A dikilce Naseera ta murmusa saita dauki jakarta tareda wani envelope ta fita bata sake cewa komai ba. Tana rufe kofar a bayan ta saida ta tsaya ta gyara kallabin ta saboda duk ya sukurkuce. Ajiyar zuciya ta sake yi saita tafi office dinta, Resident Doctor ce amma kasancewa asibitin Babanta ne Dr Abdallah dole saida aka bata nata office din.

Zama tayi akan kujerar ta, saita ɗauko takardar tana sake kallo. Ta kasa gasgata abinda yake bayyanawa. Ba karo na farko ba kenan tana sake tura sample lab, zai Kai kusan sau 6 amma duka haka results ɗin ne.

Tafasa kwakwalwarta ya cigaba da yi, anan ta soma ganin dishi dishi, duk ilahirin jikinta yayi mugun sanyi. Bakin ta ɗaci yakeyi kamar taci danyen shuwaka.

Buga kofa aka yi tareda shiga, "Dr, ana neman ki a male ward yanzu," wata Nurse ta faɗa a ladabce. Da kai Naseera ta amsa, saita kalle Beeper dinta, anan ta lura an daɗe ana mata magana batama lura ba. Envelope din hannun ta takai cikin safe ɗin office ɗinta ta kulle. Saita saka lab coat ɗinta tareda fita.

Hajia Binti ta lura da mugayen kallon da Naseera ke binta dashi kwana biyu. Amma duk abin ka bazaka ji cikin Naseera ba, kamar kwalta take saidai ka wuce amma ba'a bambaranta. Zurfin cikin ta ya bala'in ɓaci. A duniya kuma Hajia Binti ba abinda take so kamar Naseera. Kasancewar sun shekaru bila adadin bayan aure kafin suka sameta.

Gatan duniya sun nuna mata, yasa yadda ta canza mata kwana biyun nan ya bala'in ɗaga mata hankali.

Saidai abinda ta sani shine duk abinda ruwan zafi ya dafa, idan aka yi haƙuri ruwan sanyi zai dafa shi.

****

"Ƙas Ƙas Ƙas" ɗin taunar cingam ke tashi tareda waƙar Hamisu Breaker tana bi, baiti baiti babu wanda bata sani ba kamar ita ta rubuta waƙar. Tanayi tana fesa kwalliya. Idan wani ya gani zaiyi tunanin biki zata. Amma kwalliya kawai takeyi na nishaɗi saboda zata gidan kawarta anjima domin ta samu tayi hoto wanda zata watsa Instagram. Yau Laraba kuma rana ne na hashtag din WCW watau Woman Crush Wednesday.

Madubala wanda aka fi sani da saurauniyar kyau ta cige ta satin daya gabata, hotuna tayi masu kyau, gashi samari sunata yabon ta. Tabbas tasan wasu sun bita private domin su bata kuɗi. Kuma abin ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba. Dama itace abokiyar hamaiyarta a duniya. Basu taɓa haɗuwa ba, kuma ba garin su ɗaya ba, asali ma basa following juna amma suna kishin juna sosai.

Kofa aka tura yayin da aka shiga, a wulakance ta kalle wanda ta shigo, ba kowa bane illa ƙanwarta Fa'iza.

"Ruma jiya naje ajin ku amma ance babu wata mai irin sunan, babu irin kwatancen da banyi ba harta hoton ki babu wanda ya gane ki. Kaɗan kuma sun gane fuskan daga Instagram ne," ta faɗa fuskanta babu yabo babu fallasa.

Ninke kayan saman gadon ta soma yi ba tareda ta kalle Ruma Sa'u ba. Ita kam gabanta ne ya soma faɗi amma ta ƙware a bariki.

"Meaning?" Ruma tace a dikilce tareda watsa mata harara da dara daran idanta.

"Eh yana nufin ko karya kike baki samu admission ba, ko an kore ki, ko kuma ba'a department din kike ba."

"Toh FBI, da wannan lokacin da kika ɓata wajen bin diddigi da kin bincika meyasa kike da masifan muni daya fi miki... Matsalata da talaka bakin ciki da hassada. Ina ruwan ki da rayuwa ta??? " sannan saita ja dogon tsaki.

Murmushi Fa'iza tayi, idan da sabo tsab ta saba. Da kuma zagi yana aibu daya yi mata wani abu. Amma bazai yiwu yanda iyayen su ke kokarin ganin sun basu rayuwa mai inganci ba a rinka zalinta su.

"Kuma idan kin ga dama ki haɗa min annamimanci wajen su Inna, wallahi saina maƙure maki wuya, ki koma kina zare ido kamar akuyar data lashe gishiri." Ruma ta sake cewa.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now