Page Four

4.3K 316 7
                                    

🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)

Ummu Subay'a

dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)

Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA  don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin  MIEMIEBEE

Harufai sunyi kadan su kwatanta yadda kike a wajena, sai dai nadan sakura kadan na bayyana matsayinki a wajena
Kinfi Aminiya
Kinfi 'yar uwa
Kinfi kawa
Keta dabance a wajena BATUL ADAM JATTKO
Fatana Allah ya kara miki lfy, daukaka, basira, fikrah, da kuma hikma
Allah ya biya miki dukkan bukatunki na alkhairi, ya sadaki da masoyanki ta ko'ina, ya kuma rabaki da makiyanki
Allah ya baki nisan kwana mai albarka da amfani
Allah ya shirya miki xuri'arki ya dorasu akan tafarki madaidaiciya
Allah yabar xumuncinmu daga nan har a Aljannah
Ke Tawace BATUL
I heart u♥
               0⃣4⃣

Tunda Ma'u ta farka daga bacci cinyoyinta ke mugun mata ciwo, bata isa ta xauna ko ta tashi ba sai taji a jikinta, Sallah Asuba ma a xaune tayi, taba iddarwa ta koma bed taja blanket taci gaba da baccinta sau uku Batool na xuwa ta tadata akan ta tashi ta shirya su tafi skul sai tayi kamar xata tashi Batool na fita sai ta koma taci gaba da baccinta

Koda Mami taxo ta ganta bata tada itaba don tasan ba abu mai yiyuwa bane taje makaranta yau,
Kintsawa Mami tayi ta fice falo donyin break fast

A hasale Bature ya shigo Falon kamar xai kife don sauri, ko inda Mami take ba duba ba don yasan  xata iya hanashi xantar da hukunci da yayi niya

Aikuwa bai tsiraba don yana kama handle na bedroom dinta tayi hanxarin cewa

" kul kul, kada ka yadda ka shegemin bedroom, ka tattara kaje can NDA ka saukar da fushinka don su suke bida mukam anan bama bida, inba rashin tausayiba jiya ka gama nakasa mata kafa yau kuma kana expecting xata iya mikewa har taje makanranta aljana ka maidata ko mayya, maxa bacemin daga part, ka bari sai masu son kaita kabari sun danka maka ita sai kai yadda kakeso da ita amma ba a gaban Fateema ba"

Ta karashe maganar tana masa mugun kallo

Hannusa Bature ya janye akan handle na kofar ya dorasu akan sumarsa ya wargaxa sumarsan dayasha gyara ssai

Cikin murya bacin rai yace

"Wlh Mami keda Ammi Ku kuka bata Ma'u, take duk iskancin nan, wani punishment na mata wadda har xai nakasa mata kafa ta gaxa tafia School (kujimin Bature fah), Allah idan da Jidda bata kawo shawarar nan ba idan har ta girma akan yadda kuke tafiar da ita mai aurenta ma sai an rasa, idan kuwa ansamu ya aureta a rashin sanin halayenta to baxai iya xama da itaba"

Baki galala Mami ta bude tana duban Bature daga bisani tace

"Har kura xai cewa kare maye, kaima da murdadden halinka ka samu wadda ta aureka balle Ma'u, ai ni kullum jinjinawa Zahra nake da ta iya xama dakai"

Daria Jidda data shigo yanxu tasa tace

"Ikon Allah kedai Mami duk wadda yace bayayin Ma'u to duk kyaunshi mummunane"

" yawwa jira nake kixo ki sameni, Jidda idan har Bature ya nakasamin diya kema sai na nakasa don xan biki har Lagos na miki yadda ya mata tunda kin iya kawo gurguwar shawara, kuma idan.Ammi tasan ke kika kulla wannan munafurcin kin daina kallon hakorarta"

Gidan BatureWhere stories live. Discover now