page 06

1.2K 86 0
                                    

  Cikeda kidimewa Hajiya Halima ta kira driver domin yakaita Kano instantly dubaga karya da gaskiyar da Inteesaar ta fada mata,kara kiran Inteesaar din tayi awaya ta shaida mata suna hanya in less than 2hours zasu karaso dayake Hajiya Halima katsina based ce.Cikeda murna Inteesaar tashiga kitchen tashiga shirya ma mahaifiyar tata abinci,shinkafa da miyar kaji tamata sannan tahada coleslow ta jere abincin a dinning tana jiran zuwan mummy,jin karar horn yasa ta daka tsalle tafita dagudu ta rungume Halima da fitowarta kenan daga cikin motar.cikeda mamaki take kallon Inteesaar acewarta wai tayi duhu sannan tadan rame"na shiga uku ni Halima me Ahmed ke miki agidan nan,wannan wani irin zama kukeyi?"shiru tayi tareda jan Halima cikin gidan sede kansu karisa shiga Inteesaar tace"driver nan wuyanshi yyi kauri kina gani koya gaisheni"..da bacin rai Halima tace"zonan mara mutunci "dajin wannan kalamin yasan dashi take shiyasa shi zuwa jiki na bari,"bakaga Inteesaar bane?",jiki na kyarma yace"naganta"..."au shine baka gaisheta sbd bakada mutunci?"..be tsaya jin karashen cin mutuncin Halima ba ya russuna yagaida Inteesaar,aikuwa tayi banza dashi tareda jan uwarta su shige gidan.Suna shiga gidan Hajiya Halima ta yarda jaka da mayafi ta tsurawa inteesaar ido,"zauna mana"tace ma Inteesaar dake tsaye"sonake na dauko miki abinci ko akan dinning din zakici?"..jawota zuwa jikinta Halima tayi tana fadin "bar abincin for now,ni yanxu babban tashin hankalina shine duhun da ramar dakikayi,baya baki abincine?bakya jin dadin zaman ne shine baki kirani kin sheda min ba?Haka alqawari yace?gaskiya baki kyauta min ba kwata kwata"Halima takarashe maganar in a sad tune,hannunta Inteesaar tashiga murzawa ahankali "sorry mummy wallahi nazata zan iya shawo kan lamarin ne".."Allah sarki yar mummy,sekuma me kikace yana miki?"..."chatting da yanmata,mummy wallahi Elmoudan na gab da kashe miki ni,domin kinsan I am insane when it comes to him"gumi Halima ta share tace"yan mata "gabanta ya yanke ya fadi "nashiga uku,yan mata fah kikace?"girgiza mata kai tayi alamar gasgata maganar kafin Halima tace"beko isaba,ko uwarshi bata isa ba bare shi,ze zo yasameni dede wadeda. Yau seyaga bacin raina ".."yawwa mummy sannan wai ni zan riqa masa girki kullum...".."ai ba jaka ya dauko ba sannan be fadi haka ba sanda ze aureki dan haka bbu girkin dazaki rinqa yi "..."yawwa mummy inyazo karki masa da wasa musamman akan batun yan mata."..."kada ki samu damuwa yar mummy zanyi yadda bakiyi zato ba "dariya suka saki atare sannan suka kashe. Anan Inteesaar tagabatar mata abincin,kallon mamaki take jifan Inteeesaar dashi"waye yyi girkin nan".."waye zeyi banda ni?".."don't tell me bakida househelps har yanzu?"..ahankali Inteesaar ta girgirza mata kai alamar Ehh,salati Halima tasaki "yanzu kece meyin komai na gidan nan?sannan yakecewa kiyi girki saboda bashida imani?"Shiru Inteesaar tayi "lallai be dauko abinda zamu shirya ba"Halima takuma fadi tana girgiza kai,sallamar Ziyada ce ta katse musu hirarsu,dagudu suka rungume juna suna yaushe rabo,"Ziyada kinganki kuwa?".."Inteesaar kinganki kuwa?"atare suka kwashe da dariya."kinyi fari kin kara kiba wallahi "cewar Ziyada."ahakan?"hajiya Halima tace tana duban inteesar din,"ehh wallahi mummy Inteesaar duk tacanza tayi kyau""Inaga de gizo idanuwanki suke maki,banda haka duk wanda yasan Inteesaar yasan ba haka take ba".dajin kalaman dasuke