YADDA ƘADDARA TA SO 3

28 4 0
                                    

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐شاء القدر⭐
©By Sai Kasna
*proud of my first novel*
*BABI NA UKU (3)*
HANAM POV.
Tsaye take a cikin babban kitchen ɗin gidan nasu, tana haɗawa aryasn elecare, wani nau'in abincin yara, tana bashine sbd mama baya isarsa, kumama yana ƙara girma dan haka take haɗa masa da sauran kayan abinci yara. Sanye take da green cargo pants, sai wata baƙar shirt mara hannu, ta ɗaure gashin kanta da rubber band.
Fitowa tayi daga kitchen ɗin tana fifita abinda ta zuba a cikin wani sabon bowl da taga a kitchen ɗin, a lokacin masu aikin dafa abinci na gidan suna jera abinda suka dafa a kan danning table, waje ta samu tana aje bowl ɗin, yayinda take amsa gaisuwar da masu aikin suke mata.
Dakinta ta koma wanda yake haɗe da ɗakin aryaan ɗin, ta shiga ta sameshi zaune cikin munchkin baby cradle ɗinsa yana jujjuyashi, yayinda yake tsotsar pacifier ɗin dake bakinsa
"aaaah, aryaan ammy"
Ta faɗi tana masa wasa tareda ciroshi daga cikin baby cradle ɗin, ta sabashi a kafaɗa, wayarta dake cikin aljihunta ce ta shiga ringing ta sa hannu ta ɗauko wayar, ganin abbabnta ne yasa tayi murmushi, ta ɗaga kiran ta gaisheshi, baya ha amsa yace
"maman babanta, mamarki ta...." tun kafin ya karasa ta katse shi
"la abba hiya mana immi"
( a'a abba ita ba mahaifiyata bace)
"to matata, shikenan?"
Ta gyaɗa masa kai kamar yana gabanta sannaan shima yaci haba
"ta kawo min kararki, wai kin mari ɗanta"
Ta ɗan gyara riƙon da tayiwa arya a hannunta da babu wayar
"eh hakane"
"to maman babanta me yasa ?"
"abba arya ya kira da shege, ni kuma na gaza jurewa shi yasa na mareshi "
"to maman babanta a dinga haƙuri dai, kinga shi yayanki ne, ya girmeki, kuma ko ba haka ba shi namiji ne, a dinga ƙoƙarin sarrafa fishi"
"umhm" daga haka kuma suka ɗan tattauna daga bisani sukayi sallama bayan ya faɗa mata cewar gobe zai dawo, ta aje wayar sannan ta fito daga ɗakin zuwa ƙasa.
Zama tayi ta shiga bashi baby feed ɗin tana masa wasa, zuwa lokacin mutanen gidan sun fara fitowa, arya sai ƙyal-ƙyala dariya yake har haƙwaransa biyu na sama da suka fara fitowa na bayyana
"kutumar dumadu"
Hanam ta tsinkayo muryar hajiya mero a bayanta na ƙunduma ashar bata ko juyo ba taci gaba da yiwa ɗanta wasa tana bashi abincin
"ya sa kika damawa shegen ɗanki abu a cikin sabon kwano na ?, ko ke kika siyomin ?"
Nan da nan hanam ta tsuke fuska ta aje bowl ɗin ta juyo ta fuskanci hajiya meron da kyau
"kikace kwanan ki, yau ai ni inajin duk cikin ku babu wadda tazo koda da cokaline gidan nan, ko waccen ku haka aka wanko kafarta ziƙa-ziyau aka kawota, kuma kina zancen naki tunda ya riga ya shigo cikin gidan ubana ya riga ya zama mallakinsa, kuma ma faɗa min sana'ar me kike da kika samu kuɗin siyan bowl ɗin ?..... babu ko ?, nasan ai kiɗin ubana ne, dan baka babu ruwanki da ni"
"lalle hanam wuyanki yayi kauri, yanxu ni kika dubi ƙwayar idona kike faɗa min wannan maganganun?.....naji ni haka ziƙa-ziyau aka kawoni gidan ubanki, me gidan uba, shiyasa naga taki uwar ta gudu ta barki cikin zanin goyo"
A fusace hanam ta miƙe tana kallon cikin idon mero
"mero bari kiji na faɗa miki, ni bani da uwa abba shine uwata kuma shine ubana, waccan matar ba uwata bace, watace can da ban, kuma magana ta ƙarshe kada ki kuskura ki ƙara kiran ɗana da shege, ɗana ba shege bane yanada uba, kuma nice ubansa, fatan kin fahimta ?"
