Page Six

4.6K 303 4
                                    

🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)

Ummu Subay'a

dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)

🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻

Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA  don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin  MIEMIEBEE

Allah ya baka lfy Admin of Admins Yahya Hayat
Allah yasa kaffarane😥😥

Jinjina ga

Fikra Writer's Association
Mussamman
Rufaida Omar
Bingel

Allah ya kara basira nagode da kaunarda kuke nunamin❤❤

Gaisuwa
Maman Fauwaz
Aisha Bala
Maman Abdul
Da duk wadda ban ambaci sunansuba

Ina yinku irin totally nan RUFAIDA OMAR FANS (ROF)
Allah yabar xumuncin soyayya🤝🏼

               0⃣6⃣
Cikin xafin nama Bature ya kama siterin motar don kaucewa Tank din, Amma sanda Tank din ta goge jikin motar

Suna wucewa Bature yayi Hamdala tare da limshe ido, Zahra da ta gama sadarkarda rayuwa da sauke ajiyar xucia tace

"Alhamdulillah"

MA'U kam bbu magana don har ta fara digar fitsari tsabagen tsoro, sai raba ido take kamar mage

Ta mirror mota Bature ya balla ma Ma'u harara yace

"Shegiya mayya wlh sai dai ki kashe kanki badai niba"

Duk da firgicin da Zahra ke ciki bai hanata sa daria ba tace

"Allah ya kare na gaba"

          KUJE BARRACKS ABUJA

Sunan kawai da Ma'u ta kalla tasan ta kade ba karamin jin jiki xatayi anan ba ga Ya Bature Anty Zahra (sey ko Allah wadi inji Fulani)

Suna shiga cikin GIDAN BATURE Zahra ta xabawa Ma'u bedroom mai kyau tasa masu aikinta suka kai kayan Ma'un

Duk kyau da tsaruwar bedroom din bai burge Ma'u ba damuwarta kawai ta ganta a Bature Estate kusa da Amminta

Kasan tiles ta xauna ta fara fanshe kukan da bata samu tayi a mota ba

Wucewa bedroom dinsa Bature yayi wanka ya fara kan yaxo ya haye kan bed ya fara baccin gajiyar dayayi kwanaki

Ga Zahra ma hakane wanka tayi ta haye bed dinta tayi bacci

Kuka Ma'u taci ssai har ta fara kallon dishi dishi fararen idanunta sun koma jaja wur

Anan kan tiles baccin wahala ya kwasheta

1:10 alarm na wayar Bature ta tasheshi daga bacci, mika yayi hadeda salati ya nufi toilet yayi alwala ya fito ya nufi bedroom na Zahra

Gaban mirror ya sameta tana make up daga bakin kofar ya tsaya yace

"Tun daxun kika tashi kenan?"

Murmushi ta sakar masa tace

"Eh tun 12:30 na tashi"

Baki ya tabe yace

Gidan BatureWhere stories live. Discover now