tsakuwa cikin shinkafar hausa. Aliyu ne ya auno masu local uku yace su dafa. An bashi wani kwangilan photocopy kuma kuɗin ya fito. Harda nama kilo ɗaya ya siyo masu da kayan miya.

Taɓe baki Rumasa'u tayi abin bai birgeta ba, wai ace har yanzu suna cin shinkafar hausa. Duniya ta daɗe da barin su a baya. Gefe ta zauna ta buɗe ledan abincin ta, dama bata masu tayi amma yau tace bari ta gwada basu. Tunda idan ta tafi daga yau ba zasu sake gani ba.

"Inna ga dankali da kwai fah," tace tana murmushi.

Ɗago wa daga abinda take kallo Inna tayi, saita soma murmushi itama. "Ki ci abin ki Ruma, nagode," saita kafa kanta akan abinda takeyi. Taɓe baki Rumasa'u tayi. A duniya bata taɓa ganin hali irin na iyayenta ba. Basuda shi, kowa ya sheda basuda shi amma sun fi kowa girman kai. Haushi ya ƙara turnuke ta.

"Inna... Dankali ne fah da kwai!" ta faɗa cikin murya mai karfi. Sannan ta tura mata gabanta domin taci. Murmushi Inna tayi, ita ta ɗauki alwashin bazata ci abinda bata san inda ya fito ba. Babu haufi Rumasa'u tafi karfin su. Kuma ranta yana mata ƙuna yadda sukayi sake abin ya faru haka. Bazata daina binta da addu'a ba

Addu'a ne makamin mumini kuma bazata fasa ba. Kallonta tayi fuska babu annuri, "Yi maza kije ki haɗa min wuta ga itacen na baza domin su sha rana."

Rumasa'u taso tayi mata gardama saboda ita yanzu yar babban gida ce amma babu fuskan yin haka. Haka ta miƙe jiki babu ƙarfi ta fita tana gunguni. Koda ta fita waje, bokatin da Fa'iza ke wanki yana kusa da murhun. Nan tasa ƙafa ta hamɓare shi. A firgice Fa'iza ta dago tana kallonta.

Itama Inna saida ta fito tana zare ido, "Lafiya?" bata ko amsa suba ta soma haɗa wutan. Kana ganin kasan bataso tayi ne. Ranar girkin tas Inna ta bar mata shi. Ita ta dafa shinkafar tareda tafasa nama. Fa'iza takai markade sannan tayi miya.

Bayan Isha ana zaune duka a falo, Mallam ya kunna masu radio suna saurare. Shi kuma Aliyu yana dan hira jefi jefi nan yake cewa ya kamata akai gaisuwa wajen yarinyar dayake neman aurenta.

Anan itama Rumasa'u ta samu kwarin gwiwa. Murmushi ta soma yi na munafunci tana sosa kumatu.

"Dama inaso na koma wajen su Rahina da zama saboda yafi kusa da makaranta."

Gabaɗaya kallonta suka soma yi, kowa da abinda yake ayyanawa cikin ransa. Mallam ne yayi na Maza yace, "Bangane zaki koma ba."

"Dama naga nan mun takura muna bangaje juna, shine nace bari naje chan. Tunda dai yafi girma zan fi wataya wa kuma gashi sunada mota duk zamu makaranta cikin sauki,"

Idan ran Mallam yayi dubu, toh yayi mugun ɓaci. A yau Rumasa'u tayi masa mugun cin fuska. Ta karanto mashi karatun daya daɗe yana yinma kansa. Ta gaya masa cewa ya gaza a matsayin sa na uba. Zuciyar sa yana mashi raɗadi. Da kyar ya iya fitar da kalamai wanda yasan ba tasiri zaiyi wajen taba.

"Me kike nufin da gidan yafi girma kuma sunada mota?"

Itama sai a lokacin ta gane nauyin maganar da tayi, ta watso su ne bata tauna ba. Inda inda ta soma yi tana rangaji, "Mallam ina nufin itama tana makarantar mu ne kuma zai fi min saukin zuwa,"

DIYAR DR ABDALLAH Donde viven las historias. Descúbrelo ahora