*******kaman daga sama yaji ance handle what? she's responsible for that, ko haufi banayi, sannan kana maganar mata biyu, waya aura maka su duka? mikewa sukayi tsaye dukansu sanadiyar hajia asiya da ta shigo ranta abace, khalid daya take mata baya yayi tsaye yana kara yiwa yayansa kallo kana ya rungume hannayensa biyu, de Mahmoud kuwa cike da mamaki ya sunkuya ya gaisheta, ta amsa masa kana tace meyasa bazaka fito ka sanar dashi gaskiya ba? he's your friend tell him wannan ba rayuwa bace, matar shi tana cen hospital kwance unconscious amma tunda yakaita rabon da yaje ya dubata ko kira babu ayyi koda dabbace she deserve some care, dr Mahmoud yace hakane hajia, amma kiyi hakuri, Allah ya huci zuciyarki, nima yanzu nake mamakin mata biyu dinda yace, tace kaide ganeman hanyar, ni bansan yana da wani aure bayan wanda muka masa ba, ban kuma san da cewa yanada wasu iyayen da zasu nema masa aure bayan mu ba, tunda ta fara magana khalifa yake tsaye kansa sunkuye akasa, dr ya bata hakuri kana ya fice abunsa, zama tayi tace naga alamun iskancin ka da yawa yake, idan akayi dama sai kayi hagu, toh ayita a kare kawai khalifa, ka sawwakawa aisha sai na aura mata khalid inaga kaman shi zai iya rike amanar da ka kasa rikewa, jin statement dinta yasa shi dago kansa cikin hanzari ba shiri, cikin rawar murya yace saki fah kenan mummy? ta buga desk din tace sosai kuwa saki nake magana saboda zamanku bashida wani amfani, ita ka bata drugs na hana daukan ciki, ita kuma prostitute dinka ka zuba mata kwayakwan haihuwar toh ba'a gidana ba, ba'a zuri'a ta ba wallahi, dan haka kai nake jira ka bani ta karasa fadin hakan tare da mika masa hannu
********hakan ya tabbatarwa khalifa da cewa mummu dagaske take, mikewa yayi daga kan kujeransa ya dawo gabanta ya rage tsawon shi, cikin murya mai kaman zaiyi kuka yace dan Allah mummy kada kiman haka, dan Allah kiman rai, karki rabani da aisha, daidai wannan lokacin akayi knocking din kofar office din, khalid dake tsaye ya bude tare da fitowa yana fitowa yaga su samira da hanan, bayan sun gaisa, khalid yace mrs hanan, ya aiki? kin dawo kenan? tayi murmushi tace eh wallahi, dama inasan magana da boss dinka ne ko nace yayanka, khalid yace uhmmm all dsme, so sorrry bazaku samu damar ganin shi ba saboda mummy is here, samira tace yaushe zata fita? hanan tayi saurin riko hannunta kana tace toh yayi ba matsala, zamu iya jira a waiting room? khalid yayi yace okay toh yayi, nan ya hadasu da security aka kaisu waiting room, khalid kuwa kallo ya bisu dashi kana yace ita wannan mai nuna na isa ko wacece oho nan shima ya juya ya koma ciki
*******khalifa kuwa ganin mummy tayi masa ko oho, yasa shi kwantar da kanshi akan cinyoyinta, yace dan Allah mummy kiyi hakuri, wallahi nasan ni mai laifi ne agareku amma kada ku yankeman wannan danyan hukunci please, mummy ta tabe baki tace kasan danyan hukunci ne zaka ishi mutane da wai mata biyu ce dakai, sannan ita waccen dake fighting life dinta ita kuma angayamaka batada kowa ne, haba khalifa ummah hanne tanada kawaici wallahi, bata dauki komai komai ba, haba ayyi ko dan darajar hakan yasa ka nuna ka damu da yar'su amma ka nuna ko oho, yanzu kenan inda muna zurmi sai ya kenan? Shuru yayi yana hawayensa, Khalid yace gaskiyar ki mummy, Allah yaya banyi expecting hakan daga gareka ba, cikin takaici yacewa khalid shut up, mummy tace kai zan cewa shut up, let him say his mind, kowa yasan ka aikata ba dede ba, mikewa tayi tsaye tace let me warn you, ina nufin last warning kada ka kuskura zaynab ta kara 24hours acikin gidan nan, ni zanzo da kaina nayi confirming hakan, idan kuma naganta aciki then ka tanadi reasons din hakan, ni bazan daukarwa kowa hakan ba saboda babu wanda yake yiwa yarana, noor is happily married lafiya lau, sai kai nan wallahi baka isa ba, tasa kai ta fice khalid ya taka mata baya, nan khalifa yakai zaune ba shiri, tare da dafe kansa yana fadin innalillahi wa'inna illaihir raju'un
**********ummah hanne ce zaune, sanadiyar tun jiya da suka baro hospital busu koma ba, yau kam daren ga baki daya sallah da addu'a ta kwana yi, bacci ne bata kwanta ba sai misalin karfe 3 na dare, nan ya kwashe ta akan sallaya, ana kiran sallah na farko ta farka, tayi arwala, tayi nafila, kana ta gabatar da sallah subahin, nan ta roki Allah da ya bawa aisha lafiya, takai kukanta sosai gun Allah, da safe kuwa nan ta shiga hadawa aisha breakfast nan ta kammala komai ta hada komai cikin basket, dakin mai sunan mama ta dosa nan tayi knocking tare da murda handle din dakin kwance ta hangota tana bacci, cikin kulawa ta tasheta, tace kinyi sallah? Cikin muryar bacci tace eh ummah, tace bazakije ganin aisha bane yau? tace