AURE NAKESO 💞💞💞💞💞

Start from the beginning
                                        

*********bayan sun gana gaisawa, ya koma ya zauna, mummy ta maida dubanta kansa, tace ya jikin naka? habarsa ya dago yace alhamdulillahi am fine, tace toh Allah ya kyauta, mikewa yayi tsaye yace bari naje gida na dawo, Mummy tace toh, car key din Khalid ya karba ya fice, inda ya tashi anan khalid ya zauna, mummy tace tunda mukazo nan fah babu wanda ya shigo, lafiya kuwa? khalid yace kinsan ayyi yana daukan lokaci, ya kanyu ward round suke yanzu zaki iya ganinsu, baki mummy ta tabe kana tace kasan sabo da private hospital nd overseas, yace hakane

********zaynab kuwa baccinta ta shaka sosai dan ko sallar subahin bata tashi ba, misalin karfe 11 na rana ta tashi, ko shi kiran waya ne ya tada ita, dubawa tayi taga lion dogon tsaki taja kana ta mike ta nufi bandaki wanka tayi, ta dauro arwala, tayi sallah kana, sannan ta gyara gadonta, ta fito, direct kitchen ta isa, nan ta hada ruwan zafin tea, ta hada tea ta fito hannunta rike da cup tea, sai lumshe idanuwa take tana karawa, fallo ta zauna tare da dora kafa daya akan daya, wayanta a hannunta tana shan tea tana scrolling through ig stuffs dinta,

***********kofar gidan aka bude khalifa ne ta shigo, bakinsa dauke da sallama, jin sallamarsa yasa zaynab saurin mikewa tsaye ganin yanda yayi tsaye da red eyes dinsa akanta ko kyabtawa babu yasa ta aje cup tea din cikin rawar jiki, aranta kuwa sai innalillahi wa'inna illaihir raju'un take fadi, tako yake ahankali, ganin yanda yake tunkarota yasa taji gabanta ya shiga bugawa tara tara, dakyar take hadiyar yawun bakinta, idanuwanta kuwa sai kyabtasu take ahankali kaman wata baby doll

********bai tsaya wata ba, yakai zaune, murya cen kasa yace get me something light to eat, jiki na rawa tace okay, direct kitchen ta nufa, ta hada masa indomie da fried egg, bayan ta karasa ta kawo masa komai a fallo, tare da jawo wata yar stool agefe ta dora plate din indomie akai, kasa zama tayi, juyawa tayi zata fice yace zoki zauna mana, ya fadi hakan ba tare daya dago kansa ba, jin hakan yasa ta wani ya mutse fuska kana ta karaso ta zauna gefensa, nan yakecin indomie dinsa kaman bayasan ci, cikin sanyi jiki yace get me water, mikewa tayi ta kawo masa ruwa ta zuba masa, saida ya karasa cin indomie din, ya kwanta akan cinyoyinta, tare da jawo hannunta ya dora akansa, idanuwansa ya lumshe, jin yanda jikinsa ya mutu sosai yasa itama taji duk ba dadi, take ta shiga shafarsa ahankali

*********sun dauki dan lokaci a haka kana khalifa yace yanzu zaynab wanene kike tunanin zai yi kokarin rabani da farin cikina? kaman daga sama taji tambayar tasa, dan karamin bakinta ta turo kana tace bangane ba, khalifa ya kara gyara kwanciyarsa kana yace ina nufin wa kike tunanin zai sakawa aisha guba a abinci? Zaynab ta wani hararansa kana tace taya zaayi nasani tunda nidai bazan saka maku poison a abinci ba tunda nima idan ta girka ina ci, kuma gani dauke da babynka, ahankali khalifa ya dago kansa ya sumbaci dan karamin cikinta, yasa kiyi hakuri, aisha tace masu condition dinku basasan damuwa da tashin hankali, take zaynab ta fashe masa da kuka na makirci, cikin hanzari ya dago yana fadin menene zaynab? mena maki? zaynab cikin muryar kuka tace duk kadaina damuwa dani, gashi babynka yana bukatar ka yanzu sosai, amma ko ajikinka, ganin yanda take kukan yasa shi rungumota jikinsa yana bata hakuri, ahaka dai ya lallasheta tayi shuru, nan yace bari ina zuwa, mikewa yayi ya nufi dakinsa, yana shiga tasa hannu ta goge hawayenta, taja gira, tace chawwww gaskiya samun kishiya irin ki aisha shine abu mai wuya, i will use dix opportunity na samu abunda nakeso

***********nan yayi sallah azzahar, zaynab ta girka masu abinci, tare sukaci, misalin karfe uku suna zaune a falo tana kwance ajikinsa, yace yakamata naje hospital naga aisha, jin hakan yasa zaynab saurin lumshe idanuwanta, yaba sunkuyo da kansa yace har tayi bacci, ya zanyi yanzu? Kara shigewa jikinsa tayi, kara cewa yayi aisha tace baa takurawa masu condition dinku, ya zanyi, bari mu gani zuwa la'asar, nan ya kira khalid ya tambesa jikin aisha? khalid yace still bata farka ba, khalifa yace okay toh yayi, ina dan wani aiki ne amma gani nan zuwa, akan kunnen zaynab akayi komai dan guntun murmushi ta saki kana ta kara gyara kwanciyarta, khalifa kuwa komai yake yiwa zaynab yau dalilin maganar aisha ne

AURE NAKESO 💔💔💔💔💔Where stories live. Discover now