*******wato ya maku amfani da kalamansa masu kashe jiki yayi introducing zaynab a matsayin matarsa, karya yake bashida wata mata, karuwarsa ce ta waje ya kawo har cikin gida, komawa tayi ta zauna tare da dora kafa daya akan daya,kasa hakuri tayi ta kara mikewa tsaye tace kai taya zan haifi yaro amma yayi kokarin fin karfina ko alama bazan amince da hakan ba, kai ta shiga girgizawa ta danna masa kira daya, biyu, uku, amma bai daga ba, fada take tana fadin haba dan Allah, wannan wacce irin rayuwa ce, tana cikin hakan khalid ya shigo, yanayin da ya samu mummy yasa shi cewa meyake faruwa ne mummy? dukansu juyowa sukayi, ganin idanuwan nawwara sunyi jawur tana hawaye, ya maida dubansa akan ummah yaga itama haka, ya maida su akan mummy yaga ranta abace yake ita kuma, yasa shi hadiyar yawun bakinsa da kyar, ya karasa kusa da mummy ya rungumota jikinsa yana fadin is okay mummy, relax kinji, tana a jikinsa ta dago kanta tace haba khalid mena rage khalifa da shi?
**********taya za'ayi khalifa yayi auren farko bansani ba, Khalid ya dan zameta yace kamanya auren farko baku kuka aura masa aisha bane? mummy tace sunce ba aisha bace matarsa ta farin zaynab ce,Khalid yace zaynab kuma? wai wacece wannan zaynab din da ta shigo rayuwarmu haka? metake nema ne gunmu? meyasa take kokarin raba kawunan mu take kuma kokarin hada uwa da da'a fada, who is she? mummy tace don't ask me khalid ask your brother, banida amsar ko daya daga ciki, khalid yace is okay toh, kowa ya kwantar da hankalinshi, kunga yanzu aisha is sick let her wakeup first sannan ayi abunda ya dace, mummy tace nima gaskiya zanfisan hakan, nan kowa ya samu ya tattara natsuwarsa
************khalifa kuwa bacci yayi amma ba cikin jindadi ba, dan duk ya tuna da halin da yabar aisha sai yaji bai mata adalci ba, amma wani gefe idan ya tuna da duk abunda takeso ne yake yiwa zaynab sai yaji kuma ya samu natsuwa, haka kuwa da sassafe bayan ya dawo daga sallah subahin ya samu gidan babu kyawun gani, yanda ya barsa haka ya samesa, baki ya tabe ya girgiza kansa yace tabbas alamu sun nuna mai gida bata nan, dan akoda yaushe naje sallahi subahin na dawo tun daga gate nake fara jiyo kamshin turaren gidan nan, hannu ya daga sama yace Allah ubangiji ya baki lafiya matata, nan ya aje charbin hannunsa, ya cire jallabiya ya rage daga shi sai boxers, ya shiga gyaran gidan, haka yaketa gyaran sa saida ya gyara fallo tsab ya gyara dinning, ya saka turare, kana ya nufi kitchen nan ya shiga wanke plate da food flask, chak ya kai kan wanda baa taba ba baki ya tabe yace toh wa kuma aka zubawa abinci anan? murmushi yayi yace Allah sarki yanzu haka nita sakawa abincin, nan ya tattara abincin da ya rage ya zube acikin wani dan kwano bayan ya gama komai ya fito da ragowar abinci har compound din gidan nasa, nan ya shiga kiran karen gidansa, maigadi ya fito cikin hanzari yana gaida shi, khalifa ya amsa masa cikin sakin fuska kuwa, dan karamin kare ne puppy brown, kai daga ganin shi kasan dan hutu ne, nan ya shiga zagayar khalifa,
********** murmushi khalifa yayi ya aje kwanon hannunsa yace oya eat yur food, nan karen ya shiga cin abincin, khalifa ya juya ya shigewansa, nan ya karasa komai na gidan, tamkar aisha tana nan, ya shiga hada masu breakfast, nan ya hada ruwan tea ya zuba a flask, ya hada masu sandwich da komai ya kammala, ya jera akan dinning, dakinsa ya shiga, yayi wanka ya sauya kaya zuwa wasu kananun kaya riga red wando black, yayi kyau sosai abunsa, ya feshe jikinsa da arabian perfumes masu kamshin gaske, knocking dinda yaji anayi ne yasa shi tsayawa chak, kara knocking akayi ya fito, yana budewa yaga gateman din tsaye, cikin kulawa khalifa yace lafiya? Ba tare daya iya magana ba ya masa nuni da puppy dog dinda ke kwance akan robar abincin da khalifa ha bashi, cikin hanzari ha fito ya karasa gunsa yaga jini yana fitowa daga bakinsa, nan ya aje karen ya koma ya fito da car key dinsa, ya dauki karen ya saka a mota, baiyi birki ko ina da shi ba sai hospital din animals, nan kuwa dr dinda ya shiga dubasa, khalifa yana tsaye dr din ya juyo da hand glovesa hannunsa yace am sorry ayyi ya mutu, khalifa yace nasan da ya mutu, inasan insan dalilin mutuwarsa, dr yace okay, nan aka shiga masa test na blood tamkar yanda ake yiwa mutane, bayan yan wasu mintuna dr din yace poison yaci, wanda ko mutun yacisa bana sa ran ya rayu idan ba Allah ya masa karin kwana a duniya ba, sannna it is more effective akan human beings nd also dangerous, wasu kan dauki week ba tare da sun falka ba, wasu kuma kan daukk years in comma, khalifa ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu sannan yace kana nufin ba food poison bane, poison ne?
YOU ARE READING
AURE NAKESO 💔💔💔💔💔
Short StoryMatasa ne mata uku, masu kudi, masu kyau, komai sukeso na duniya Allah ya basu but they are looking for true love, let's see how it gonna roles💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞shin zasu samu koya?
AURE NAKESO 💞💞💞💞💞💞
Start from the beginning
