Page Five

3.9K 275 16
                                    

🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)

Ummu Subay'a

dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)

🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATE🤝🏻

Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA  don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin  MIEMIEBEE

               0⃣5⃣
Washegari tun karfe 6 Bature da Zahra suka gama shiryawa dasheka Bature a Kaduna ya kwana

Suna tsaye a parking space Bature ya kira Jidda a waya ta kawo mishi kayan Ma'u kuma ta tabbatar masa Ma'u na bedroom na Mami tana kwance ita kadai

Hade fuska Bature yayi kamar hadari

Balarabe yasa daria yace

"Man duk wannan hada fuskar duk na Ma'u kamar mai xuwa sambisa tunkarar Shekau, lalle Ma'u ta cika boss"

Duk sukasa daria banda Bature daya nufi part din Mami

Zahra dake saka handbag dinta cikin mota tace

"Ai ta'addancin Ma'u yafi na shekau"

Jidda data lafe jikin Balarabe tace

"Wlh har tsoro take bani, bbu hali ta bayyana a waje bomb bai tashiba, idan kunason xama cikin sauki da ita sai Ya Bature ya xama Buratai ke kuma kin xama Kukasheka"

Daria suka sake sawa Balarabe yace

"Muma xasu barmu da wata Shekau din ai, idan Ammi ta farga bbu Ma'unta ai sai ta dagawa kowa hankali musamman idan taji Baturene yayi awon gaba da ita"

"Idan xata daga mana hankalin ban muma mu tattara mu koma yau"

Cewar Jidda tare da dagawa Balarabe jera daya

Kasa yayi da murya don kada Zahra taji mexai ce yace

"Da hakan xai faru dana more, nayi missing na komai.ssai"

Murmushi Zahra tayi data gama jin komai ta xauna a kujerar dake wajen

Baccinta take mai dadi don ta gama sakankancewa  Bature ya kama hanyar Abuja batada wani fargaba

Tsayawa akanta yayi yana kare mata kallon tun daga gashin kanta daya barbaxu ya rufe mata fuska har tafin kafanta, short night gown ne a jikinta iya gwiwa yabi jikinta ssai

Hips natane ya janyo hankalinshi kan kallonta wani abu yaji yana masa yawo a xuciarsa

Kawar da fuskarsa yayi ya kori shedan hadda cewa

"Yar Ma'un nan idan ba shedan ba me mutum xai kalla a jikinta(hmmm Bature kenan)"

Kusan 2minutes yana tuna yadda xai tadata, murmushin mugunta ya saki daya tuna favorite tadata dayake lokacinda take primary idan taki xuwan school ta koma bacci

Fridge ya nufa ya ciro gorar ruwa mai tsanyi har ya fara kankara ya bude gorar watsa mata a fuska

A birkice Ma'u ta tashi xaune tana tattare gashinta don taga wadda yayi mata wannan aika aika ta maida mai martani yanxu basai anjima ba

Kara firgicewa tayi ganin Bature na tsaye akan fuskarnan tashi a daure tam wani mugun miyau ta hadewa ta fara magiya

"Wlh yanxu xan tafi school, Allah kuwa yanxu xan......."

"Up that ur dirty mouth and dress up"

Hurga mata hijab na Mami daya dauka a gefen bed din yayi

Jiki na rawa Ma'u ta sanya hijab din

"Follow up"

Bature ya fada a dakile bbu wasa ya bude kofar bedroom din ya fice

Sauri sauri gudu gudu Ma'u ta shiga bin Bature

Daria Su Jidda suka sa time da suka hangi Ma'u da Bature

Jidda tace

"Don Allah dubeta kamar ba itace ke wadan nan abubuwanba"

Zahra ta mike daga xaman datayi tace

"Tom and jerry xanje nasha kallon movie"

Rumgumar juna Jidda da Zahra sukai suna sallamar juna Jidda tace

"Insha Allah next month xaki ganni"

"Yasha'ullah"
Cewar Zahra ta janye jikinta daga na Jidda

Hakama Bature da Balarabe suka rumgume juna Balarabe yace

"Man pls kada ka dinga dibo alluran sojanka kana saukewa Ma'un Ammi"

Hararar inda Ma'u ke tsaye Bature yayi yace

"To naji Abba, nidai kabimin kanwa a hankali don nasan yanxu kana hannu kada bayan 2months muji wani cikin"

Ya sauya topic da Balarabe ya dauko

Bayanshi Balarabe ya duka yace

"Banason sa ido bbu ruwan mutum dani"

Sake juna sukayi suna murmushi

Ma'u take tsaye tana binsu da ido a cikin ranta tace

" Niko Uban me ya kawoni inyi anan? Yayi ya tafima mutum ya huta wlh, ya saura Anty Jidda itama ta tattara na koma free world na (rashin sani yafi dare duhu inji hausawa)"

Bayan sun gama sallamar juna Bature ya shiga driven site ya xauna, abunda yake burge Family dashi kenan duk matsayinshi a Soja duk kudin gidansu Sam baya bari driver yayi driving dinsu shida iyalinsa, shida Kansa ke driving

"Ma'u shige muje"

Cewar Zahra tana kokarin shiga motar

Ido Ma'u ta xaro tanama Zahra kallon mamaki

"Baxaki ji menace bane ko sai Ya Bature yaxo ya miki da yaren da kikafi fahimta"

Zahra ta sake cewa tana rufe kofar motar

Ganin kofar side din Bature na girgixa yasa Balarabe saurin tura Ma'u data tsaya kamar mutum mutumi tana kallonsu don Neman Karin bayani cikin motarta ya kulle

Ta bashi tausayi ssai Sam bayason tun anan Bature ya  kirbata

Jam motar Bature yayi ya fice a Bature estate

Mamaki, firgici, da tsoro su suka lullube Ma'u da hawaye keta ambaliya a fuskarta, tanason karin bayani amma bbu mai fahimtar da ita

Saura kiris fitsari ya xobo mata lokacinda taga suna fita daga garin Kaduna

Zahra kam ma ta manta da wata Ma'u sai hira ta ke ma Bature na mugunta ya murmusa don baya murmushi sai ta baci

Wani raxanennen ihu Ma'u tasa mai raxana duk wadda yaji

Karfin ihun yayi tasiri a kunnen Bature sake siterin motar yayi yana kokarin toshe kunnensa yama manta yana tuki

Tangal tangal motar ta fatayi kan titin, ga tank na Total oil ya nufo saitin motar

Sautin Haduwar karfe da karfene ya cika wajen wani kiyyyyyyy........... Kakeji

Me kuke xato xai faru?

Idan bbu abunda ya faru wani irin xama Ma'u zatayi a GIDAN BATURE?

Ya kuma 'yan GIDAN BATURE xasu kare da Ammi idan ta fahimci Ma'unta bata BATURE ESTATE?

Kuyi hakuri da karancin page nan Night duty nake banda isheshen lokaci ga Fans ta ko'ina suna bidar ci gaba

My Fans ❤
Duk inda kuke ina yinku ssai
Irin ssai nan fah
Heart you all♥

Gidan BatureWhere stories live. Discover now