Nine - Mabuɗin Zuciya

Start from the beginning
                                    

"Wani makaranta? Zaki faɗa masu ko ni zan gaya masu?" Fa'iza tace yayinda hawaye ya soma cikowa idanta. Cikin rawar jiki Kankana ta soma magana. Duk ta firgita, amma bazata saduda ba. Dole taci wannan yakin. Kota halin ƙaƙa ne saita bar wannan gidan.

Rawar baki Rumasa'u takeyi, kwalkwalwarta ya birkice ta rasa me zata ce domin ta fidda kanta. Tsaye ta miƙe tana kallon kowa, Mallam ya kalle Fa'iza, "Menene ?" yace damuwa cikin idansa.

Anan Fa'iza ta labarta mashi cewa karya Rumasa'u takeyi bata samu addmision ba. Kawai damfarar su takeyi, Inna ta fara kuka. Ita kaɗai tasan yawan bashi da Mallam ya ciyo domin ya bada kuɗin registration. Har yanzu yana biyan wasu.

"Da gaske ne?" Mallam yace da kyar. Ko kallon Rumasa'u ya kasa saboda takaici. Babu haufi ita ce zata zama ajalin sa.

Tana rawar baki saita soma magana, "Wallahi karya Fa'iza takeyi. Baƙin ciki take dani saboda na fita farin jini," dafa kai Inna tayi shima Mallam abinda yayi kenan. Aliyu ne ya miƙe ya yanke Rumasa'u da mari.

"Dan rashin mutunci kashe su kike so kiyi? Wannan wani irin rashin imani ne? Kinsan cewa bamuda wani gata sai su amma kullum kina hanyar nakasa su"

Cikin kuka Rumasa'u ta soma magana, "Wallahi karya ne, Fa'iza yar bakin ciki ne.... Bari na kawo maku addmision letter ɗina......" sai a lokacin ta tuna cewa ta taune randa yan sanda suka tafi da ita na farko.

Anan ta ƙara gigicewa, Inna banda kuka babu abinda takeyi. Dama ance ɗan kuka shi ke jawo ma uwarsa jefi. Yanzu ta tabbata cewa Rumasa'u bazata taɓa hutu ba saita ga sun ɗaiɗaice.

"Toh naji karya nayi, amma ku fahimci ni saboda bada gangan nayi ba. Wallahi aikin shedan ne." saita fashe da kuka tana shesheƙa. Aliyu yaso yaje ya taka mata wuya idan ta mutu kowa zai huta. Ya nufeta kenan sai Mallam ya dakatar dashi.

" Karka taɓata, bazai canza komai ba." sai ya juya ya kalleta sosai." Toh uwar mu, gashi mun baki duka hankalin mu, me kike so muyi maki? Tunda yanzu mun gane cewa bakya makaranta da wani karyan zaki tafi chan gidan?"

Kallon Mallam tayi tsab, tana tunanin ko gatse yake mata. Amma ita koma me yakeyi bai dameta ba, gidan ne saita bari. Gyara tsayuwa tayi saita soma magana," Dama nayi ma kaina register computer school a Independence way. Nayi ma kaina faɗa kawai naji nauyin faɗa maku ne," tace.

Mallam ya kalle Inna, "Nafisa yar ki tace zata tafi,"

Inna bata bar kukan ba, shi kuma Mallam jira yakeyi yaji ta bakinta, Aliyu ne ya tashi ya durkusa gaban Mallam. "Dan Allah ka barta ta tafi, koba gidan Rahina ba ko duniya ce ta shiga. Dan Allah Mallam kada ka bari bakin cikinta ya illanta ka. Kayi hakuri haka naka kaddarar yake..."

Mallam ne ya kauda kansa gefe, hawaye ya soma kwarara masa. Baisan da wani yare zai gayama Rumasa'u cewa bariki alalen gero bane. Idan baka iyaba zai kwaɓe maka. Amma kuma Rumasa'u tayi nisa bazata ji kira ba. Baisan wanne yafi ba, ta saka kai tayi tafiyar ta koko tazo neman izinin sa.

Da hannunsa yayi maza ya share hawayen, daɗin abin babu wuta sai fitilar 'makarfi ya gaza' wanda ke aiki. Shiru yayi har saida muryan sa ya daidaita kafin ya soma magana, "kika ce gidan Rahina zaki?"

Da sauri ta amsa tana murmushi, "Eh wallahi nan zan tafi,"

"Inace itace yarinyar Chairman wanda suka tashi?"

"Yauwa ka ganeta Mallam, ai zan rinka zuwa ina duba ku. Kuma zan rinka taho maku da abin alheri," ta faɗa da fara'a kamar tayi abin arziki.

"Allah ya kiyaye hanya," ya faɗa saiya fita da sauri. Buta ya ɗauka ya nufa bayi. Inna runtse idonta tayi domin tasan cewa kuka zai je yaci. Rumasa'u tana cin masa tuwo a ƙwarya fiye da yadda kowa ke zato amma kawai dannewa yakeyi.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now