AURE NAKESO 💞💞💞💞💞

Start from the beginning
                                        

******nan ya fito baiyi birki ko ina ba sai gidan dan uwansa malam usman, nan fah aka shiga mamakin ganinsa, da kuma yanda ya cenza, bayan sun zauna, suka gaisa sosai, malam usman yace kaima haka bai fiye maka dadi da rufin asiri ba, kana cikin iyalinka, hankali kwance, amma duk tsabagen kudi ne yasa ka manta damu, malam muhammadu yayi murmushi yace wadanni iyali kuma? malam usman yace su hanne mana, dan nasan acen kawai zaka samu sutura irin wannan, malam muhammadu yace toh kayi kuskure, ayyi kasan nagari basa karewa, nan ya kwashe komai ya gayawa malam usman, malam usman yace innalillahi wa'inna illaihir raju'un tabbas na gari basa karewa, wallahi banida labarin komai, ashe zamu kara ganinka, kai amma yaya naji dadin hakan sosai, malam muhammadu yace ni yanzu banida wani tashin hankali da ya wuce rashin sanin inda su hanne suke, wallahi nasan hakkin su akaina bazai barni ba, kuma nasan na zaluncesu na kuma cucesu, ka taimaka ka kaini gun hanne da yarana saboda neman gafararsu, kwana kin nan dasu nake kwana da kuma su nake tashi, malam usman yace Allah sarki, dama haka Allah kanyi abunsa, komai yayi farko zaiyi karshe, sannan duk abunda hakuri bai kawo ba rashin hakuri bazai kawo shi ba, na amince zan kai ka gunsu hanne, sedai gidan ita Aisha ne bansani ba, mai dakinsa ce ta fito tace aaaah yau babban bako ne damu? nan suka gaisa, tace yanzu kuwa zan gayamaka adireshin gidan, nan ta gayamasa sunan anguwar da aisha take aure, nan suka mike suka fice

***********zaynab ce kwance akan gadonta, wayanta a hannunta tana charting, kukan ruwan da naji ne ya tabbatar man da khalifa yana bathroom, kiran lion ne ya shigo wayanta, cikin hanzari ta tashi zaune, ta duba taga babu alamun fitowar khalifa, nan ta daga wayan murya cen kasa tace lafiya kake damuna da kira? ka kira daya biyu, baa dauka ba, meyasa bazaka daina Kira ba? lion yace kinga ni fah ba wannan zancen nakeso ba, ya akayi kwana biyu najiki shuru? wallahi don't play smart with me, zaynab taja wani dogon tsaki tace kaga banasan shirme, ya akayi ne yanzu? lion yace maganar kudinda mukayi dakene, ina bukace da kudi kuma ina bukace dake a kusa dani saboda babyna, zaynab tace kaga wane babyn kuma, yaushe ka damu da juna biyu dinda ke jikina? kaga yanzu dai ka daina kira na gobe zan kiraka dakaina mu hadu, bata jira feedback dinsa ba ta kashe wayan, daidai lokacin khalifa ya fito wanka saurin komawa tayi ta kwanta, yana fitowa ya shiga shirinsa

********saida ya kammala shirin nasa tsab, kana yace zaynab tashi ki watsa ruwa koh? zaynab ta masa wani kallo kana tace ina zamuje ne? khalifa yace bazakije ganin aisha bane? Zaynab ta kara gyara kwanciyarta tace mezai hana naje, zanje amma dai ba yau ba, khalifa dake tsaye yana feshe jikinsa da perfume ya juyo yace why not today? zaynab ko ta kansa batayi ba, ta lumshe idanuwa tace nadai gayamaka not today please, banasan repeating kaina, khalifa yace okay then no problem

************take khalifa ya shirya tsab ya dora hannunsa akan handle kenan, yaji zaynab tayi wata yar kara wayyooooo tare da dora hannunta akan juna biyu dinta, cikin hanzari ya juyo ya dawo kanta, rungumota yayi jikinsa yana fadin menene? gayaman menene? ina yake ciwo? Hannunsa ta dora akan kasan mararta cikin kukan shagwaba tace nan ne, ahankali yake shafawa yana kiran sorry kinji, sannu, azuciyarta kuwa cewa tayi uhmmm renin wayon banza, ahaka dai khalifa ya gyara rungumar da yayiwa zaynab tun yana duba watch har ya sadakar yaci gaba da aikinsa

