BABI NA HUDU

1.4K 76 1
                                    

🔥MATA UKU GOBARA🔥
                      BY
Maryam Alkali { MAMU}

BABI NA HUDU.

**

Tafiya suke yi a hankali har suka Karaso gidan, parking suka yi duk suka fito waje, Mahmoud ya bude kofar falon yace da Anty "Bismillah."
kanta ta kutsa a cikin falo tayi turus tana kare masa kallo, ko'ina yayi kaca-kaca, ta juyu tana yiwa Humaida kallon tuhuma, tayi saurin sadda kanta kasa ganin irin kallon da Anty ke mata.

kofar kitchen Anty ta bude wasu kudaje suka karba mata sallama, da yake Humaida ta bar window din kitchen a bude wannan dalilin kudajen suka samu wurin party, fitowa tayi daga kitchen taje dakinta.
Tashin hankali karara bayyane a fuskarta, ita kam tana mamaki yadda Humaida ta mayar da kanta kazama, ko don ta saba a gida bata aikin komai, masu aiki keyi, iyakacinta tayi kwalliyarta kullum.

Mahmoud yana ganin tayi hanyar bedroom ya karasa wurinta, durkusawa yayi ya mata sallama zai fita kasuwa.
Anty tayi masa adawo lafiya muryarta cikin yanayin damuwa, yana fita gidan ta fisgu Humaida, turata tayi cikin dakin "duba yadda gadonki yake Humaida." ke baki san kullum ki gyara gadonki akalla sau 2 a rana ba, dubi yadda bedsheet din duk ya zame, wai wannan doyi daga ina yake fitowa?" cewar Anty.
Humaida tayi rau-rau da ido cikin murya kasa-kasa tace toilet dina ne.

Dafe kirji Anty tayi, ba dai har da wanke toilet din bakya yi ba?, zaki kuwa janyo ma kanki infection."
"ina wankewa Anty." kina wankewa yake yin wannan zarnin, lekawa tayi toilet din warin kashi da fitsari ba'a magana, ta juyu ga Humaida.
Baki san toilet mai tile yafi fitar da wari ba, akalla kullum sau daya a wuni ki wanke toilet dinki tas ki saka tirare, zai ta fitar da kamshi mai dadi.

Dan Allah ni fito na tayaki ki gyara gidan, kuma komai a kunnen Alhaji, shasha wadda bata san ciwon kanta ba.

Haka Anty tayi ta gayawa Humaida dabarun gyaran gida da tsafta, tare da bata tsoron cewa mijinta zai iya karo aure ta daina ganin basu jima da aure ba, domin shi aure anayinsa domin samun kwanciyar hankali.

Amma idan mutum bai samu ba to lallai namiji zai iya karawa, ai tuni Humaida ta rude taji zancen kishiya, cewa take yi to Anty ya samu min mai aiki, kinga zata taya ni kula da gidan, tsaye Anty tayi tana kallonta.
Ke humaida kazama ce, ko da kuwa kina da mai aiki, Yanzu ina kwalliyar da kike cancadawa a baya? ai kin daina Yanzu ko kuwa mai aikin ce zata rika maki wanka da kwalliya??

Ke dai idan zaki gyara ki gyara. Idan kuwa so kawai kike kiji an shigo da wata gidan nan, mu dai ba ruwanmu.

Yau namiji ko kina masa komai zai iya karo wata matar, ballantana ke da komai ma baki tsare masa ba, wlh Humaida ki shiga hankalinki, ina laifin da safe da kun gama sallar asuba kiyi addu'o'inki kije kitchen dinki ki gyara, falo, bedrooms, kizo kiyi ma angonki breakfast kije ki cancara adonki, ki tasheshi shima yayi wanka yazo yayi break ya fita, a lokacin zaki samu time kiyi baccinki enough.

Ki tashi ki dora girkinki kan ya dawo kin kammala komai, gida yana tashin kamshi, amma ke kinzo kin zama wata kucaka kamar ba Humaidata ba, mai tsananin kwalliya da kamshi.

Haka dai anty ta taya Humaida gyara gidan, tana yi mata nasiha akan zaman aure, kuma ta jaddada mata ba dole sai mace tana da mai aiki zata yi tsafta ba, idan dai ta tsara aikinta bata biyewa son jiki tas zata rika gyaran gidanta kuma ba tare da tasha wuya ba, kan ta tafi sai da ta idar da tsife kitson kanta, ta wanke gashin da shampoo da conditioner, tayi wanka tayi kwalliyarta cas irin ta baya, fuskar nan ta fito radau yau, taji foundation irin Wanda ta kwana biyu bata ji ba.

Sallama Anty tayi mata, Humaida har mota ta rakata tare da godiya sannan ta juya cikin gidanta.

Mahmoud yau ya dawo gidan komai tsaf har aransa yaji dadi, yadda yaga komai tsaf, sai kallon falon yake yi amma bata cikinsa, direct bedroom dinta yayi, ya sameta tana sana'ar tata wato bacci, da kyar ya tasheta ta mike tana zumbure baki, wai ya tayar da ita daga bacci alhalin yau tasha aiki, binta kawai yayi da kallo daga bisani yayi kwafa ya bar dakin.

