AURE NAKESO 💞💞💞💞💞

819 36 1
                                        

🅿🅿🅿🅿109-110🅿🅿🅿🅿🅿

Story by
M. HANNA

Edited by
M. HANNA

Written by
M. HANNA 💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔

Cast
Ikram
Hanan
Zahra
Zaynab
Samira
Sagir
Farhan
NABIHA
Nawal
Noor
Nuriyya
Ameer
Aminu
Mr nd mrs Ahmad zaki
Mr nd mrs ABDULLAHI SALIM
Aisha
Nawwara
Mai sunan mama
Nd other's 🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗

Ummah hanne ce zaune da hawayenta tace innalillahi wa'inna illaihir raju'un hajia guba kuma, ni kuwa wanene yakesan ganin bayan yar'ta? hajia ASIYA dake gefenta zaune tace haba dai maman aisha, ayyi wannan ba daga bakin ki yakamata ace ya fito ba saboda kema kinsan muma bazamu zauna mu zurawa komai ido ba, ayyi wallahi sai munbi mata hakkinta, mai sunan mama ta saukar da wata ajiyar zuciya kana tace toh yanzu mummy ta na ina? mummy tace tana uduth, yanzu haka nima shirin zuwa cen ne nake sai gashi kun shigo, ummah hanne tace toh ayyi zama ba namu bane yakamata mu hanzarta muje, hajia asiya tace yanzu kuwa amma ki goge hawayenki, haka akayi kuwa,dukansu suka fice zuwa hospital din

******kwance aisha take da drip a hannunta idanuwanta alumshe alamun mai bacci, cikin hanzari ummah ta karasa gunta, tare da zama gefenta, hannunta ta dora akan goshinta cikin rawar murya tace sannu kinji mamana, Allah ya baki lafiya, Allah ya isa tsakaninmu da wanda yakesan yaga bayanki, in sha Allahu mutuwa ba taki bace yanzu, mai sunan mama ta aje basket din hannunta agefen gadon, kana tace ummah yakamata hankalinki ya kwanta yanzu tunda kin ganta kuma ga numfashi tanayi ga alamu tana raye, hajia ASIYA tace gaskiya ne mai sunan mama, kiyi hakuri maman aisha, haka ummah tasa hannu ta goge yan hawayenta,kana suma suka nami guri suka zauna, kowa da abunda ranshi yake saka masa

**********10am*****
Misalin karfe goma na safe khalid ne a tsaye yana shirinsa cikin kaftan sky blue yayi kyau abunsa, tsaye yake ajikin dressing mirror yana kara gyara zaman hularsa, Addu'ar tashi daga baccin da naji ne daga kan gadon yasa na juya bakowa bane face khalifa, kwance idanuwansa alumshe yayi maganar, fuskarsa dauke da murmushi yace uhmmm my baby shine yau baki tadani ba? ya fadi hakan yana kara lalube agefensa, khalid ya juyo yayi murmushi tare da girgiza kansa, yace yaya khalifa? sai lokacin ya bude idanuwansa wadanda suka sauka akan na khalifa, zaune ya tashi tare da dafe kansa yace innalillahi wa'inna illaihir raju'un, hasbunallahu wani'imal wakil, khalid ne ya zauna gefensa yace kayi hakuri, ka shirya muje koh? khalifa ya dago da red eyes dinsa yace wane shiri zanyi nida ran matana yake kokarin daukewa, Khalid yace aaah tashi kaje ka watsa ruwa mana, ahaka dai khalifa ya nufi bathroom din dakin khalid, ya jima atsaye ba tare da ya cire kayan jikinsa ba yana kallan kansa ta mirror, bayan dan wani lokaci kuma ya saukar da wani numfashi kana ya shiga cire kayan jikinsa

***********khalid kuwa khalifa yana shiga bathroom yayi murmushi yace uhmm wani abu sai mace, nan ya mike ya nufi durowa, ya dauko jallabiya black mai ratsen white, nan ya shimfidata akan gado, ya fice daga dakin nasa yana smiling, fitowarsa kenan yaci karo da iyya dauke da faranti babba, mai flask da tea cups, sai dan plate rufe agefe, yace uhmmm morning my iyya, tayi murmushi tace yau kuma shi na samu, ya jikin yaya naka? Khalid yayi murmushi yace lafiyarsa kalau kawai su mummy ne ke masa kallan ya zautu, iyya tace toh Allah ya kyauta, ga breakfast din naku? khalid ya karba ya juya ya koma dakin, har lokacin khalifa bai fito ba, nan ya zauna akan carfet ya hada masu tea din, yana cikin cin chips din da fried egg sai khalifa ya fito daure da towel, nan ya shirya tsab cikin jallabiyar da khalid ya aje masa, yayi kyau abunsa, komawa yayi ya zauna a gefen gadon yayi shuru, Khalid yace ka sauko ka karya mana, khalifa yace no ci kawai, nan khalid yaci abincin sa, ya gama kana suka fice zuwa hospital din tare

*********isarsu kenan suka nufi dakin da aisha take kwance, khalid ne agaba, khalifa yana baya tafiya yake tamkar wanda kwai ya fashewa aciki, khalid ya shiga dakin bakinsa dauke da sallama yanda muka barsu ahaka muka samesu, nan ya sunkuya har kasa ya gaida ummah, ta amsa masa cikin sakin fuska, tace uhmmm surukina kana lafiya? ya amsa da lafiya ummah, ya mai jikin? tace toh ba abunda zance dan tunda nazo bata bude idanuwanta ba, khalid yace zata bude in aha Allahu, mai sunan mama ga gaida shi ya amsa cikin sakin fuska yana fadin har kanwarmu, tana smiling tace ina babban yaya ne? khalid yace ayyi yafi kowa shiga damuwa tare muke dashi amma tafiya yake yanda kikasan mai juna biyu, dariya sukasa har mummy, tace uhmm khalid kenan, suna haka khalifa ya shigo sulululu, tamkar bayada jini a jiki, ummah najin mai sunan mama tace babban yaya, yasa tayi saurin gyara zamanta ta kara sunkuyar da kanta, khalifa ya dago tare da sakin wani murmushi na dole yace my sis, yakke? ta amsa masa da lafiya lau, zama yayi sanadiyar jikinsa ba kwari, yace ya akayi kikasan batada lafiya? mai sunan mama tace tun jiya naketa kiranta bana samu, so yau da safe mukaje gidan akace ayyi kuna hospital, shine mukaje gidan mummy mukazo nan tare, khalifa yace dake dawa? nuni ta masa tace da ummah mana, cikin hanzari ya sauko daga kan kujeran da yake zaune ya sunkuya yana gaisheta ummah, ummah kuwa murya cen kasa take amsawa tsabagen nauyinsa da takeji, kunsan abunku da fulani

AURE NAKESO 💔💔💔💔💔Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang