Page Twenty Five

4.6K 220 5
                                    

🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)

Ummu Subay'a

dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)

🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻

Maman Rufaida
Ina yinki irin ssai din nan

Congratulation Sameena Aliyu
Gaskia kin fadakar damu, kin nishadantar damu kuma kin wa'axantar damu
Allah ya saka da alkhairi
Allah ya kara basira, daukaka, hikma tareda fikrah
Gaskia A Duniyarmu  yayi ssai

Up up up Sameenanmu❤❤❤❤

               2⃣5⃣

Ko sallama bbu Ma'u ta bude kofar falon Bature ta shiga, bata samu kowa a falonba ta wuce bedroom direct

Zaune ta sameshi yana aiki akan laptop, tsayawa tayi akanshi tana kakkada jiki irin na isan nan, da mamaki Bature ya dago yana kallonta

"Amma ina xaton kin san inda kike koh?"

Baki Ma'u ta tabe tace

"Ai ni ba mahaukaciya bace kuma ba makauniya bace, naxo jin dalilin dayasa xa'a sawa diyata suna Zahra, idan kanason mata takwara ai sai ka kara haxaka ita kuma ta baka hadin kai sosai sai Ku samu Baby ka mata takwar..........."

Wawan Marin da Bature ya xabgawa Ma'u ne ya katseta daga xancen datake, durkushewa tayi kan gwiwarta tasa kuka, da dan yatsa ya nunata

"Wlh kinyi kadan kixo kinamin wannan iskancin naki, taimakonki daya kina jego da bbu abunda xai hana namiki shegen duka, oya fice kiban waje tun kan na canxa xuciata na miki shegen duka"

Mikewa Ma'u tayi bakinta a ture ta nufi hanyar fita bedroom din sanda takai bakin kofar tace

"Ni wlh idan har aka sakawa diyata Zahra xa'aga ba dai dai ba, kuma sai na karantawa mutanen karatun haukawa wlh xan kankaro mutunci"

Tana direwa ta fice da gudu tabar dakin

Cije lips Bature yayi ya kada kansa irin xan kamakin nan

A bakin part din Ma'u ta hadu da Zahra na shirin shigowa, tsayawa Ma'u tayi ta tare bakin kofar falon

Kallon mamaki Zahra ta tsaya tanama Ma'u

"Ke lfy? Bani hanya na wuce sauri nake"

Dariar renin wayo Ma'u tasa tace

" wai ke kinajin dadi xa'a miki takwara ko? Gaki mowan miki, idan takwara kikeso ai sai ki xage ki dage ki haifo diyarki a miki takwara da tushe, kuma baxaki wuceba don banga amfanin shigarki turakaba"

Kuka Zahra ta saka ranta na kuna ta juya da gudu ta koma part din Ummi

Tsaki Ma'u taja

"Aikin banxa"

Washegari suna kamar yadda Bature yadau niya sunan Zahra ya sakawa diyarsa

Ado ssai Ma'u tayi ta fito daga part din Ammi ta nufi part din Mami da diyarta a hannunta

Maroki na ganinta ya taso da sauri ya sha gabanta

"An gaida tauraruwar mata Amarya a gidan Alhaji Bature wato Hajiya Asma'u Maman Zahra hasken mata"

Harara Ma'u ta bugawa marokin kamar xata mareshi

'Don Allah malam matsamin a gaba na wuce, a'a ba Maman Zahra ba uwar Zahra"

Batool dake tsaye bayan marokin tace

"Tafi kayanka kada laifin da ba takaba ta shafeka, jecan kace a nuna maka Zahra, acan xakayi kirarinka"

Gidan BatureKde žijí příběhy. Začni objevovat