YADDA KADDARA TA SO 26

37 1 0
                                    

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*BABI NA HAMSIN DA BIYAR (55)*

*Alaro city Hospital*
*12:30am*
Maryam ce zaune a kan kujerar dake kusa da gadon marasa lafiya. Ɗazu bayan sun kawo Eshaan asibiti, likitoci suka shiga duba shi.
Yayin da itama aka shiga dubatan, amma hankalinta na kan Eshaan ɗin, shi yasa bayan an gama mata tretment ta bazama ta fito ta tsaya tare da Baban Ilham.
Suna wurin har likitocin suka fito, suka sanar musu cewa doguwar suma ya shiga, amma su sun duba basu ga abinda ya janyo masa doguwar sumar ba.
Sai da Baban Ilham ya tambayeta abinda ya faru da su, amma bata ba shi amsa ba, dan a ganin ta babu wanda zai yarda da abinda zata faɗa.
Shima kuma be ƙara tambayar tata ba ya barta, abinci ma da Maman Ilham ta kawo musu bata ci ba, kuma rabonta da abinci tun daren shekaran jiya, amma bata jin yunwa, batajin wani abu me kama da ita.
Babu abinda ke gabanta sai ganin tashin Tafida, ya kalleta da shuɗayen idanuwasa ko kuma ja idan ya rikiɗe, ya kirata da 'Miriam' ko 'Daaso' ko yace mata 'Wifey'. Amma sam hakan ya gagara, gashi kwance a gabanta tana ganinsa, kamar me bacci, kamar idan ta kira sunansa ze amsa.
A hankali ta kwantar da kanta a kafaɗarsa, sannan ta ƙara riƙe hannunta dake cikin nata.
“Kai jarumi ne, jarumin da ya tsaya a gaban sheɗanu, ya fuskance su, ya yi yaƙi da tsoransa har ya yi galaba a kansu, me yasa yanzu ma bazaka yi yaƙi da wannan tsoron ba?”
Ta tambaya tana ɗago da kanta, ta kalli fuskarsa ta cikin hasken dake ɗakin.
“Me yasa ba zaka yaƙi abinda ya hanaka tashi ba ?”
Muryarta ta kuma amsawa a cikin dubun daren, da kuma shurun ɗakin.
Ƙara kwantar da kanfa ta yi a kafaɗarsa, tana karanto dum addu'ar da Allah yasa ta gifto a ranta.
Kamar da ga sama ta ji motsawar yatsunsa cikin nata, da sauri ta ɗago da kanta tana kallon fuskarsa, hannun nasa ya ƙara motsawa. Bakin Maryam ya tale da dariya, tana ci gaba a kallonsa.
“Da kyau, nasan zaka iya, Allah zai temakeka...”
Bata ko rufe bakinta ba idonsa ya motsa, kafin a hankali ya shiga buɗe shi, ya sauƙe su tar a kan Maryam.
Ƙoƙarin miƙewa zaune ta ga yana yi, dan haka ta shiga ƙoƙarin taya shi zaman, har ta samu ya jingina da jikin gadon, se jera masa sannu take, yayin da shi kuma ya ci gaba da kallonta, yana ganin yanda take ta fara'a. Zama ta yi a gefen gadon tana kallonsa fuskarta ɗauke da murmushi.
“Kaga ko...”
Hannunta da ya ja ta faɗo jikinsa yasa ta yi shiru, se kawai ta kwantar da kanta a kafaɗarsa tana kewaye shi da hannayenta.
“Allah ya bamu iko Daaso, Allah ya temaka mana”
Ƙara matse hannayenta ta yi tana murmushi. Kafin ya sake ta yana kallon fuskarta, zuwa yanxu ta fara hawaye, dan haka ya motsa hannunsa na dama a setin bedside drawer yana so tisssu yasauƙa a hannsa,amma ko motsawa tissuen be yi ba.
Ya juyo ya kalleta yayin da ita kuma take dariya, hannayenta ta saka ta tallafi fuskarsa.
“Komi ya ƙare Eshaan, babu abinda ya rage, sharrinsu ya bisu, babu baƙin ruhi babu jan ido, babu fiƙa, babu gurnani haka kuma babu super natural, yanzu kai ne, asalinka, gangar jikinka, ka sarrafata yanda kakeso”
Ƙara rungumeta ya yi a jikinsa yana furta.
“Alhamdulillah, Allah na gode maka”.
Ka fin Maryam ta ɗago da kanta tana kallon fuskarsa, still tana kwance a jikinsa, shima sai ya sunkuyo da kansa ya kara fuskarsa kan tata.
A hankali Maryam ta lumshe idonta sannan tabuɗe su cikin nasa.
“Miriam!, I love you to the moon and back....”
A hankali muryarsa ta faɗi, kuma leb'ensa kan na Maryam, kafin Maryam da kanta ta haɗesu wuri guda.....
*Peacock theater, 777 Chick Hearn CT, Los Angless*