uhmmm zanje ummah, bara nayi wanka, nan ta mike ta shiga bandaki, ummah kuma ta koma nata dakin
*****ki saka himma mana raliya, malam muhammadu yana waje yana jiran mu fah, nan ta fito tana kokarin gyara zaman hijab dinta, nan sukayi sallama da mahaifiyarta suka fice, a waje suka samu malam muhammadu zaune yayi wanka cikin shaddarsa yau sky blue yayi kyau abunsa, nan suka samu adaidaita suka shiga, malam muhammadu yace tunda nazo gabana yake faduwa usumanu, malam usman yayi murmushi yace kada ka sawa kanka damuwa,kafi kowa sanin halin hanne batada matsala
********FLASH BACK*****khalifa kuwa ranar bai samu ganin kowa ba a office dinsa, dan babu wanda yasan fitarsa, dawowarsa gida ya samu zaynab zaune a fallo tana kallo cikin wata yar short gown handless red tayi kyau abunta, kallo ta bisa da shi ko kyabtawa babu, ganin bai bi ta kanta ba yasa tace lafiya kuwa baby? juyowa yayi yace kinga dan Allah banasan takura bai jira wata ba ya shige dakinsa ya saka key, zaynab kuwa baki ta tabe tace uhmmm mugun halin ya motsa kenan
*********FLASH BACK******samira tace nifah hanan nagaji Allah, i can't just keep waiting for him, hanan dake charting tace kinga dan Allah relax mana, tashin hankali is not ours, ayyi kinga mum dinshi ce aciki, samira tace ayyi zaifi dadin shiga, nan ta nufi kofar ta fice, hanan kuwa mikewa tayi ta shiga kiran sam, sam, sam, samira, koda ta ankaro samira har takai kofar office din khalifa, koda ta shiga taga office din wayam bakowa aciki, nan taja wani dogon tsaki daidai lokacin hanan ta karaso samira tace kingani koh, ayyi baiyi gadon mutunci ba har ya ficewansa fah, ni kiyiwa Allah ki nema mana address din gidan shi, hanan tace taya zaayi nasani ba kin taba zuwa gidan ba? samira tace hakane fah, i think haka za'ayi kuwa, muje gidansa kawai ayita ta kare gaskiya, hanan tace fine nd good then, haka suka fito samira sai faman hushi take
*********haka zaynab ta tashi da safe, tayi wanka, ta hada tea nata kadai ta sha, ta zauna fallo tare da zuba wani uban tagumi, khalifa ne ya fito cikin jallabiyarsa yace kije ki hada kayanki ki zo muje, zaynab da taji maganar kaman daga sama, ta juyo tace muje ina? khalifa ya wulga mata wata uwar harara kana yace lahira, zaynab tace ayyi ba bakuwa bace kowa sai yaje cen idan takamar ka bakar magana, cike da jin haushinta yace ke kam wallahi bakida albarkar aure, sai kace mai farar kafa tunda kika shigo rayuwata bantaba kwana cikin jindadi da kwanciyar hankali ba, yau tashin hankalin yau daban na gobe daban, tunda na auri aisha nake cikin kwanciyar hankali kina zuwa komai ya sauya shine saboda tsabagen kishi na jahilci zaki zuba mata poison a abinci koh zaynab? Jin hakan yasa gabanta yayi wani faduwa, baki ta turo tace yau kuma ni zaa dorawa kazafin kisa, meya hana ni na mutu tunda kowa abincin gidan yaci ranar, khalifa yace kedai akeji, ki tashi kar na bata maki rai kinji koh? zayanb ta mike tsaye tana fadin koda yaushe mutun cikin tashin hankali yake, knocking dinda ake ne da karfin gaske yasa khalifa cewa innalillahi wa'inna illaihir raju'un kingani koh? tun dazu nace ki hada kayanki amma rashin mutuncin ki ya hana, toh wallahi duk abunda ya biyo baya don't blame me Allah
*********cikin rashin fahimtar me yake nufi tace kamanya i shouldn't blame you, meyake shirin faruwa ne? ko ta kanta khalifa baiyi ba ya nufi kofar yana mai karanto duk wasu adduo'i daya sani na neman natsuwa,wani gumi ne yake karyo masa ta ko ina, haka yake tafiya yana mayarda numfashinsa tamkar wanda yayi wani jan aiki
**********zaynab kuwa kasa ce masa komai tayi, hasalima tsoro ne ya kamata, a zuciyarta kuwa cewa tayi innalillahi wa'inna illaihir raju'un Allah yasa ba sa zaiyi a kamani ba, na shiga uku, itama tuni idanuwanta suka rine sukayi jawur, hawaye ne zafafa suka cika idanuwanta, hannayenta ta dora akai tana kallan yanda khalifa ke tafiya tamkar wanda kwai ya fashewa aciki, sai rawar dari take tana up nd down, kasa hakurin ya bude kofar tayi ta dauki wayanta ta nufi dakinta da gudu kuwa tamkar wacce ba komai ajikinta
*******khalifa kuwa yana bude kofar ya wani zaro na mazurunsa, duk inda tashin hankali da rashin natsuwa yake saida ya bayyana akan fuskarsa, murya na rawa yace.............
Toh fah
Wa khalifa ya gani?
more likes
More comment
More vote
More post💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
YOU ARE READING
AURE NAKESO 💔💔💔💔💔
Short StoryMatasa ne mata uku, masu kudi, masu kyau, komai sukeso na duniya Allah ya basu but they are looking for true love, let's see how it gonna roles💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞shin zasu samu koya?
AURE NAKESO 💞💞💞💞💞💞
Start from the beginning
