Page one, two, three

13.3K 509 26
                                    

🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story & Family Saga)

Ummu Subay'a

dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)

Wattpad UmmuSubaya

Ina mai bawa SOYAYYA CE fans hakurin rashin ci gaba da banyiba a dalilai na tsaro

Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA  don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin  MIEMIEBEE

               0⃣1⃣

"MA'U MA'U MA'U pls xo kiban littafina ai bani na hanaki yin assignment dinba, kuma ai kinsan ina baki ki copy idan har ba'a mana gargadin kada a kawo iri dayaba"
Wata yarinya ce da baxata wuce shekara 15 ba takebin wadda ta kira da MA'U itama baxata wuce 15 years dinba, tanata mata magiya

Amma ko a jikin Ma'u sai tafiarta take kamar ba da ita akeyiba hadda guntun dariarta

Palon Amminta ta nufa kai tsaye anan ta taradda Anty Jidda tana bawa diyarta Amal nono, tunda taga Ma'u ta shigo da sauri tasan akwai magana

" wa kuma kika tabo  Anty Masifa" bata gama rufe bakinta ba Sukrah ta shigo kamar xatayi kuka

Murmushi Anty Jidda tayi tace

"Nasan xa'a Rina ai, Shukrah me tayi miki?"

Hawayena suka fara ambaliya a fuskar Shukrah

"Assignment nawa ta kwace wai xata kwafe kuma.tacewa Uncle namu nice na kwafe nata baicin kuma yace bayason copy copy"

Kallon bbu wasa Anty Jidda tama Ma'u wadda take tsaye ta kama kumkuminta kamar wata babbar mata

" maxa bata littafinta"

Bani Ma'u ta tura tace

" wlh baxan bataba don ban yiba kuma ban iyaba, da a dake ni daya gwara an dakemu mu biyu"

" xaki bata ko sai na tashi na babbalaki a wajen"

Ganin sarai Anty Jidda xata aikata abunda tace don tasan ba'a kawo mata wargi yasa ta fara kwadawa Amminta kira

Ai kuwa bbu bata lokaci sai ga Ammi ta bayyano

" keda wayene? Sam ba'a barin kuruwarki ya huta sai an dinga daga miki hankali"

Ssai Anty Jidda ta bata rai tasan sarai yanxu Ammi xata goyi bayan Ma'u

"Wlh Ammi kekike goyawa Ma'u baya take duk fitsarar dake, har ta isa na bata umarnin tace baxatayi ba, wlh kada kiga idon Ammi idan bakiyi maxa ki bata littafinta ba bbu Uban da xai hanani  farfasa miki jiki da duka"

" uwar ubankine xata hanaki fasa mata jiki da duka kinji ko nace ni nan Asma'u uwar Ahmad ubanki ni xan hanaki fasa mata jiki da duka, littafi kuma baxata bayarba, ke kuma munafuka kinyi fuska kamar wata munina kina jira a amsa miki littafinki to baxata bayarba maxa bacemin daga part

Da gudu Shukrah ta fice tana kuka mai ban tausayi don ta tabbatar littafinta ya tafi kenan forever

A balcony Shukrah taci karo da  Zahra, har xata wuceta Zahra ta kamo ta

Gidan BatureWhere stories live. Discover now