Page 21

852 94 6
                                    

*MABRUKA*

_By Safiyya._

Page 21.

Tana isa bakin k'ofar taja tatsaya cak, k'ofar tabi da kallo mai kyau dashi har da padlock ajikinsa d'an janyo handle nasa tayi taji a kulle yake 'Wato kulleni yayi kenan?' Ta furta a ranta.

Motsin tafiya tasomaji a waje sai anyi nisa can da tafiyar sai kuma adawo bakin k'ofar da alama wani abu ake nema a wurin.
Lek'awa tayi ta sak'on key numfashinta ne yakusa d'aukewa sakamakon ganin wasu irin halittu, ga sudai mutane amma jikinsu babu kaya sai fatar dasuka d'aura a k'ugunsu gashin kansu a cukurkud'e abin kyama, hannayensu d'auke da makamai masu had'ari.

Da baya da baya ta dawo ta zauna samar 2 seater wanda tagani a gefe d'aya.
Dafe goshinta tayi jiri na d'ibarta "Oh ni Mabruka nan kuma wace duniya na fad'o me d'auke da halittu masu ban tsoro?, Allahumma ajirni fi masibati wa kalifni khairan minha."

Suratul isra'i tasoma karantawa cikin zuciyarta, take natsuwa ya ziyarce ta duk wani tsoron datake ciki yayi k'aura, sai d'an abinda ba'a rasaba.

Ihu da kururuwa tasomajiyowa ta mik'e tsaye tana cigaba da karatun afili ta kuma zuwa bakin k'ofar ta lek'a halittun nan ta hango suna ihu da kururuwa suka nufi cikin daji, hamdalah tayi natsuwa na k'ara nashe hurinta.

Turo k'ofar yayi yana fad'in "Hello Queen of beauty kinga na jima bandawo ba ko?"

Banza tayi masa, ya k'araso gefenta ya zauna, hannun ta zai kama ta janye da sauri "Oh sorry natuna kina musulunci fa."

Idanu ta tsira masa, ya d'an kanne mata nashi, had'e rai tayi ya kyalkyale da dariya, ya zame zuwa samar rug yana mai janyo buhun bakkon da yashigo dashi, samira mai girma yafiddo sai plate da spoon, ruwan roba da big robar fanta drink, duk ya jere gabanta sannan ya bud'e samirar, jelof d'in shinkafa mai manja ce wanda taji wake luhu - luhu tare da nama manyan yanka, atake gamshi ya cika wurin.

Sliver nata ne ya tsinke, sai lokacin taji wani mahaukacin yunwa ya kawo mata ziyara, kallon ta yayi cikin murmushi "Oya sauko kici iya cinki dan nakine ke kad'ai."

Ba musu ta sauko ta d'iba a plate tayi bissimillah, sosai abinci yayi mada dad'i, tana gama ci ta kora da ruwa ta jingina da Cushing idanunta lumshe tace "Nagode Allah yabiyaka da gidan aljannah."

"Amin mai kyau."

Murmusawa tayi, ya saki ihu mai sauti ahanzarce ta mik'e tana kallonsa, dariya yabkyalkyale dashi yana nunata, komawa tayi ta zauna nata hasko banbancinsa da Mashkur ta hanyar d'abi'a, 'Eh hakika kam yanzu tasoma gano banbanci mai rata tsakaninsu, lallai da alama bashi d'in bane.'

Kama bakinsa yayi "Affuwan bansan zan baki tsoroba."

Shiru tayi, ya yamo hannunta ya matse cikin nasa "Bani labarin yarda akayi kikazo wurin danaganki, dan wuri mai had'ari ne ainun zuwarsa sai irinmu amma abin mamaki sai gashi nasameki wurin."

Zare hannunta tayi "saika soma sanar dani waye kai kuma nan wani yanki."

Kallon daya kafeta dashi ne take tsoro ya kuma ziyartarta addu'a tasomayi, murmushi yasaki ya janyo abincin da ta rage yasomaci cikin natsuwa, ita dai idanu ta zuba masa cike da fad'uwar gaba.
Saida yaci yayi nak ya saki gyatsa "Oh am very full."

Zare idanu tayi 'Shin wannan wani kalan mutum ne d'azun ya shigo ba sallama yanzu kuma yayi gyatsa babu hamdallah, abin mamaki kuma gashi d'azun zancentukarsa ya nuna kamar yana da sani a addini.'

"Kada kisake zuwa k'ofar fita tantin nan in har batare da ni ba ne."

Maganarsa yadawo da ita duniyar zancen zuccin da ta fad'a.

MABRUKHAWhere stories live. Discover now