04

1.1K 89 2
                                    

*MABRUKA*

Page 4.

Ganin ta sami barci sai ta d'auko Qur'ani ta zauna gefenta tasoma karantawa a cikin zuciyarta har lokacin sallar subahi yayi, tayi addu'a tashafe jikin Ummie sannan ta nufi toilet d'auro arollah.

koda tafito tasami Ummie zaune dafe da kanta da sarsarfa ta isa wurinta ta zauna rik'e da hannunta tace "Kai ne keyi miki ciwo?"

"A'a inadai son tuno mafarkin da nayi daren jiya ne amma na kasa."

"Ikon Allah."

"Haka nakeyi zanyi mafarki amma da zaran gari ya waye ban iya tunoshi."

Shiru Mabruka tayi tana jinjina lamarin.

"Tashi kiyi sallarki, bari na tada Madeena muyita cikin lokaci." Ummie ta ambata cikin raunin murya.

Suna gabatar da breakfast Ummie ta umurci Madeena ta tafi ta kirawo Mabrukha ayi breakfast d'in da ita, a tare suka dawo, zama tayi gefen Ummie tana lumshe idanu wad'anda suke cike da barci sakamakon barci da bata samu tayi daren jiya ba.

Kowa ya maida hankali yana lodawa tumbinsa abinci ita kuwa sai motsa tea takeyi da spoon, Ummie na lura da ita amma tak'i ce mata komi, saida ta kammala nata sannan ta d'auki teacup d'in ta kafamata a baki tare da tsareta da idanu kan dole ta shanyeshi tas, ta zubo farfesun nama tasoma bata shima hakanan tasoma amsa amma ba dan yanayi mata dad'iba.

Murjana da Madeena sai tsokanarta sukeyi wai ta zama baby, itadai murmushi take tayi masu tana maijin dad'i yau mahaifiyarta na cigar da ita abinda take muradi kenan arayuwarta, rayuwa bisa kulawar mahaifiyarta amma  Abbanta bazai tab'a amincewa ta dawo wurinta da zama ba.

Bayan kammalawarsu Madeena da Murjana suka fice yawon ganin gari ita kuwa tace su dawo lafiya ba inda zata ta kwasowa kanta rana.

Barci sukayi ita da Ummie, daf da azuhur suka tashi bayan sun gabatar da Sallah suka nufi dining inda iya kulu ta jere masu lunch.

Tana kwance samar cinyar Ummie suna hiransu ta d'a da uwa cike da nishad'i.

"Ummie amma kinsanko jiya mafarki kikayi wata zata cuceki ke kuma kina cewa sai kinga bayanta ko ke ko ita."

"Tabbas anyi haka, sai yanzu na tuno haka mafarkin ya kasance."

"To Ummie wacce mata ce kika gani cikin barcin naki?"

Jim tayi tana son tuno ko wace ce amma ta kasa.

"Kai bazan iya tuno fuskanta ba amma lallai matan azzalumace dan ko sanda na kwanta baricin da ban farkaba sai da na kwanta na yini ita ganani tazo tana yarfamin wani ruwa mai wari ni kuma ina tayin addu'a.

" Ya salam, Ummie wannan wani irin lamurane suke damunmu?"

"Jibeki da wani zance dai, to wannan al'amura su akekira da ikon Allah, babu tsimi babu da bara sai sun afku, abinda nakeso dake shine kada kigajiya wurin yimin addu'a ako da yaushe,  Allah yasane dani, jarabawarsa ce ina fatan Allah yalamuncemin wurin cinyewa"

"To Amin, Amma Ummie me kike tunani akan lamuran Momy?"

"Kamar na me fa?"

"Uhmm Ni dai gaskiya ina zarginta akan wasu abubuwa da dama."

"Mabrukha ki tsarkake zuciyarki ga barin zargi danshi zato zunibi ne mai girma ko abin gaskiya ne balle naki hasashe ne baki tabbatarba, dan haka  koma me kike son sanar dani game da Hannatu to dan Allah kirik'e kayarki bana buk'atar jinsa sabida da inayi masa kyakykyawan zato haka ina yabamata da kulawar datake baki dan ko ni iyakar abinda zan iya yi miki kenan, Allah yasaka mata da alkhairi dai."

MABRUKHAWhere stories live. Discover now