fitowa bakin Halima tasan da biyu take fadi,wani tunani tayi sannan ta rausayar da kai tana murmushi,zubama Ziyada ragowar abincin Inteesaar tayi"bismillah ga abinci"..cakala abincin  Ziyadar tayi domin akoshe take,hirar duniya sukayi ganin Halima nawurin shiyasa basuyi zancen yaza su bullowa Elmoudan ba,karfe 5:30 dede Ziyada tace"ke banga kina da niyyar dora girki bane"...harararta Inteesaar tayi"anfada miki kullum nakeyi?sena buna nasha iska nakeyi""..kallon  mamaki tabi inteesar dashi"da gaske kike?".."a'a dawasa nake".."toh amma gsky elmoudan nada haquri..."..."se ki sashi rashin haqurin,mara kunyar yarinya kawai"Halima tasoma fada."keko ina kika samo wannan figalalliyar yarinyar mara tarbiyya bare da'a?agabana take fadin wannan maganar dayake ita shafaffiya da mai ce."mikewa Halima tayi ta nuna hanyar waje da fingernta"tashi ki fita!"Jakarta ta dauka tareda mikewa sannan tace"bazan yi musayar yawu dake ba sbd ke mahaifiyar aminiyata ce amma wallahi sekinyi mamakin abinda zai biyo baya"tana kaiwa nan tafice daga gidan,Salati Halima tayi"ni take fada ma wannan maganar baki gurje bakinta ba?"..shiru  Inteesaar tayi domin taji haushin yadda mummyn tayi adressing ziyadar,"ba magana nake miki ba?"nan ma shiru Inteesaar takumayi,"kai kaga shashashar yarinya dan uwaki wa kika ma shiru?".."mummy gsky banji dadin yadda kikayi addressing Ziyada ba".."au lefina ma kika gani?"."a'a nibance ba".."gashi nan kuwa kince "...haka hajiya Halima tachigaba da bambaminta ,inteesar kuwa tayi shiru ranta be soba.Driving Ziyada takeyi ahankali tana taunar chewing gum,Sahad tashiga tasiya foodflasks masu kyau sannan tawuce bristol palace,abinci mai rai da lafiya tayi order suka zuba mata acikin warmers,daga nan office dinsu Elmoudan tawuce straight,yana shirin danno hancin motarshi kan titi ta tsayar dashi,da mamaki yake binta da kallo harta karisao ta bude mirfin kofar tasa cikin dakewar zuciya,"ina yini ta duka har kasa tagaida shi abinda ba'a taba masa ba,"lafiya kalau"yace yana me kara kaima fuskarta duba"you look familiar"."yeah I am Ziyada inteesaars bestfriend "..."yeah haka ne toh ya gida?".."lfy kalau Alhamdulillah hope same?".."yeah same "..."nasan de kafada ne amma you don't really mean it".zaro dara daran idanuwanshi yyi"ban ganeba?"...murmushi tayi tace"koda yake barshi ma"kafada ya buga mata alamar shikenan,sannan yace "zan tafi.".."ina zuwa"tace sannan takoma motarta ta dauko warmers din tadawo kallon mamaki yake jifanta dashi"ga wannan dan inada tabbacin bazaka tarar agida ba"...numfashi ya sauke sannan yace"you're mistaken,dan haka fice min daga nan"...wata dariya tayi"haba yakake magana kamar bakasan cewar ni aminiyar Inteesaar bace matarka?"tachigaba da fadin "na tabbatar da nafika sanin abinda zatayi dawanda bazatayi ba Don haka amshi wannan ka rage zafi"kallon kiyi kadan ya watsa mata sannan ya rufe kofar motarshi yana Allah wadai da masu irin halin Ziyada,.sauri tayi ta ajiye warmers din agaban motar tana tunanin baze iya kin dauka ba,ga mamakinta taga ya takesu da motarshi yyi gaba abinshi zuciyarshi na zarginshi da rashin kyautatawa,Tabbas koba komai atleast she show some care.share tunanin yyi daga ranshi yawuce gida bayan yyi takeaway.Ziyada kuwa kamar ta fasa ihu taji,wani bakin ciki ya ziyarce ta mara fasaltuwa,Duk wanda yasanta ze gane bata cikin hayyacinta,kwafa tayi tace"adingi zuwa rafi..."Driving take tana rafka uban tsaki kamar wata tabbabiya harta karisa gidansu.
