BABI NA SHA TAKWAS

1.3K 92 3
                                    

( 22 Jan, 2016  5: 18PM)

🔥 MATA UKU GOBARA 🔥

           Maryam Alkali

BABI NA SHA TAKWAS

Jeren gwanon motoci ne akalla ba akasara ba sun kai ashirin, manya masu tsada, hadaddu sai wutace suke fitarwa masu sha'awa (Double signal) ba kalar motar da babu, sai wadda ba'a rasa ba.

sun karya kwanar layin gidan Mahmud, a dai-dai get suka tsaya kowa na matsa horn, motar amaryace kawai aka budewa get ta shige ciki, sauran kam duk a waje suka yi parking mutanen da ke ciki suka fito.

Dai-dai nan wata bus ta iso sai ihu ta keyi alamar ta kwana biyu, MERMUE NOVELLA HOME GROUP 1&2 ne, suke dirkowa daga cikin motar, wasu kan wasu, na dauke kaina da sauri don karsu ganni, domin naga ana rikicin hada kuddin bus din.

Amarya an shigo da ita cikin gidanta bayan tayi alwala a k'ofar falo, ta shiga da kafar dama tare da addu'a a bakinta, a falo aka zaunar da ita domin kiran yayyenta wato Humaida da Zuhra domin damk'a masu amanarta.

Sai dai ko da 'yan uwanta suka je kiransu kowacce ta rufe k'ofar dakinta GAM da key, suka yi knocking din duniyar nan amma yan gidanku ko tari suka k'iyi a dole sunyi bacci.

Haka aka kwashe Jalila zuwa dakinta, sai kuka take yi harda ciccika, a haka 'yan uwanta da abokan arziki suka yi mata sallama bayan sunyi mata doguwar nasiha, yadda zata kula da mijinta da abokan zamanta.

Jalila tana ganin kowa ya wuce an barta ita kadai kukanta ya tsananta, can taji motsin shigowar ango, hankalinta ya k'ara tashi, sai da yaje d'akunan matansa, shima ba irin knocking dinda baiyi ba, amma suka yi mus kamar matattu, ya gaji da tsayuwa, ya bude frigde yasa masu kazarsu da lemu, ya dauki na amaryarsa ya shige d'akinta.

Da kyar da lallashi da komai Jalila tayi shiru, suka ci kazarsu mai kabeji da yajin daddawa da lemu.

Bayan nan suka yi sallar nafila, suka yi addu'o'in samun zaman lafiya mai d'orewa da zuri'a ta gari.

Ango yaja Amarya saman gado, amma gabansa sai faduwa yake yi, sai cewa yake yi a cikin ransa "ita kuwa wannan ko meye matsalarta Oho?"

Yayi sama da kansa yana rok'on Allah " Allah kasa daga wannan na kawo k'arshen matsalata."
Amarya kam itama ta rude tuni, haka dai abubuwa suka kankama na fitowata waje na basu wuri.

Humaida da zuhra ne lab'e a bangon kofar amarya, ganin basa gane komai ya basu damar lek'awa ta jikin key,  komai ya faru a cikin kunnensu, kuma suna lek'awa ta jikin key.
Bakin ciki ya turnik'esu jin zantukan Mahmud wanda bai masu ba. ai tuni suka fara tsaki suka bar wurin.

Misalin karfe bakwai na safe, Amarya ta fito da kyar ta gane kan gidan, ta fara gyaran falon gidan, bayan ta gama ta shige kitchen ta hada break fast ta jere a dinning, ta koma dakinta ta shirya cikin super koriya mai yarfin golden riga da skirt, tayi kyau sosai, ta kafa dauren nan na zamani, face dinta ma tayi kwalliyar zamani, ta saka saka sark'a da dankunne da awarwaru da rings.amma fa komai take yi cikin k'arfin hali ne, domin ita kad'ai tasan yadda take ji a jikinta.
ta fito amaryarta sak.

K'amshinta ne ya tayar da Mahmud, mamaki ya kasheshi, shida yasan amarya indai virgin ce da safe langab'ewa take yi komai sai an mata, amma banda Jalilarsa, yadda yaga ta tako tana yi masa murmushi tare da tambayarsa har ya tashi, ya gane taji jiki k'arfin hali ne kawai take yi.

Mik'ewa yayi zaune fuskarshi ciki da murmushi, cikin shagwaba tace "na hada maka ruwan wanka a toilet." ta fada tana d'an rausaya eyes, gogan naku tuni ya rude, k'ok'arin hugging dinta yayi ta kauce, a dole ya shige toilet zuwa wanka.

