Page Seven

4.2K 287 14
                                    

🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)

Ummu Subay'a

dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)

🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻

Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA  don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin  MIEMIEBEE

Gaisuwa ta musamman ga
Ummu Muneeb

Happy Anniversary🎂🎂

Kainuwa Writer's Association

Allah ya kara mana Basira, hikma, Fikrah da haxaka

Allah ya kara mana son junanmu

Jinjina ga
Batool Adam Jattko
Anty Fauxy (Mrs Talba)
Maman Rufaida
Zainab Goni
Maimuna Matar Abdullah
Halima Mk
Khairy

Da duk WRITER'Sna KAINUWA wadda ban ambaci sunansuba

KAINUWA DASHEN ALLAH BA DASHEN MUTANEBA

               0⃣7⃣

Handsfree Bature yasa bayan yayi picking na wayar

Maimakon yaki muryan Abba sai yaji na Ammi

"Ba Bature kake ba ko Nasara kake ka dawomin da Ma'u ko na wanke kafa naxo Abujan don kasan Abujan ba bako na bane tun kan na haifi ubanka nake xuwa Abuja"

Hannu Zahra tasa ta rufe bakinta da daria ke shirin kubce mata kada Ammi taji ta samu nata kason

Tsayawa cak Ma'u tayi tana Allah Allah Bature ya yadda ya maidata

"To ni meya dameni da sanin Abujanki, Ma'u dai gata da yardarta naxo da ita, idan kuma kin musu gata kiji daga bakinta"

Cewar Bature yama Ma'u dake kallonshi alama taxo

Jiki bbu karfi Ma'u taje gaban Bature ta durkusa,idonta sai tsiyayar kwalla yake

"Ko kunne dubune a jikina wlh baxan yadda Ma'u ce ta amince xata bika ba dan rainin hankali"

Mikawa Ma'u wayar yayi tare da mata mugun kallon kashedi

Jiki na rawa Ma'u ta amshi wayar cikin sanyin murya tace

"Hello Ammi"

A dayan bangaren Ammi tace

"Ma'uta ya akayi kikabi Bature, ni nasan ba da amincewarki bane koh"

Kai Ma'u ta daga alamar "eh" kamar Ammin na gabanta, kafarta Bature ya shure, tayi saurin cewa

"A'a da amincewata ya tafi dani, ni nafison xaman nan"

Ganin kuka na shirin kubce mata ne yasa Bature hanxarin karbar wayar yace

"To ai kinji da kunnenki sai kibar mutane su huta"

"Duk wannan mana kisanka ce dan goyon Hauwa ai bbu abunda baxaka iya......."

Kyat Bature ya katse kirar don bayason a xaga masa Umminsa

"Oya tashi kiban waje Mayya"

Cewar Bature yana kara janyo Zahra jikinsa

Tashi Ma'u tayi ta nufi bedroom din tana kuka a hankali gudun kada Bature yaji ta kuma wani laifin

Gidan BatureWhere stories live. Discover now