BABI NA UKU

1.6K 116 4
                                    

🔥MATA UKU GOBARA🔥
                       BY
               MAMU💕

BABI NA UKU.

***

Misalin goma na safiyar litinin, Mahmoud ya fito dakinsa cikin shirinsa na fita kasuwa, hula ce kube rike a hannunsa yana karyawa, har dakinta ya leka yana kiranta amma shiru, ya leka bayinta babu ta, sai wari ke tashi a toilet din alamar anyi kashi ba'ayi flushing ba, ya dawo falo nan ma bata, har kitchen ya shiga babu alamarta, kitchen din sai kudaje kebbin plates da ba'a wanke ba.
Gaba daya gidan ko'ina ya karade babuta babu alamarta.

Wayarsa ya ciro ya kira layinta  amma wayar a kashe, fitowa yayi harabar gidan yana kwalawa mai gadi kira, Baba Abu! Baba Abu!! Baba abu!!! A guje ya karasu wurinsa, mai gadi yace, "An tashi lafiya?? Mahmoud bai wani tsayawa karba gaisuwar ba, yace "ko kaga madam ta fita a gidan nan?"
Mai gadi yace "Eh na ganta ranka ya dade ta fice da sassafe nan." kai kawai ya gyada yace zaka iya komawa bakin aikinka."
" A fito lafiya yallabai."

Kai tsaye motarshi ya shige yayi mata key, ko slow bai tsaya tayi ba ya fisgeta yabar gidan, mai gadi yana "Allah ya tsare Alhaji."

Tunaninsa daya toh ina Humaida ta tafi??? Shin tana nufin tayi yaji ne yanzu? Kuma fa cikin sati na biyu suke da aure, ko meye ai bai kamata a fara jin kansu yanzu ba, yana tsakanin tuki ya rasa ina zai dosa. Karar wayarsa ne ya katse masa tinani, dubawar da zaiyi yaga Anty din Humaida ce tayi kiransa, da sauri yayi parking gefen hanya ya dau wayar.
"Assalamu Alaikum" ya fada, a dayan gefen aka karba masa, cikin girmamawa ya gayyar da Auntyn, ta karba masa a gaugace, tare da cewa "Dan Allah Mahmoud idan baka komai kazo yanxu domin ga wannan shashar tazo tun dazu, ta sakamu a gaba da kuka, yace gaya nan zuwa yanzu."
key ya kara yiwa motarsa ya bata wuta sai Runjin sambo, unguwarsu Humaida.

  ************************
Da sallamarsa aka shigo dashi a cikin falon gidan, kansa a kasa cikin jin nauyi da kunyar mutanen falon ya gayar dasu, suka amsa masa fuska a sake, ya neme wuri ya zauna a kasa da kyar ya dawo a kujera bayan sun matsa masa.

Abban Humaida ne yake tambayar Mahmoud meke faruwa tsakaninsa da iyalinsa alhalin ko 2 weeks basu cika ba da aure???

Mahmoud yayi shiru, shi dai a iya saninsa shine ma ya kamata ya kawo kararta ba ita ba, can ya nisa yace, "Abba ka tambayeta tunda dai itace ta kawo karana, nifa ban ma san zuwanta ba, sai Yanzu na fito zan fita kasuwa na duba ko'ina ban ganta a gidan ba."

Kallon kowa a falon ya kuma ga Humaida, Abba yace "me mijinki yayi maki kika kwaso kafa kika zo bada izninsa ba?"
jiki a sanyaye ta fara "Abba shine fa ya canjamin." toh muna jin ki wani irin canji kenan?

"Baya cin abincina, baya zama a gida, harta kai ta kawo kyankyamina yake yi. anan ta fashe da wani irin kuka mai cin rai.

kallonsu ya dawo ga Mahmoud, jiki a sanyaye Abba yace "haka ne
Mahmoud?"

Kunya duk ta rufe Mahmoud, yace "Abba ai ita bata fadi abinda take yi har na canja mata ba."

"Toh muna jinka Mahmoud."
cewar Anty, step Mother din Humaida, ita dai Ummar Hummaida tunda aka fara bata ce komai ba.

Mahmoud yace "Dan Allah Alhaji idan babu damuwa kuzo muje kuga abinda take yi da idanuwanku, kazantar da Humaida keyi ban taba tinanin zata yi ba."

Cikin zare ido suka ce  "kazanta fa Mahmoud?" Anty har da dafe gaba, idan aka yi la'akari yadda Humaida take yar gayu a baya, zai yi wuya yanxu mutum ya yadda cewar tana yin kazanta a gidan aurenta.

Mamaki ne karara a fuskarsu Alhaji, ya yiwa Anty umurni taje ita da Humaida, driver ya kaisu. Ko meye a gidan idan ta dawo ta gaya masu.

Mahmoud yayi masu godiya hade da sallama ya bar falon. Compound din gidan ya tsaya yana jiransu Humaida, su gama kammala kimtsawa su fito.

A cikin gida kowa Abba ya rufe Humaida da fada, idan aka dawo aka gaya masa cewar tana yin kazantar da gaske sai yayi matukar sa6a mata.
Ita dai kuka kawai take yi, Anty tace ya bari dai ta dawo, amma ita kam tana mamaki wai Humaida da kazanta, haka ma Abba yace na san Mahmoud ba zai yi mata karya ba, fitowa suka yi suka zo suka samu Mahmoud a compound, driver ya jasu shi kuma yabi bayansu a motarsa.

  
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.

MATA UKU GOBARAWhere stories live. Discover now