*******bangaren su malam kuwa, busuyi birki ko ina ba sai gidan ummah hanne, suna zuwa malam usman yayi knocking, maigadin ya bude, kokarin shigowa sukeyi, sai maigadin yace kuyi hakuri, basa nan sun fita, malam usman yace kai yaro kodai ce maka tayi batasan damuwa gayamata cewa malam usman ne, maigadin yayi murmushi yace haba baba ayyi ummah batada hakanan kowa nata ne, wallahi ta fita, kaga cen motarsu bata nan ya fadi hakan tare da masa nuni da motor park dinda yake wayam, malam usman yace toh na yarda dan Allah, sai yaushe zata dawo? maigadin yace Allah banida masaniya, nan dai sukayi dai anjima, suna kan hanyar su, malam muhammadu yace kana nufi wancen gidan shine gidan hanne? malam usman yayi murmushi yace uhmmm shine kuwa, ayyi idan kanajin aljannar duniya gidan kenan, nan suka nemi mai adaidaita yakai su anguwar da aisha take aure gidan khalifa

******nan ma malam usman ne yayi magana, maigadin yace hajia bata nan, malam usman yace kaga kai dama ance dan iska ne kai, bakada kunya, iyayenta ne mu fah, kayiwa Allah ka bamu guri mu wuce, maigadin yace uhmmm toh yoooh karya zan maka baba Allah bata nan, malam usman yace toh ina megidan nata? maigadin yayi shuru kaman bazaiyi magana ba saida malam muhammadu yace ka taimaka, sannan yace yana ciki, malam usman yace alhamdulillahi, toh ka gayamasa ana sallama? maigadin yace toh ku shigo, shigowa sukayi tare da yin tsaye bayan ya rufe kofar gate din, yace karki biyoni fah, malam usman yace jeka kaidai haka akayi kuwa

*******maigadin ya isa tare da murda handle din kofar gidan, ciki ya karasa bakinsa dauke da sallama, shuru yaji, harya juya yaji muryar khalifa gana fadin waalaikassalam, juyowa yayi yace aaaah yallabai barka da fitowa, bayan sun gama gaisawa, khalifa yace lafiya kuwa? yace eh lafiya lau yallabai, dama wasu dattijai ne su biyu suka zo nemanka, khalifa ya dan dubesa cike da mamaki yace dattijai kuma? ce masu su shigo toh? har ya juya, zaynab ta fito tace kaga, je kace masu baya nan, khalifa da gateman din suka juyo lokaci daya, gateman din yayi tsurutsuru yana kallan su, khalifa yayi murmushi yace kin tashi kenan? bari nagansu mana, bakisan ko dame suka zo ba, tuni zaynab ta karaso tana kokarin masa kukan shagwaba, khalifa ya juyo yace je kace masu bana nan, gateman din yace toh yallabai, haka ya fice cikin hanzari

********zaynab tana rungume da khalifa yace uhmmm amma kidaina man irin haka banaso okay? zaynab ta dago tana murmushi tace kayi hakuri habiby, wallahi nisa ne dani banasan kayi amma bazan kara ba, ta fadi hakan tare da rike two ears dinta, yace tau muje ki kwanta koh? , cikin shagwaba tace daukana zakayi, haka ya dauketa kuwa kaman wata baby

*********yana fitowa yace kuyi hakuri fah, na dauka megidan yana nan, na shiga akaceman baya nan, malam usman yace toh kace kuma hajiar ita bata na, waya gayamaka baya nan kuma yanzu? Maigadin yace hmmm baba kenan dama ayyi mata biyu ne acikin gidan, amaryar ce ta fita, uwargidan kuma itace aciki yanzu, malam muhammadu ya maida dubansa kan malam usman yace dama mai mata ne aisha ta aura? malam usman yayi saurin girgiza kansa yace kaga ita kadai ce kawai dai shirme ne irin nasu, nan suka juya sukayi tafiyansu, malam usman yace kwantar da hankalinka kawai dai yau bamu taki sahun annabi bane amma duk nazo ina samun hanne a gida yau ne kawai, malam muhammadu da yayi shuru yace kaga yanda Allah yake lamarinsa yanzu hanne harda mota ce da ita? malam usman yace babba kuwa ingayamaka, ga gida lafiya lau, ga maigadi, yanzu haka raliya cen take zama yau tazo ganin mu, kabari duk sanda zata koma sai muje tare, malam muhammadu ya daga masa kai alamar toh


More comment
More likes
More vote
More post📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿

AURE NAKESO 💔💔💔💔💔Where stories live. Discover now