Babban ɗakin taron cike yake fal da shaharrarun mawaƙa, makaɗa, 'yan fim da masu bada umarni, duk wani me ruwa da tsaki na harkar entaitament to ya hallara. Sakamakon taron karammawa da ake na Grammy Awards.
Daga kan stage kuma me gabatarwa ne ke jawabi cikin harshen turanci kamar haka.
“......Kamar yanda kowa ya sani, yau ne ake raba lambar yabo ga zaƙaƙuran da suka dace da samun wannan kyauta, a jiya aka gabatar da Grammy award talent cast, a yau kuma zamu karrama waɗanda suka yi nasarar cin wannan karammawa ta Grammg Awards.
Zan kira babban zaƙaƙuri, fasihin mawaƙin da waƙarsa ke zagaya faɗin duniya baki ɗaya, haziƙin da ya lashe lambobin yabo masu dama, irin su First african Grammy nominated artist, highest dubut on billboard hot hundred for an african artist, the accumulator of more than 7 million views on tiktok, waƙarsa ta CONTROL itace on top 10 biggest song globally on Spotify, haka kuma vedion waƙar tasa ta Control ta samu makallata sama da mutum million 57 a cikin wata ɗaya kacal, idan har nace zan ci gaba da lisaffo nasarorin da wannan waƙa da mawaƙinta suka samu zamu cinye lokacin shirin ba tare da na gama ba, leddies and gentlmen wannan nawaƙi ba kowa ba ne faceeeee. Uchenna Haris Franklin!”
A sanda ya ambato suna gaba ɗaya hole ɗin aka saka tafi, kowa dube-dube yake dan ganin ta inda wannan ɗan baiwa ze fito, da ga seat ɗin gaba ya miƙe yana murmushi.
Sanye yake cikin baƙar suit, haka ya shiga taku har zuwa kan stage ɗin, sai da suka gaisa da wanda ze gabatar masa da award ɗin, sannan ya damƙa masa. A lokacin wurin ya kacame da ƙarar tafin jama'a, ga 'yan jarida da ke akkin ɗaujar hoto.Microphone aka miƙa masa dan yin jawabi.
A sanda Haris ya karb'i microphone ɗin, a lokacin wata ƙwalla me ɗumi ta sauƙo da ga idonsa na b'angaren hagu, Abba ya tuna, yau gashi ana lisaffo sunansa cikin masu nasara, amma baya raye, baya duniyar bare ya ga irin nasarar da ya samu.
A hankali dubansa ya kai kan ahalinsa dake zaune a kusa da kujerar da ya tashi, Rashidat, Zakiyya, Jude, Aja da ya koma yahaya, Hanam, Arya, Masarrat, Salwa, Al-amin, Khalil, Abu Tayyab, da Kamal wanda yazame masa babban aboki ayanzu.
Ji ya yi ya gama samun komai,baya buƙatar komai, gaba ɗayan ahalinsa na tare da shi, a shekaran jiya Rashidat ta yafewa Yahaya, komai ya cika, Abba ne kawai babu.
Hannunsa na dama ya kai ya share ƙwallar,sannan ya kai microphone ɗin bakinsa.
“Ina me matuƙar godiya ga ƙungiyar Grammy, sannan ina me godiya ga SSGF Record leble, da ma ita kanga C.E.O ɗin, wata Falaƙ, ina me godiya ga masoyana na duniya baki ɗaya, zan yi amfani da wannan damar wajen sadaukar da wannan lambar yabo ga matata da ɗana”
Wurin ya ƙara ruɗewa da tafe-tafe harda masu fito, Hanam ce ta miƙe, tare da riƙo hannun Arya dake tafiya kan ƙafafunsa, sanye yake da Baƙar suit irin ta jikin Uchenna, yayin da ita kuma take sanye da wata baƙar doguwar riga ɗinkin Empire.
Uchenna nabinsu da kallo har suka hawo kan stage ɗin, tsugunnawa yayi ya ɗauki Arya a hannunsa, sannan ya riƙo hannun Hanam dake ta jifansa da murmushi.
“Nagode Bannute,kinsauya rayuwata ta inda ban yi zato ba, nagode”.
Hanam ta ci gaba da kallonsa fuskarta ɗauke da murmushi, sai a yanzu ne labarinta ya cika, ƙaddarar ta tazo ƙarshe, ƙaddara da ta mata zab'i mafi kyau arayuwarta.
Abba ya tafi, amma bai tafi ba saida ya bar mata kyawawa  abubuwan da zasu ci gaba da faranta mata rai har bayan rayuwarta.
Uchenna ya ƙara kai microphone ɗin saitin bakinsa.
“I love you Hanam, and na sadaukar da wannan Award ɗin da na samu gareki”
Ya ƙarashe yana miƙa mata award ɗin, Hanam naci gana da murmushin da ke fitowa tun daga ƙasan ruhinta ta karb'i award ɗin, sannan ta rungumi Harees daga gefe, masu ɗaukar hoto suka ci gaba da sakar musu shi kamar ba gobe.

