Abin hawanta Napep ta hau zuwa layinsu Rahina, cikin ikon Allah mai gadi yace yau ta taka sa'a sun dawo. Da sauri ta shiga ciki murna fal ranta. Kai tsaye ɗakin Rahina taje, anan ta risketa tana waya. Bata ko damuba ta ruga ta rungumeta ta baya.

"Kawata naji daɗin ganin ki. Abubuwa da dama sun faru bakya nan. Me kika taho min dashi?" duk ta faɗa. Rahina ta rasa da wanne zata fara amsawa. Kawai girgiza kai tayi saita kashe wayan datake yi ta kalle ta.

"Ya su Inna, lafiyan su ƙalau koh?"

"Lafiya lau... Ke nace me kika kawo min," saita wuce wajen mirror ɗinta ta soma dube dube, bataga sabon abu wajen ba, sake waigowa tayi, "Yanzu kije Dubai ki dawo ƙandas hannu yana dukkan cinya. Allah ya tsine ma fatara," tace tareda rankafa tsaki.

Kwanciya tayi a gadon Rahina tana ajiyar zuciya, tana kokarin tunanin yadda zata gaya mata abinda ya kawo ta.

Anan ta zauna ta kafa ma Rahina Ido, "Menene?" Rahina tace mata. Fashewa da kuka Kankana tayi. Saita Labarta mata labarin ƙarya. Inda Mallam ya ciyo bashi yan bashi suka zo suka tozarta su. Yanzu haka an kwace gidan su haya suke yi ciki da falo. Aliyu ma kwanan shago yakeyi, su kuma suna kwanan falo.

Rahina ta tausaya ma Kankana. Tasan batada hankali amma tasan bazata masu Inna karya haka ba. Sai Rumasa'u ta gyara zama, magana ta soma cikin natsuwa.

"Dama wai nace bari na dawo nan da zama kwana biyu, sai na rinka zuwa gida jefi jefi. Wallahi ko karyawa banyi yau ba, abinci gagaran mu yakeyi." Saita sake fashewa da kuka. Anan Rahina taje wajenta ta zauna sannan ta rungume ta. Haƙuri ta soma bata tareda cewa zata tambayi izinin iyayen ta.

Murna fal ran Kankana saboda zata soma yin rayuwar daya kamace ta. Rayuwar data daɗe tana mafarkin sa. Dama mahakurci mawadaci. Duk hakurin da tayi a talauci yanzu Allah zai musanya mata da arziki.

Ta soma tunanin yadda zata ƙaro wulakanci a Instagram, hotuna kala kala harta a bayi wajen jacuzzi. Yanzu babu babban yarinya irin ta. Itace asalin ajebo. Ganin hannu Lala tayi da wani waya ba IPhone ba.

"Ke kam mugun abu yabi dare, me kike yi da android?" tace tareda zare ido kamar taga dodo. Murmushi Lala tayi saboda Kankana bata san dawan garin ba. Akwai android dayawa da suka fi IPhone daraja.

"Wannan wayan Huawei p30 ne, kuma yafi tsadan IPhone 11 da Samsung s10. Rashin sani ke damun ki... Yafi min IPhone sau dubu"

"Amma da ai IPhone ɗin kike rikewa," ta faɗa tareda watsa mata harara.

"Eh har yanzu ina da shi, ɗayan layina anan ya yake. Screen ɗin ya fashe yasa bana amfani dashi. Akwai layi babba ya fito akai."

Girgiza kai Rumasa'u tayi, tasan ta samu waya a sama. Sannu a hankali zata roƙe Rahina ta bata. Komai yana tafiyar mata yadda ya dace. Zata zama asalin ajebo mai kwana a GRA. Ta tabbata ba zata sake mafarki ba sumul zata rinka barci.

Balle yanzu a wannan makeken gadon zata rinƙa kwana. Sau da dama tana jin Rahina na ƙorafi akan laushi gadon, idan ta kwana kai tana makara asuba kuma bata iya tashi sallah dare. Ta fi son ta kwana akan rug da pillow tunda shima yanada taushi. Tausaya ma Rahina takeyi yadda taƙi gogewa, babu haufi ta gaji tsiya. Yanzu gadon zai zama nata duka tayi ɗaiɗai da kafa.

Da kyar Naseera ta tattara jikinta domin ta tafi gida, test result ɗinta yana hannunta tana kallonsa. Duƙunƙunawa tayi ta watsar cikin bola. Hawaye bai dena zuba ba. Duk gabanta faɗi yakeyi ta kasa haɗa ido da mutane. Tsoro takeyi kada su gane ciwon dake tareda ita.

Daɗin abin Dr Chinedu ya soma preparing ɗinta, har ARV ya amsa mata daga HIV centre wanda zata fara sha. Sannan yace kada ta damu ba ita zata rinƙa zuwa karɓa ba. Tayi a hankali har Dr Abdallah ya warke kafin a gaya mashi. Bayaso ya tada mashi hankali ko kaɗan. Da wanne zaiji, raping ɗinta kokuma HIV.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now