BABI NA SHA SHIDA

1.2K 88 3
                                    

🔥 MATA UKU GOBARA 🔥
                      By
                  Mamu

BABI NA SHA SHIDA

****
                  

Kallon juna suke yi na k'urilla kamar yau suka fara haduwa, a lokaci guda suka fashe da kuka kamar hadin baki, sai da suka yi mai isarsu, ba mai lallashin daya.
sannan suka ja jiki kowacce ta shige dakinta da kyar.

Bayan kamar minti talatin Zuhra rarrafo ta dawo falo, akwatinan ta shiga budewa tana kallon kayan da k'yar kamar wadda aka yiwa dole, jin motsinta ya fito da Humaida, itama ta bude nata tana kallo.

Can Zuhra ta sauke ajiyar zuciya, tace " Ni kam ba zan daura wadannan zannuwa ba, duk wulakancin da Mahmud yayi min, ya nuna min k'arshena."
Humaida ta chafe "kinsan me? kawo kunnenki kiji."

Ta rada mata wasu kalamai a kunne, fuskarta ta dau annuri, suka ta6e tare da dariya.

A wurin Mahmud yana fita gidansa, ya wuce family meeting dinsu, bayan ya biya ya dauki Hajiyarsa, a mota yayi mata bayanin komai, tace yanzu ai idan muka karasa wurin meeting za'ayi zancen komai.

Sai da akayi dauki ba dadi kafin families su yarda ayiwa yarsu kishiya, acewarsu duka-duka yaushe ne auren nasa da zuhra, ba'ayi shekara ba yanzu zai zo ya k'ara wani, can dai wani uncle din Mahmud yace "ka fada mana gaskiya Mahmud ko dai haihuwa kake so, shine kake ta wannan aure-auren?" Kowa falon ya dauka sai dai haka kam.

"Toh ai indai haihuwa ce Allah ke badawa Mahmud, kayi hakuri ka jira lokaci mana." Cewar wani Baffansa.

Cikin jin kunya Mahmud ya dukar da kansa kasa yace " ba haka bane, ni dai gaskiya matana duk suna da matsala, shine nake son k'ari ko zan dace.

K'anin kakansa yace " duk tsiyar aure-aurenka idan ka cika hudun ai ka tsaya nan."

Nan take falon ya dauke da dariya, haka dai da kyar suka amince bayan gwoggo tayi dogon sharhi, gobe za'aje sa rana, ya sanar da yarinya ta fadawa gidansu.
Da haka taron ya watse, Mahmoud murna fal ransa.

Direct gidansu Jalila ya wuce, ya samu Ahmad yayi masa bayani, daga baya gimbiyar ta fito sanye da atamfa take yau, dark purple da milk, dinkin gown "A" shape, tayi rolling da veil milk, hill ne  a k'afarta purple, tayi kyau sosai abinka da farar mace cikin purple colour, gogan naku sai smiling ake watsawa, ta gaidasi cikin siririyar murya tana wani nokewa alamar kunya, ga wani murmushi da take jefa masa duk ya rikice.

Bai San lokacin da bakinsa ya subuce yace " ranki ya dadi sannu da fitowa." da rawar jiki.
Dariya tayi kadan tana lumshe idanu,  Mahmud ya neme inda yake ya manta, can yayi karfin hali yace " ledar dana baki jiya fa waya ce a ciki, na kira naji baki hada ba, me yasa?"

"Lah!" Ta fada cikin shagwaba "ban duba bane, bari na dauko yanzu." daga masa hannu tayi alamar ya jira, yabi yatsunta da kallo sun sha rani jajir dasu.

Bakinsa yau kam har ya gaji da wangala, sai gata ta dawo tana takawa d'ai-d'ai kamar tana tsoron kada takalmin su yadata, ta mik'a masa. " ka hadamin toh Baby."
Sai da ya k'ara kallonta saboda sunan data kirashi, ta bata rai kamar ba ita ta fada ba.

Murmushi yayi ya fara hada wayar, ya hada mata komai harda watsapps, ya bata, haka dai suka yi ta hirarsu ya fada mata komai ake ciki, har da kukanta na shagwaba wai yayi wuri nan da 2weeks ta zama matar aure.

Mahmud dariya yake mata, yana k'ara zugata, "gaki yar karamar yarinya kuwa."
Ai kuwa ta fashe da kuka sai cikin gida.
Haka yabar gidan ya wuce kasuwa ransa kal.

Wayoyinsu kawai suka zare cikin akwatinansu irin na Jalila, Mahmud akwai adalci, wayar daya siyawa Jalila shine ya siya masu, sun hada watsapps dinsu suma wai su samu k'awaye su basu shawara yadda zasu ci uban Mahmud, sunga yanzu watsapps yana damawa son ransa. 

Suna jin shigowar Mahmud, ya bude falon ya shigo, suna dakunnansu, ya shige nasa, shigarsa bada jimawa ba, ya fara jin k'auri, da gudu ya fito yayi wajen falo inda hayaki ke fitowa, turus yayi ganin aikin da matansa suke yi.......

          Mrs Jabo.

MATA UKU GOBARAWhere stories live. Discover now