*****
Akofar Alhaji Suleiman yyi parking ganin Jidderh nakokarin shigewa gida,tsayar da ita yyi"Hauwa'u"yace cikin muryashi mai tsananin zaqi kamar bata namiji ba,juyowa tayi ahankali tana dubansa cikin faduwar gaba har ya kariso inda taake"hauwa'u "yakuma ambata yana kallon fuskarta,"Naaam"tace itama tasamu kanta da sirantar da muryarta,shiru ne ya biyo baya,banda idanuwa daya rufeta dasu,kallon kasa tayi ta soma wasa da yatsun hannunta,baice mata komai ba har kusan 30seconds,"se anjima"yace sannan yakoma cikin motarshi yana tunanin ya akayi ma yafito?.seda yaga shigarta cikin gidansu sannan shima yashiga nashi gidan,Ya Allah!kwata kwata beyi farin cikin dawowa gidan ba,sannu ahankali yashiga gidan inda ya tarar da Halima tayi crossing leg gamida Shan kunu,cikeda ladabi yace"ina yini mummy kinxo lfy?"..."garas ma kuwa domin da dawata mishkila dabaka ganni azaune ba sannan bansan inda yinin yake ba"...tunda tafara magana yake kallon bakinta.Tabe baki yyi ahankali sannan yakuma fadin"ya mutan gidan?"..."dakana son sanin lafiyarsu ai daka taka kaje".numfashi ya sauke sannan yace "yi haquri"...tareda mikewa yakalli sashen da Inteeesaar take da ko sannu da zuwa bata masa ba"don't walk out of me cox I am not done with you",komawa yyi ya zauna itakuma tachiga ba da fadin "dafarko de 'yata ba jaka bace inason kafihimci wannan,baze yiwu tamaka abinda bata saba yinshi ba agidansu,wallahi kayi kadan,fara daga shara wanke wanke da girki,kafita kasamo mata wanda zasu rinqayi domin bazan laminci amayar min da ya baiwa ba,kadubeta dakyau ahaka ka aureta?"yafadi tana girgiza kai,"dafatan maganata tafarko tashiga kanka,nabiyu baze yiwu ka riqa wulakanta auranku ba,baze yiwu karinqa cin mutuncin aurenku dawasu yan iska awaje ba,don haka ina baka concrete warning da ka kula."numfasawa tayi tachigaba da cewa"dawasu minor things da banida lokacin fada maka,wallahil azim kada kabari nakara zuwa gidan nan sabida wannan maganar "tana gama fadin haka ta mike ta yafa mayafinta tareda saba jaka,"mummy ina kuma zaki?naga yamma tayi bade kt zaki koma ba".."kin san muba matsiyata bane don haka bazan rasa wurin kwana ba,kede Allah ya miki albarka sannan duk sanda kika ga wani abu dabe kwanta miki ba kiyimin waya"ta fadar hakan ne tana fita daga falon"tsaya na rakaki mana"cewar Inteesaar ita tana fita daga gidan,da kallon marasa hankali yabisu yana mamakin wannan lamari,dan tsananin raini da rashin kyautatawa shi zata kai kara duk irin iskancin datake masa?,na auri matsala yace yana me mikewa yahaye sama abinshi,amma kasan zuciyarshi bbu dadi yadda Halima tayi masa cin mutunci.

LABARIN JIDDERH Where stories live. Discover now