03

1.2K 97 6
                                    

*MABRUKHA.*

Page 3.

Misalin k'arfe biyu da rabi na dare Mabrukha ta farka sakamakon mugun mafarkin da tayi addu'a tayi kamar yarda tasaba tashafe kijinta da shi sannan ta nufi bathroom.

Barci ne cike da idanunta amma hakanan ta daure tacigaba da jan tasbahan bayan idar da sallar nafilar da takammala badajimawa ba.

Tasami kimanin 1hr tana hailalah sannan wani barci mai dad'i ya kwasheta wanda yasa tasbahan ta kufce daga hannunta ta fad'i batare da ta saniba.

Motsin tafiyar dataji kamar sukuwar doki cikin dad'in  kuma daf da ita ya haifar da farkawanta a firgice tasoma waige waige amma bataga komi ba haka kuma tadainajin sukuwar dokin ba, shiru tayi tana nazarin wannan al'amura da suke son takurawa rayuwarta.

Mik'ewa tayi ta haye samar gado ta kwanta lamo tare da bawa Madeena baya wacce take ta sharan barcinta cikin kwanciyar hankali.

Miyawww!! miyaww!!!! Shine sautin da yasoma karad'e d'akin.

"Kukan Mage kuma cikin d'akina." Ta furta hakan  cikin tsoro.

Cikin hasken dabai wadaci d'akin ba ta hango fird'ed'iyar mage tsaye ta tsuro mata idanu jajaye kuma jikinta yana fitar da launi kala kala masu walk'iya wanda hakan ya hanata gano cikakken colour d'inta.

Saukowa tayi ta tsaya tana kallon magen cike da tsoro kuma ta kasa yin addu'a, sannau magen take matsowa wurinta tana cigaba da kukanta mai bantsoro dan in tayi kukan mage sai tajuya tayi na jarirai.

Ahaka ta iso gabanta ta bud'e bakinta masu d'auke da hak'ora zak'o zak'o bakin cike da jini yake, tayi wani girgiza ta daka tsalle zaka fad'o mata ajiki cikin hanzari ta gofce magen ta daki bango ta kwalla ihu cikin miryan mutum, jin haka Allah ya taimaketa tasoma karanta ayar _Wattaba'u matatitul shayad'inu ala mulki sulaiman....._ da k'arfi, atake magen ta kwala k'ara ta ba'ce.

Zama tayi bakin bed jikinta sai rawa yakeyi tana cigaba da karanto duk kan addu'ar da tazo bakinta.

Tananan zaune cikin zullimi har aka kira Assalatu, tamik'e jiri na d'ibanta ta d'auro arollah ta fuskanci alk'iblah tagabatar da raka'atanul fijir, tasoma karatun Qur'ani har zuwa lokacin sallar subhi yayi tatashi ta gabatar.

Tashin Madeena tayi dan tayi sallah sannan ta zauna yin Azkar d'inta kamar ko dayaushe, alfijir na fitowa ta sallame ta haye gado cikin k'ank'anin lokaci barci ya d'auketa.

Suna gabatar da breakfast amma hankalinta na wurin tunanin magen da tagani jiya ido biyu abin mamaki kuma wai so take ta halakata.

"Baben Abbanta ya dai, ko bakyajin dad'in jikinki ne?"

D'ago da idanunta tayi ta zube mata su k'uri.

D'an zabura tayi miryanta na rawa tace "Meke daminki Mabrukha?"

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali "Babu komi Mumy."

"To in har kin tabbatar hakane inga  kinsoma cin abinci kamar 'yarda yan uwanki keci."

Gyad'a  kai tayi batare da tayin mata magana ba tasoma kurban ruwan Lipton d'in da ta had'a, tana shanyewa tamik'e ta haye sama.

Da kallo sukabi bayarta, Muftah ya girgiza kai cike da takaici dan ya tabbata kome ke damunta baza arasa sa hannun mahaifiyarsa ciki ba.

Bajima ba shima yabar dining d'in, Momy tarakashi da harara kamar eyeballs nata zasu fad'o.

Sahal ya kyalkyale da dariya, Madeena ta kaiwa bakinsa bugu yayi hanzarin mannewa jikin Momy yana hararanta.

Tana had'a kayanta cikin k'aramin trolley Mama Gajiya ta shigo d'auke da sallama, amsa mata tayi batare da ta dakata da abinda takeyi ba.

Daf da ita Maman ta matso tayi k'asa da murya "Uwar d'akina jiya na fito shan ruwa naga k'atuwar mage tafito cikin d'akinki da masifar gudu ta shige d'akin Hajiya, kuma nakai mintoci talatin amma banga alamar fitowarta daga cikin d'akin ba sai nayi yunk'urin shiga nagani kotana lafiya aiko sai nagamu da gamona dan marika akayi tabani sadakarsu dama da hagu wanda suka gigitani, nad'imace da kyar nasamu na sakko k'asa da jan gutsu sannan nasamu sauk'i."

MABRUKHAWhere stories live. Discover now