Eight - Mahfooz III

Start from the beginning
                                    

A ranar Mahfooz ya bar kano bai sake waiwayan garin ba saidai idan sunje kwallo da yan team ɗinsu. Shima yana ɗaki ko filin ball. Sam baya yawo saboda kada yayi gamo da Fauziyya.

Ita kam jira takeyi a gama zaman makoki domin taci uban Mahfooz. Batayi wani ma Zanira addu'a ba. Tana chan tana kullace kullace irin rashin mutunci da zatayi ma Mahfooz idan sun hadu. Tabbas saita nuna mashi cewa gwara zaman sa a kabari. Ya kashe mata yarinya kuma bazata yafe ba.

Duk da bawai tana wani san Zanira bane, ita a ganinta kamar ba yarta bace. Yadda take shishige ba Mahfooz da sauran jama'a kamar wanda bakin uwa ke binta. Sam batada aji ko kaɗan. Kusan duka ƙawayenta babu yaran babban gida.

Yasa Koda suka zo ta'aziyya bata basu ruwa ba. Tabarma ta bada aka kai chan bakin Gate aka ajiye su. Amina ce tayita hidima dasu, ta tabbata abinci bai tsinke masu ba.

Da Fauziyya taji Mahfooz ya gudu ta ɗan ji dama dama. Amma ta ɗauki alwashin duk randa sukayi ido hudu dole gawa ta faɗi. Ko nata ko nashi. Saboda kada Allah ya raga ma wanda ya raga ma wani tsakanin ita dashi.

Kaduna garin gwamna yaje, bai taɓa zuwa ba. Anan ya samu yaje wani hôtel da yan kuɗaɗen sa. Abinka da baƙo kuɗin ya zabtare. Daga nan Mahfooz ya nema makarantar gwamnati domin ya saka kanshi. Ya ɗauki ma Zanira alƙawari bazai tagayyara ba, zai zama wani abun. Zai nema ilimi duk wahalar sa.

Sau da dama tun yana turjewa akan baiso yasan abinda aka koya masu saboda Fauziyya ranar bata bari yaje makaranta ba. Zanira zata ce kada ya bari wanda suke so su cutar dashi su samu galaba akan sa. Idan sun nuna bai isa ya samu ilimi ba, yayi kokari ya samu. Cinsa nasara a rayuwa shine babban ramuwa gare su.

Zuwa yayi Sardauna Memorial College ya saka kansa. Yaje masu da birth certificate ɗinsa da primary school leaving certificate. Anan akayi mashi ƙaramin test aka gane yanada kokari. Tunda dama a private yake a Kano.

Yanzu anso yayi jarabawa amma yace bazai iya ba, idan second term yayi sai dawo. Duk tunanin Zanira ya cika mashi rai. Kawai yana daurewa ne. Ranar yana zaune a filin makaranta har yamma saiga masu buga ball sun zo.

Daga nan abin ya soma bashi sha'awa. Yana kallon su har yaje yayi sallah la'asar. Bai ce masu komai ba. Tunanin Zanira yakeyi, banda cewa da tayi tana sanshi babu abinda yake tunani. Haushin kansa yakeyi da bai cema Zanira yana santa ba. Abin yafi masa ƙuna akan abinda Fauziyya tayi masa.

Haka yayita zama a hotel, da kudinsa ya kusan ƙarewa saiya kwashe kayansa. Dama kullum yana zuwa SMC idan yamma yayi yana kallon su. Daga nan suka saba data wasu, har suka rinka gayyatar sa training. Dama yana kallo, bugawa ne baya yi.

A hankali ya fara training yana exercise, tun baya ganewa duk jikinsa yayi masa ciwo har yazo ya fara jin daɗin. Kayansa daya kwasa daga hotel sai ya bama wani abokin sa wanda suka haɗu a filin kwallo. Shi kuma idan dare yayi sai yaje ajujuwan ya shiga ta window yayi barci. Da safe saiya ɓace kafin kowa ya gansa.

Da aka koma makaranta haka ya cigaba, yaje gidan abokinsa Faisal amma ana ce masa Faash. Shi ba SMC yake ba, kawai dai yanasan kwallo ne. Iyayen sa nada hannu da shuni. Shi kuma Mahfooz bayaso ya takura ma sa.

Bama kullum yake zuwa gidan ba, a school bag ɗinsa akwai komai nashi. School uniform, kayan kwallo da bargon sa. Idan zashi wanki ne yake zuwa. Daga baya ma wani masallaci yake zuwa yana share masu masallaci yana zuba ruwa a buta. Daga nan sai ya wanke kayansa tas babu wanda ke hanashi.

Kullum idan ya tashi daga aji da safe zai wuce yana ganin wani mutum mai Bus zai fita, anan Mahfooz ya yanke shawarar cewa zaima mutumin magana idan yana neman conductor kokuma abokan aikin sa suna nema su bashi.

