BABI NA SHA BAKWAI

1.2K 96 2
                                    

🔥 MATA UKU GOBARA 🔥
                     By
                  Mamu
                
BABI NA SHA BAKWAI.

Ganin aikin da suke yi yayi matukar girgizashi, kayan daya kashe kuddi ya kawo masu, domin kwatanta adalci, sune suka zubawa fetur suka k'ona, sai ci suke yi da wuta bal-bal, ransa yayi matuk'ar baci, amma ya daure, ya danne zuciyarsa a matsayinsa na d'a namiji wanda yafi mata hangen nesa, kuma idan yace kullum yayi ta jibgarsu sun zama jakuna kenan.

Tunda dai su kishi ke cin zuciyarsu bal-bal, ya juya yayi shigewarsa ciki, ganin ya koma cikin falo suka sa ihun murna tare da rungume juna, bukatarsu ta biya, tunda sun bata masa rai.

Humaida taja zuhra "zo mu tafi ai burinmu ya cika, tunda mun k'untata masa, yadda shima ya k'untata mana."
      "Anty Humaida yanzu ya fara ganin b'acin rai, damu yake yi."
Cikin gidan suka shige cike da murna.

Baba Abu mai gadi da yake kallon duk abinda yake faruwa, ya girgiza kai yace " Allah ka yiwa wannan bawa naka sauyi da mace ta gari, yanzu wadannan kayan da suka k'ona mai makon su kyautar, a'a sai su k'ona alhalin wasu na nema."

***
Yau dai Mahmud ya matso abinka da d'an adam, wanda ba icce ba, rabonsa da matansa har ya manta, yayi wanka yasha turare yayi dakin uwar gida sarauta mata, har ta fara bacci taji shigowarsa, tak'i motsi sai da ya hau gadonta, ta mik'e da sauri, tace "karka soma Mahmud, ka jira matarka nan da 2 weeks."

Ya kwantar da murya "haba Humynah ai kema matata ce..."
Ta turesa, tare da fadin "Humaida k'azama ce fa."

Mahmud ya kwantar da murya yana lallashinta, amma fafur Humaida tak'i, sai yab'a masa bak'ak'en maganganu take yi, har ransa ya baci.

Abinka da zuciya bata da k'ashi, tuni shima ya fara mayar mata, "ance maki k'azama, k'arya nayi?"
Wata dariya ta shek'e da ita ganin ransa ya baci, " ki kalli kanki a madubi mana, kullum daurin k'irji, hammata gashi tunkus, hakama gabanki gashi ne dam sai tsami..."

Ya dan rage murya kadan,
  "kinga kuwa mai irin halin nan dole a kirata k'azama, idan kinyi zuciya ki gyara, ai da ba haka kike ba."
Cikin kulewa tace, "anji din, kuma ba za'a gyara ba, idan jikinka ne sai naji."

Mahmud ya fita dakin ransa a bace.
Hanyar dakinsa yayi, sai can yace bari naje dakin zuhra na gwadata ko zata amince, da addu'a abakinsa ya shiga dakin. Tayi baccinta hani'an da kayan bacci irin na gidan iyaye, masu kauri.
     Ya hau gadonta ya kwanta, jin motsin mutum yasa ta farka, tana ganinsa ta fara harararsa domin ta san kan zancen.
Goganku ya kwantar da murya har da bata hakuri, ai kuwa ta runtse ido tayi masa k'wal.
Yayi mamaki matuk'a domin gwanda Humaida da ita.

Haka ya janyo tsumman jikinsa yayi dakinsa, kitchen ya dawo ya rasa me zai dauka yasha yaji sanyi, can ya tuna da lime ya hada ruwan ya zauna falo ya fara banka, ransa matuk'ar bace, da matansa amma abu daya ya gagaresa.

                    ****
Dare da rana tare da wuni nata juyawa, kwanaki nata tafiya, lokaci yana wucewa, a cikin haka ne lamurra nata juyawa, al'amarin gidan Mahmud sai Allah ya kyauta, domin haushi kam yana kwasarshi, inda shi kuma ya bawa babu ajiyar matansa.

Acikin haka har ansa rana, an mik'a kayan akwati gidansu amaryarsa.
Har ta kai ta kawo yau ne za'ayi walimar Jalila tare da angonta Mahmud inda aka daura aure dazu bayan sallar jumu'a.

Za'a yi walima k'arfe hudu na yamma, akai amarya gidanta k'arfe takwas na dare.
Amarya tayi kwalliyarta cikin brown and golden material, dinkin gown fitted, kasa ta bude sosai da step-step, tasha alkyabba ta net brown, shoes dinta nd purse golden, fuskar nan ta sha make-up na zamani, tayi kyau har ta gaji.

Motoci sun fara daukar mutane zuwa giginya hotel inda can aka dauki hall domin gabatar da lectures akan zamantakewar aure.

Sai da aka kwashe kowa, motar Amaryar itace last, tare da k'awayinta, amarya tana shiga hall kallo ya dawo gareta irin kyaun da tayi Mashaa Allah.

Taje wurinta ta zauna, ba bata lokaci aka fara lecture, wanda malama ta gabatar, malamar da akeji da ita a garin sokoto.

Lecture ta Shiga jikin mutane sosai, lura yadda malamar ta watse formula, wasu harda kwalla ciki har da amarya, jikinta yayi lakwas.

An kammala walima aka fara rabon take away da suviniours, bansan ya akayi ba, sai ga yan MERMUE HOME OF NOVELLA GROUP bansan wanda ya gayyacesu ba, suna kokawar take away, ba kamar Beeba da ummin rabajau da Mum Sultan sai kokawa suke yi suna karbama saura.
Haka dai taro ya watse lafiya, bayan kowa yaci ya sha.

Misalin takwas da rabi motocin daukar Amarya sunzo, aka fito da ita da kyar daga jikin yayarta, Anty Aisha, sai kuka suke yi, Amarya tasha kyau cikin atamfarta super orange and lemon green, tasha gyale lemon colour, haka aka sata mota tare da rakiyar ilahirin yan uwa da abokan arziki, sai gidanta.

   

            Mrs jabo

MATA UKU GOBARANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