Ko da ya shiga ruwan wanka wani irin k'amshi suke yi ga toilet din shima yana bada nasa kalar k'amshi, Mahmud ba abinda yake yi sai godiya ga Allah, yana fatar abu ya dore.

Yana fitowa ya tarar da kayansa a gado ta fitar masa, amma tabar dakin, murmushi dai har yanzu shine a face dinsa.
Ya shirya tsaf cikin three quarter white da black shirt, yayi kyau sosai sai k'amshi yake badawa ya fita zuwa falo.

Mamaki ya k'arayi break fast dinda yaga ta hada, dinning ciki mak'il, yaje ya zauna tazo tayi serving dinsa, taje ta kwankwasa su Humy kowacce ta fada mata tazo suyi break.

Sannan ta dawo ta zauna a dinning tana yiwa mahmoud yar hira, irin ta dariya din nan, shikuwa sai kwasar dariya yake yi yana loda abinci a tunbensa.

Su hajiyoyi sun fito, suna ya tsina, suka zo suka zauna, Jalila ta mik'e ta gaidasu, suka k'arba a dak'ile, ta tambayesu me suke so ta zuba masu, bayan ta zayyano abinda ta girka, cikin wulak'antawa suka ci tabari su zuba abinda suke so, ai kayan abincin na mijinsu ne, don haka suna da iko dasu.

Bata yi mamaki ba, akan abinda suka yi domin halinsu ba wanda bata sani ba, shi dai Mahmud basu ce masa ba, bai ce masu ba, ya gama lodawa ya tashi, Jalila ma ta mik'e tabi bayansa.

A falo suka zube Mahmud sai kallonta yake yi yana wani kashe mata ido, fuskarsa murmushi yak'i b'acewa, nan Ahmad ya kirasa a waya yana masa tsiya, yace zai zo anjima suje gaida baffan Jalila, suka yi sallama ya kashe wayarsa.

Ya kalle jalila data dan kishingida saboda ta kasa jin dadin zaman, yace " my zumah muje ki zaga kiga fasalin gidan, kinji wannan yayanki yace zamu fita anjima gaisuwar surikai."
Tsaki yayi "don ni ya kwafsa min, yau get banyi niyyar lek'awa ba."

Yar dariya tayi cike da salon yaudara, ta mik'e tare da cewa "muje."
Yabi bayanta suka fita yana nuna mata ko'ina na gidan.
Su kuwa su Humaida ture abincinsu suka yi suma suka mik'e tare da shigewa d'akin Humaida.

Bayan sun dawo daga zagaya gida, suka zube a falo, jalila tana mayar da numfashi, domin fa a wahale take, k'arfin hali kawai take yi, shima Mahmud yana kule da ita, sai sannu yake zuba mata, ya dauko ruwa a frigde ya bata.

Misalin sha biyu na rana zai fita, jalila ta biyosa har k'ofar falo tana masa rakiya, tace " Allah ya tsare Mine, a dawo lafiya." cikin jin dadi Mahmud ya k'arba har yana rafka tintibe wurin waiwayenta.

A daki ta zube saman gado, ta fada tinanin  abinda ya faru jiya tsakaninta da Mahmud ne yake dawo mata, kai tasha albarka jiya ba sunan da ba'a kirata dashi ba.
My zumah
My tea cup
My fried rice
My stew
My jallop rice
Kai ita kam wasu kunya ma suka bata, tayi yar dariya ta jin dadi, ashe haka aure yake, kai Allah dai ya basu zaman lafiya.

Dai-Dai nan taga su Humaida a gabanta sai huci suke yi, cikin daga murya Humaida tace "Munafukar banza munafukar wofi, yau k'aryarki ya k'are ai."

Zuhra ta cafe "ni abinda ya bani mamaki irin yadda ya Mahmud keyi mata a daren jiya, yau sai kin yabawa aya zak'inta."
Ba bata lokaci suka ciro SUPER GLUE daga jikinsu, "inda ya shiga har ya rude, nan zamu toshe yau." cewar Humaida.

Cikin zare ido jalila ta mik'e zata gudu jikinta ko'ina rawa yake yi, k'afa suka sa suka tadeta, ta fadi kasan dakin, Zuhra ta hayeta ta dafe, Humaida na k'ok'arin bude kafafuwanta.

               Mrs Jabo.

MATA UKU GOBARAWhere stories live. Discover now