Mutumin yace yayi hak'uri wani yaron ƙaninsa ke masa amma idan yaga mai nema zai samu mashi. A lokacin kuɗin Mahfooz ya ƙare tas. Gashi an koma makaranta, Faash ba kullum yake zuwa ball ba. Shi yana makaranta kuɗi ne a GRA.

Haka Mahfooz yake zuwa wajen masu abinci, yayi masu shara da wanke wanke sai su bashi saura. Har matan mai abincin ta gane Mahfooz wanke wanken sa yafi fita. Yana zuwa zata fara murmushi, tun tana bashi saura zata ajiye mashi mai kyau a roba. Sannan kuma ta haɗashi da naira hamsin.

Gode mata yakeyi sosai saboda tana rufa mashi asiri sosai. A haka ya cigaba da zuwa makaranta yana kwana a aji, idan an tashi yaje yayi wanke wanke sannan da yamma yaje kwallo.

Kafin kace kwabo har shekara ya zagaya yakai SS2. Yan unguwan sun sanshi kowa yana alfahari dashi, bayada kiwiya. Gashi kuma ya soma zama babba a kwallo. Idan akwai match yan unguwa suna zuwa suna kallonsa.

Shi da kansa yace su rinka ƙiransa Qwaro, saboda wahalar dayake sha. Idan yana filin kwallo ya iya zara kuma da passing. Sai kaji kowa yana ga Qwaro. Anan ne ya shiga wani football academy suna training a ex minister's quarters dake Rabah Road.

Yanzu ya daina wanke wanke, yana cikin wanda suke bada abinci watau waiters. Hajiyar ta yanke mashi albashi duk wata dubu ɗaya da dari biyar. Sai kuma Faash ya nace akan dole saiya dawo wajen sa da zama kwanan aji bai kamata ba.

Bai taba tambayar Mahfooz labarin sa shima bai bada ba, yasan cewa randa ya shirya zaiji komai. Abu ɗaya ya sani game dashi cewa daga Kano yake. Shima idan ana magana da maza ne saiya ce "a Kano ai...."

Kuma sanda Mahfooz yazo kayan alfarma yake dashi, ta wannan fanni Faash ya gane Mahfooz ɗan wani. Dama baban Faash yanada gidaje, yaransa maza suna zaune a tsohon gidansa dake kawo. Anan su Faash suka fara zama kafin sukayi gini Unguwar Dosa suka koma.

Faash shima yana zuwa gidan amma ba sosai ba, yayyen sa nada mota kuma suna zuwa aiki. Idan yaje gidan toh saidai a motan haya zashi boko kuma yana latti. Direban babansa yana babban gidan.

Kwashe kayan Mahfooz yayi suka wuce kawo, anan ya soma zama har yanzu. Yayyan Faash basu damu da zaman Mahfooz ba, musamman saboda yadda yake kokarin gidan yayi tsab kamar bana maza ba.

Da chan idan sunci abinci nan suke bari, musamman takeaway idan suka zo dashi ko roban lemu. Zaka iya tsintar ledan da yayi wata daya ba'a kawar dashi ba. Amma yanzu kam kullum ƙal ƙal zaka ga wajen. Abin yana matukar birge su.

Sannu a hankali sukayi introducing Mahfooz wajen baban Faash, suka ce mashi iyayen sa sun rasu kuma team mate ɗin Faash ne. Daga nan aka daina wariya tsakanin Mahfooz da Faash. Har Shira yake binsu a garin Bauchi idan sallah yayi. Sannan kuma Alhaji sai yace ma yan Shira wannan yaron abokinsa ne, a Kaduna kuma yana cewa wannan yaron ƙaninsa ne daga kauye.

Koda suka gama zana jarrabawa na SSCE, Faash ya samu Engineering kamar yadda ya bukata. Shikam Qwaro bai samu ba. Baban Faash da kansa yaje Kaduna Polytechnic, abokinsa yayan rector ne. Nan shima aka samu mashi Civil Engeering ya bazama karatu.

Yanzu haka duk sun gama suna aiki a Julius Berger.

Tunda Zanira ta rasu bai sake tunanin cewa zaiyi wata budurwa ba wai yana santa da gaske. Saidai ayita ɓata ma juna lokaci. Shi acewar sa idan yayi haka cin amana ne wajen Zanira. Tunda tace tana sanshi bai amsata ba. Yana ganin babu macen data cancanci wannan kalmar sai ita.

Ranshi yana mashi ƙuna sosai idan ya tuna yadda mutuwa tayita tafiya da masoyan sa. Bai taɓa tunanin zai iya cewa wata yana santa da gaske ba sai Rumasa'u. Akwai wani yanayi datake yin masa wanda ya kasa fahimta. Shi dai yanzu yana ganin finally he's ready. Yana ganin Rumasa'u a rayuwarsa zatayi daidai. Rumasa'u zata maye mashi gurbin Zanira. Rumasa'u zata zame mashi haske a cikin duhu.

Wannan kenan!

#Naseera
#RumaSau
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah


Ainakatiti 🌠

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now