*House No.122, B3, Alaro city lekki, Lagos*
*08:00am*
Maryam ta fito daga ironing room, hannunta na dama riƙe da kayan data ɗebo a ciki.
Tris ta ja ta tsaya,sakamakon shigowar Tafida. Yau monday, kuma ɗazu yace mata ya tafi aiki, ke nan dawowa ya yi ?, Eh mana, ya dawo tunda kina ganinsa a gabanki, cewar wata murya a cikin kanta. Kayan hannun nata ta aje a kan sofa, dai-dai da ƙarasowar Tafida cikin falon.
Hannayenta ta ɗaga ta saƙalo su ta wuyansa, tana kallonsa, ya yinda shi kuma ya kewaye waist ɗinta, bayan ya aje ledar da yashigo da ita.
“Mantuwa ka yi ?”
Sai ya girgiza mata kai yana jingina goshinsa akan nata.
“Ba mantuwa na yi ba, kewarki ce ta isheni, sai kuma wasu kayan jarirai da na gani a hanya, shind na siyo”
Sai da ta ɗan ja da kanta baya ta kalleshi, dudu ma muntunsa nawa da fita?, kuma ita tun suka gano cewa tana da ciki ya fara siyan kayan yara, cikin da baima kai wata ɗaya ba.
“Yaya babyn mu?”
Se ta turo baki gaba tana ture shi tare da juya masa baya, Hannuna ta ji ya kewayo cikinta ta gaba yana janta jikinsa, kansa a kafaɗarta.
“Ina san babyn nan!”
Ƙara ture shi ta yi,amma sai ya sake kamata.
“Laifi na yi dan nace ina san ɗana ?”
Sai ta yi dariya. Ya tsira mata ido yana kallonta, zai iya rantsewa kan Maryam itace silar sauyawar rayuwarsa, tun bayan da ta shigo rayuwar tasa komai ya sauya, duk wani hali da yake ciki ya kau.
Farin ciki yake a ko da yaushe, duk da rayuwar ɗan adam ba'a rabata da ƙalubale, amma rayuwarsu ta hau hanya, a koda yaushe yana cikin ibadarsa, istingfari kuwa baya rabo da bakinsa, dan gani yake kamar shekarun da ya shafe a cikin sab'o ya yi su.
Babu wani super natural a jikinsa, shi ne,ai na hin shi. Ga kuma ƙaruwar ɗa da suke shirin samu. Jan Maryam ya kuma yi sannan ya furta.
“I love you”
A hankali, Maryam ta kwantar da kanta a ƙirjinsa.
“I love you too”
A yanzu bata da buƙatar komai, komai nata ya zama dai-dai, bata da wata buƙata se godewa Allah da take, dan zaman lafiya take da mijinta, ga 'yan uwanta da a koda yaushe suke kiranta ko ta kirasu su mata fatan alkairi.
Sosai Tafida ke kula da ita da buƙatunta, baya tsallke koda abu ɗaya da zata buƙata. Barin ma da aka samu cikin nan, hatta da aikin gidan hanata yi yake.
“Zo mu kalli kayan dana siyo”
Ya faɗi yana ɗagota, ta re da jan hannunta ya zaunar a kan kujera, zama ya yi a gefenta yana nuna mata kayan, ita kuwa dariya kawai take masa.
“Kinga wannan kalar zata masa kyau, dan nasan kamata zai iyo, kinsan sanda ina yaro bana jin magana, shi yasa na siyo masa wannan, tana da kauri, koda ana sanyi k8n hanashi fita, tofa ina me tabbatar miki da sai ya fita, idan wannan na jikinsa sanyi ba zai kama mana shi ba”
Dariya Maryan ta ci gaba da yi, tana ɗora hannunta a kan cikin nata.
Bata ankara ba sai jin sauƙar kan Tafida ta yi a kan cinyarta, yana kallin cikin idonta, yayinda itama take raba nata cikin nasa.
“Miriam Nagode da komai, musammanma wannab kyautar”
Ya ƙarashe yana ɗora nasa hannun a kan cikin nata, ita ma nata hannun ta ɗora a kab nasa tana ci gaba da kallonsa.
_“Allah alhamdulillah ” _
Kusan a tare suka furta hakan. A zuciyar kowannensu.