Dakinsa ya shige ya watsa ruwa yayi alwala ya fito, jallabiyarsa ya zira fara kal ya fito zuwa massalaci domin yin sallar magrib, bai dawo ba sai after isha, ya shigo falon da sallama tana nan zaune tana kallo da remote a hannunta, "lah Honey har anyi sallar isha'i?" eh yace mata, "ki tashi kije kiyi idan bakiyi ba, tace toh bara akarasa wannan.
Dan karamin tsaki yaja, yace wannan ba zai kaiki ko'ina ba kedai kullum kallon zee TV dramers din banza, ba zasu amfaneki ba duniya da lahira.

Ni dai bani abincina yunwa nake ji."
Ido ta zaro, haba Honey ba kaga wahalar dana sha ba, gyaran gidan nan ko'ina jikina ciwo yake yi, ni dai kawai muje "prince restaurant" muci abincinmu mu dawo."

Wani kulolon bakin ciki ya turneki Mahmoud, ba abinda ya tsana irin cin abincin kasuwa, ganin ya bata rai tace "toh ko muje Sa'a mai Sa'a?"
banza yayi mata ya wuce dinning ya hada tea dinsa yasha ya shige dakinsa, tare da sanya key yayi kwanciyarshi.

   
***

Haka rayuwarsu ya kasance har tsawon wata biyar da aure, kazantar Humaida da son jiki sai abinda ya karu, kwata kwata shima Mahmoud yana nema ya zama kazamin, gidansu Mahmoud duk sun gane Humaida kazama ce.
Kuma gidansu anyi-anyi da ita ta daina taki, sun kawo na gani sun dora mata.

Yau Humaida tana zaune a falonta a kasa, saman centre carpet dinta tayi rashe-rashe tana shan mangaro, kudaje sai binta suke, da yake lokacin mangaro ne yanzu, ya nuna ga ruwa.
Ruwan mangaro yana ta tarara a hannun Humaida, har sun kawo mata ijiyar hannu, shan abunta take yi hankali kwance ruwan na dirara a centre carpet dinta, daga ita sai daurin kirji wai ita a dole zafi ake yi, hammatarta tanata yoyon zufa ga gashi cunkus da ita, duk fa wannan bidirin da ake yi Mahmoud yana kwance  a kujera baya jin dadi, shine yau bai fita kasuwa ba.

Remote a hannunsa yana kallon news a Aljezeera, sallama aka rafka a kofar falon, shine ma ya karba sallamar don bakin Humaida ciki yake da mangwaronta, kodagun gaba daya ta tura a baki, wadda Mahmoud yaga ta shigo falon sai da gabansa ya fadi.

Gwoggonsa ce, kauna ce a wurin mahaifinsa marigayi mai rasuwa, uwa daya uba daya. Sam bata daukar wargi kuma bata shiri da kazami.

Mace ce mai matukar tsafta da kyankyami, da sauri Mahmoud ya mike yana yi mata sannu da zuwa, turus tayi ganin Humaida da iren kazantar da take yi.

Ta nunata, "Wannan fa Mahmoud???"
Yana sosa keya yace "gwoggo Humaida ce, baki ganeta ba?
Zauna mana yace da ita."

Ita kuwa humaida sai yanzu ta cire kodagon mangarun a cikin bakinta, ta mike tana gyara daurin kirjinta, sannu gwoggo kice ke tafe yanzu cikin zafin nan."

Gwoggo binta kawai take yi da kallo, "tabdi!" ta fada a ranta.
Mahmoud ya kara maimaitawa "ki zauna
mana gwoggo" ta karewa falon kallo tsaf, tace "Mahmoud banga wurin zama a falon nan ba, idan akwai wurin da yafi nan dan kimtsuwa kai ni."

Ta nuna Humaida,  "please kije ki kimtsa kanki ki zo ki samemu."

kada kai kawai Humaida tayi, ta juya ta shige dakinta.
"Itafa ta fara kuluwa da matar nan, bata son cin fuska.

Mahmoud kai gwoggo yayi dakinsa ta zauna a resting chair dake dakin.
Tace Mahmoud dama ashe kucaka ka auro? Toh ba zata sabu ba, bindiga a ruwa. aure zaka kara!"

" Aure?" Mahmoud ya tambaya kwarai kuwa bari matarka tazo, dai-dai nan Humaida ta shigo, hijab kawai ta zuba saman daurin kirjinta, ta neme guri a gefen gado ta zauna tana cika tana batsewa, ita a dole an wulakantata.

Gwoggo tace Humaida kalloni nan, Mahmoud aure zai kara domin ba zaki kashe mana d'a ba, muna ji muna gani, wannan kazantar har ina? ai sai ki bashi kulara yasha ciwon ciki ya aikasa lahira. Ki bude kunnuwanki da kyau, na yanke shawara yanzun nan zamu hadashi aure da yar uwarsa Zuhra, yarinya wadda ta iya tsaftace gida kai da kula da kowacce bukatarsa.
Humaida tuni ta kidime kishiya? Wayyo hannu ta dora a ka ta zunduma ihu, tuni ta fice dakin.

Dakinta ta fada tana kuka, birgima ta fara saman gadonta har ta fado kasa.

Gwoggo mikewa tayi tana karkade zaninta, tace kaga tafiyata, yanzu zanje can gidanku na same Haj. Talatu mu yanke magana.

Shi dai Mahmud rike kansa yayi da ya ji ya fara juya masa, baya yayi ya fada sama gadonsa yana mayar da numfarfashi.

®NAGARTA WWRITERS ASSOCIATION.

MATA UKU GOBARAWhere stories live. Discover now