Page 24

870 96 19
                                    

*MABRUKA*
_By Safiyya._

Page 24.

Kamar ta tashi daga barci haka taji, son tuno abinda yafaru takeyi amma iyaka inda Sabeer ya sanar da ita labarin dodonnin fadar sarki take tsayawa, girgiza kanta tayi dik cikin k'ok'arinta nason gano ya lamarin ya kasance.

Kallon hannunta tayi da yake cikin nasa ya matsa da k'arfi ta d'an zabura, ya kallota, motsa baki tayi a hankali tace "Me yafaru damu?, naji kamar na farka daga barci?."

"Bakomi beauty amma dai yanzu haka muna cikin d'akin Innaji ce, kinatsu pls banda tsiwa domin mace ce mai daraja arayuwata."

Wurin tasoma bi da kallo, d'aki ne mai fad'i babu wani kayan jan hankali hasalima tamkar dutsene aka fidda shape din room.

"Lale marhabin da bak'uwa mai daraja, haskenmu abin alfaharinmu." Sautin miryar Innaji ya dawo da ita duniyar kalle kallen datake k'arewa d'akin.

Sakin hannunta yayi ya tafi ya zube bisa guiwayinsa ya sunkuyar da kai ya soma yimata kirari "Uwa abin alfaharin yaronta, uwa d'aya tamkar da dubu, uwa mai share kukan gudan jininsa, uwata wacce tafi na kowa, sanyin idaniyata dafatan munsameki lafiya?"

Dafa kanta tayi cikin jin dad'i "Allah ya albakaci rayuwarka, Allah yayima jagora cikin lamuranka, k'udirinka na alkhairi Allah yacika maka shi, lafiya lau nake, dafatar kuma kun iso lafiya?."

"Amin Innaji, lafiya lau."

"Hakan akeso."

Tashi yayi ya zauna kusa da ita samar fatar damisa dake shinfid'e, ta janyo shi ya kwanta samar laps nata, shafar sumar kansa takeyi cike da kulawa shi kuma sai lumshe idanu yakeyi yana kallon Mabruka d'auke da murmushi.

Cikin wani yanayi Mabruka ta kauda fuska sakamakon tunowa da nata iyayen da tayi, kewarsu yake damunta barinma da taga Sabeer kwance samar cinyoyin mahaifiyarsa.

"Taho d'iyata, nima kamkar mahaifiyarki nake."

Tsirawa dattijiwar idanu tayi, farace sol tamkar Sabeer amma bata inda sukayi kama da juna, bata da muni saidai gajerace mai  cika idanu, sabida hakik'a tayi mata kwarjini, sanye take cikin doguwar riga amma samar kanta nad'e da k'aton fata wanda batasan ko nawani kalar dabba ba ne.

"Taho mana haskenmu." Ta kuma cewa tana mik'o mata hannu.

Cikin sanyi ta iso ta zauna gefenta tana lek'en fuskan Sabeer, abin mamaki barci yakeyi abinsa dan har da sakin numfashi alamar barcin nasa yayi nisa.

"Kingansa ragon maza daga kwanciya har barci ya kwashe shi." Innaji ta furta hakan tana shafa sumar kansa mai kama da na buzaye.

Murmushi tayi tare da kauda kai ga barin kallonsa.

Innaji ta d'auke shi daga samar jikinta a hankali ta ajiye samar fatar, ta mik'e wani lungu ta nufa bata jimaba ta fito d'auke da kwarya cike da fruits ta ajiye gaban Mabruka, tana mai furta "Bussimillah d'iyata."

Shiru tayi tana bin dattijuwan da idanu, ita kuwa sai d'auko kayar tarbar da ta tanadarwa bak'uwar takeyi tana jerewa gaban Mabruka.

Dangin abinci ne kala - kala da ababen sha sai kayan marmari masu tsafta.

"Ina yini mama." Ta furta da k'yar sadda taji Innaji ta zauna gefenta.

"Lafiya lau d'iyata, kici abinci ki k'oshi nan tamkar gidan ku ne."

'Allah ya tsareni tab'ewa da rayuwa cikin matsafa.'   Cikin ranta ta furta amma a zahiri sai ta amsa "To."

Hira tasoma janta dashi itakam tak'i cewa komi jin hirar nata tayi dik ya isheta amma bazata iya fad'a mata ba sakamakon kwarjin nin da take yi mata a tun kallon farko da tayi mata kuma da darajar Sabeer da taci.

MABRUKHAWhere stories live. Discover now