*Balu Thanda Village, Telangana state, South india*
“Kai Kartik ka dawo da ga nan”
Wani matashi dake tsaye da ga nesa yake ƙwalawa ƙaninsa kira, wanda yake kutsawa cikin dajin Kurabi.
“Ka yi haƙuri Yaya gani nan zuwa”
Kartik ya ci gaba da tafiya ta kan ciyayin dake ƙasa.
Ƙafafuwansa basu tsaya a ko ina ba sai a ƙofar kogon Manikandan, sai de kuma babu kogon babu alamarsa, tun wattani biyu da suka wuce jama'a suka nemi kogon suka rasa,kamar ma ba'a tab'a hallitar wani abu me kama da kogo a wurin ba.
Sai da ya gama kalle-kalle kalansa sannan ya juya ya bar wurin.
Kundali dake tsaye daga saman wata bishiya ta yi murmushi. Tun bayan abinda ya faru a waccan ranar ta nitsar da kogon ƙasa, dan wannan hasken da ya mamaye Manikandan da Subhu sai da ya kashe ko wannensu.
A lokacin ne kuma waɗanan masoyan suka suma, ita kuma ta ɗauko su da kanta ta dawo da su gidansu, sannan ta dawo kurabi ta nitsar da kogon Manikandan ƙasa.

***TAMMAT BIHAMDULLILLAH**
________**END**_______
Alhamdulillah Alhamdulillah
°°Assalamu alaikum.°°
Jama'a babu abinda zance da ku sai godiya, ga waɗan da sukayi ta bibiyar littafin YADDA ƘADDARA TA SO tun daga farko har ƙarshe, nagode na gode, Allah ya ƙara danƙwan soyyaya.
Kuraran dake cikin wannan rubutu nawa Allah ya yafemin, abubuwan da na rubuta daidai kuma Allah ya bamu ladansa ni da ki baki ɗaya.
Sai dai akwai waɗanda zan miƙa saƙon gogiyata gare su.
*Fatima Ahmad Isah(ke kam godoyarki ta da bance sis,)
*Sadi Sakhna(ina miƙa godiyata gareki)
*Hadiza D. Auta(Malamata ba, ina me godiya gareki)
*Dr. Muhammad (Allah ya saka da alkairi)
*Nafi'u Baturiya (ina godiya)
Dama gaba ɗaya jam'ar sa suka riƙayin comment, domin ƙwararamin gwuwa har muka gama, ina me matuƙar Godiya a gareku.
Albishirina gare ku kuma shine, zan rubuta muku sabon littafi na me taken LABARINMU. Ina me baku tabbacin ba zaku koka game da wannan labari ba, kude ku zuba ido domin jin labarin ZAID, ALIYU, MISHAL da kuma RABI'A.
I ❤ you WUJIGA-WUJIGA🤣🤣🤣.
Sai mun haɗe da ku a littafin LABARINMU.


Best regards🌸🌸
SALMA AHMAD ISAH A.K.A SAI KASKA CE✍️(Alƙalami makahon doki).

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 22 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

YADDA KADDARA TA SOWhere stories live. Discover now