BIYAYYA

1.6K 88 0
                                    

*😥😥BIYAYYA😥😥*

~NA~

*muneera*

🤪🤪🤪yau wanga page naki ne ke kadai *DIYAR KATIBI* kiyi komi ba komi muneera na tare dake iya wuya🤟🏻

*ZAMAN HOSTEL mabiya kuma makaranta wanan book din ku cigaba da hakuri kuma kuyiwa my Raheema addu'a Allah ba bata sa'a exam zata fara ne masu kirana da masu min text duk ga amsarku nan exam zata fara amma tana gamawa inshaa Allah zaku ganta ta dawo ta cigaba da nishadantar daku ⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀*

*16💞17*

Faruk mahaifiyar shi dake gefe ke kiran sunan shi Amma ina tuni yaja motar shi ya bar harabar gidan
Zaune take a dan corrodor na gidan su wanda duk wanda ya shigo tana iya hango shigowar shi sedai ita baza'a ganta ba kallon wanda yake fitowa daga motar take ta tsurawa wurin ido faruk ne ya fito murmushi tayi tana fadin bazaka dena min gizo ba faruk amma me gani tai tabbas faruk din ta ne da sauri ta fito daga wurin tana kallon shi, shima kallon ta yake sun kai 10mnt suna kallon juna kafin Ahlam ta saki wani kuka me tsuma zuciya faruk kaine? ka dawk gareni? mafarki nake? Shiru yayi yana kallon ta Ahlam dinsa ce ta rame haka Ahlam dinsa ce ta zama haka ya za'ai duniya ta juyawa Ahlam dinsa baya haka hawaye yaji yana zuba daga idon sa, itama kukan take tana fadin nasan ko kowa be yarda dani ba zaka yarda dani koo faruk ban aikata duk abinda ya fada ba faruk ka yarda dani hawaye ne kawai ke ambaliya a fuskokin su faruk ya fara magana koda bana kusa dake Ahlam zuciyata kullum na tare dake nasani Ahlam bazaki taba aikata wani mumunan abuba nasani Ahlam *kazafi* aka miki Amma Allah ma tare dake nasan ke me gaskiya ce a koda yaushe Ya akayi mutane har suka yarda da wanan sharin da aka miki ko kowa ya yarda ni bazan yarda ba dan Allah ahlam ki dena kuka ki yarda da *KADDARA* nasan ke me tawakalli ce Amma ni zan share miki hawaye koo ma menene kome kika aikata ni zan kasance tare dake *A DALILIN AURE* (na muneera) kin shiga matsala amma Allah ya sani ke me gaskiya ce Ahlam a koda yaushe yana gama fadin haka yace gobe zan turo manya na ayi maganar auren mu kallon shi tayi da shanyayun idanuwan ta tana girgiza kai alamar gaskiya ne kuwa daga mata kai yayi haka ne zan turo Ahlam yana gama fadin haka yai kokarin shigewa Motar shi yaji ana fadin kai karuwar zaka aura a fusace ya jiyo yana kallon shi a kowa bane se yusuf, faruk yayi gefe yana tofar da yawo A'uzubillah ,ni bana son magana da makaryaci wanda babu Allah a ranshi se zalinci da kazafi yusuf yayi wata irin dariya yana fadi kashhh na tausaya maka kai yanzu me zaka samu anan ka sani maza da yawa sunyi amfani da ita


A haka kake so da sauri faruk ya jiyo hade da shakar wuyan yusuf yana muzurai ku bar fada mana na yarda ni mazinaciya ce faruk ni karuwa ce kaji ko ka yarda duniya bazata yarda ba faruk ka nemi wace baxa a maka gori akanta ba yusuf bakomi burinka kaga bana cikin kwnciya hankali birinka ka bata min rayuwa ka yi kaji dadi nagode kaji tana karasa fadi tayi cikin gida da gudu faruk kuma ya kali yusuf yace koo maza dubu ne sukai amfani da Ahlam ka sani inason ta a haka bale nasan karya kake mata ma bata aikata ba mugu azalumi ka jira karshen ka yana gama fadin haka ya shige motar shi ya fice daga harabar gidan, a palo ya zauna inda ya tarar ba kowa kuka ya fashe dashi Aa Ahlam baki aikata ba nasani toh wa kike kulawa bayan ni meyasa duniya zata yarda kin aikata wanan mumunan aiki ni bazan yarda ba ko kowa ya yarda kijira ni Ahlam sena wanke ki daga zargi a idon duniya duk abinda yake fadi a kunen maman shi, karasowa tayi ta zauna tana fadin labarin abinda Ahlam ta aikata ya dade da zuwa kunena faruk Ko zaka hadiye zuciya ka mutu bazan taba yarda ka kawo min wanan yarinyar a matsayin suruka ba, bazaka lalata min sunan zuri'a ba bazaka taba auren ta ba ka cire ta ma a ranka faruk yana gama jin maganar da take ya tashi yayi daki batare da yace mata komi ba



Duk abinda suke A idon habib akayi shi yana ganin fitar faruk ya karaso inda yake ka bata kanwata rayuwa yusuf meya kawo ka gidan mu abinda kayi ma be isa ba ya fada a fusace hade da jan hanun yusuf yakai shi bakin gate yana fadin wallahi ka kara takowa cikin gidan nan duk abinda ya faru dakai kai ka jiyowa kanka wawa jahili kawai
Ahlam kuwa bangaren mamanta tayi ta sameta zaune akan daduma da alama sallah ta iddar gefe guda ta samu ta cure ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta, A hankali ta saki kuka me tsuma zuciya tanayi tana sauke ajiyar zunciya maman ce tayi gyran murya Ahlam kuka yanzu kika fara shi tunda rayuwar da kika zabarwa kanki kenan kuka gwra ma ki dan adana hawayen ki zuwa nan gaba ze iya miki amfani , mama ya...... Yi min shiru Ahlam bakida bakin da zaki min magana tana gama fadin haka tayi cikin daki ta barta wurin tana kuka harda shidewa.

dont forget to
#Vote
#commemt
#share



~muneera~

BIYAYYAWhere stories live. Discover now