"Dr ina abin murna a HIV?" ta faɗa a hasalce. "Na shiga uku ni Naseera, banida sauran amfani a wannan azzalumin duniyar. Mena masu da zasu haɗani da wannan mugun ciwo? Mena mashi da yana kallo yaƙi hanasu? Kowa azzalumi ne babu Allah a tareda shi... I am too nice to be treated this way."

Su Hajia Binti sun shirya tsab suna jiran Naseera tazo su tafi, da taga bata zoba saita tambaya wata Nurse inda ta shiga. Anan tace taga sun nufa hanyar da ofis ɗinda Dr Chinedu yake. Umma bata kawo komai ranta ba tana tunanin cewa ƙila aiki ne ya kamasu. Anan suka wuce gida da Dr Abdallah inda ya jima bai jeba. Yayi mugun ramewa saboda ciwo harta kayansa duk sun soma masa yawa. Amma Umma bata damu ba, tasan kwanan nan zai murmure.

Rumasa'u Annoba, kokuma Rumasa'u Kankana bata jin daɗin yadda suke zama. Da chan ta saba daga ita sai Fa'iza. Amma yanzu kam kwanan falo sukeyi da Fa'iza. Sai su Inna da Mallam na uwar daka. Abin ba ƙaramin takura mata yake ba.

Sannan da asuban farko idan Mallam zai fita kiran sallah a masallaci yake ta dasu. Dama ita asuba sai rana ya danno kai takeyi, yanzu zance ya canza. Kafin kaga Rumasa'u tayi asuba cikin lokaci to tabbas saidai da Ramadan.

Inna yanzu tana binta koda yaushe, itace take saka mata ruwa a buta, idan ta idar da alwala sai Ruma tayi da sauran. Batada waya yanzu gantali baya mata daɗin fita.

Har yanzu tana karyan fita makaranta, sai tayi kwalliya tayi chatan Napep taje layin masu kuɗi, anan take sauka bakin titi saita soma strolling. Tana kyautata zaton yaron mai kuɗi zai fito ya ganta. Kokuma shi kansa Alhajin zai ganta yazo ya aure ta.

Idan ba jari ta samu ba na sama da dubu ɗari biyar bata tunanin zata iya wani sana'a. Gashi ta kasan cin jamb balle taje makaranta har ta gama ta samu aiki. Koda yake tana ganin koda taci jamb bazata gama makaranta ba. Kanta baya daukar komai, balle kuma ita kanta ta tsani karatu.

Yanzu abinda kawai ya rage mata ta aure mai bala'in kuɗi, ubanta talaka ne balle ta gada. Sau biyu tana zuwa gidansu Rahina Bulala amma basu dawo ba. Yau dai ta ɗauki alwashin zata sake komawa.

Atampha tasa wanda akayi ɗinkin boubou, kamar yadda ta saba fuskanta shaƙe yake da make-up kamar zata biki. Inna tana falon tareda ita tana kallonta. Mamaki takeyi yadda take sarrafa kayan kwalliyar, gashi ta ɗaura eyelashes kamar gwana.

"Wannan abin baya takura maki?" Inna tace mata.

Murmushi Rumasa'u tayi, "A'a Inna shine kyan ai,"

"Kema ai kyakkyawa ce ba sai kinsa ba. Ni Nafisa ai na iya haihuwa," Inna tace tana raha. Itama Kankana dariya tayi. Ba kasafai Inna take yawan barkwanci ba. Kullum baka rasata da tagumi tana tunane tunane.

Tunda Inna taga Naseera ta soma tunani, tana mata yanayin sanayya tsakanin su. Kuma kana ganinta kasan kusan shekarar ta ɗaya da Rumasa'u.

Tabbas Rumasa'u nada wasu mugayen halayya daya fita daban da sauran yaran gidan. Batada wadatan zuci yafi hasken rana bayyana. Saidai kuma akwai kama tsakanin su. Daga Fa'iza da Aliyu sunada kaman halitta na Inna da Mallam, ita kuma Rumasa'u kamar Inna ne gareta. Sannan kuma tanada haske.

Wannan kaɗai yana kawar ma Inna da duk wani tunanin data keyi akan Rumasa'u ba yarta bace. Tabbas Ruma yarta ce, amma wacece wancan da suka gani a police station? Tun kwanakin nan tafi jin wancan wanda bata san sunanta a ranta fiye da Rumasa'u.

Uwardaka Rumasa'u taje domin ta ajiye jakar kwalliyar ta. Anan taga Fa'iza tana sallah na Walha. Cikin izgili tayi mata magana.

"A'a harda su sujjada, halan kin kashe wani kike neman yafiya," saita bushe da dariya ta fice.

"Dan Allah kada ki janyo mana abin magana. Ki kama talaucin ki," Inna ta sake jaddada mata sanda takai kofa. A kumbure ta amsa da, "toh Inna," saita fice.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now