Tana kaiwa nan ta bar wajen bayan ta ɗauki ɗanta.
MARYAM POV.
*Da misalin karfe 7:30am*
Maryam na zuba musu abinci a kwanuka, dan hassan da hussain da muhsin duka sun shirya domin zuwa makaranta.
Abincin ta gama zubawa tazo ta aje musu a gabansu.
"yaya ke yau bazakije makaranta bane ?"
Hassan ya tambaya ganin sam ba tayi shirin zuwa makarantar ba
"aa hassan bazanje ba, registretion mukayi ai"
"oh na gane"
"au ni kin tuna min ma, idan kin gama ki kiramin kawu usman ɗin nayi masa maganar kuɗin" cewar maanmu.
Kawu usman shine babban yayan su maanmu, kuma tun lokacin da tijjani ya tsiri rashin mutunci shine ya dawo yake kula da maanmun da yaran nata, kuma yanzu haka shine yake ɗaukar dauyin karatun maryam ɗin, dan a yanzu haka ta gama ND 1, zata shiga ND 2, kwana nan suka gama siwes ma.
"to, in anjima zanje gidan su badar, jiya nace mata zanje amma banje ba...."
bata ko gama rufe bakinta ba saiga sallamar badar, tana shigowa ta gaida maanmu ta shiga aikawa maryam sakon harara
"badariyya zo muci taliya"
"aa wallahi maanmu, a ƙoshe nake, dade ɗumame ne"
"ke wai yau bazakije makarantar ba ?"
"ban sani ba"
badar ta faɗi tana kawar da kai
"ke kiyi haƙuri wallahi jiya aiki ne ya riƙeni shiyasa banzo ba"
"hassan kuyi sauri ku gama ku miƙamin yaron nan makarantarsu, kar ya makara su dakar min shi"
"ai da zasu dakeshi ma da ba haka ba" cewar hassan yana wurga masa harara
"wai dan allah me auta ya tare muku ne ?"
"babu wallahi kawai muguntace irin tasu" cewar maryam.
Bayan sun gama cin abinci su hussain suka fita suda muhsin, su suna ss3 ne a makarantar government day garko, yayinda shi kuma muhsin yake primary 3 a garko islamiyya, duka makarantun nasu basu da nisa da gida.
"ke tura min sabbabin vedios ɗin"
*
cewar maryam yayinda suke zaune a ɗakin maryam ɗin
"ke aliyu ne zai zo jibi"
cewar badar, aliyu shine saurayin badar, kuma a yobe yake da aiki, amma ainahinsa ɗan hadejia ne, aikine ya kaishi can
"to allah kawo shi lafiya"
"girki nake so ki masa"
"badar, ina rabaki da kiwon killa kina killa ta haihu, ba wai girkin ne bana san miki ba, tsorona duk ranar da kukayi aure yace ki masa girki irin wanda kika saba masa lokacin kina budurwa, kikayi bai kai nawa ba yaya zakiyi ?"
"ke rabu dashi wallahi, ni bazan iya ba, kawai ki masa"
"shikenan, me za'a masa ?"
"kinga last time fried rice aka masa yanzu kawai a masa awara me miya"
"shikenan, amma ki kawo da wuri, dan nima jibi zan raka anti fati gidan auren 'yan uwan mijinta"
"ai shikenan"
badar ta faɗi tana duba mata sabbabin vedios ɗin girkin data samo mata a tiktok.
TAFEEDAH POV.
zaune yake a mazaunin me zaman banza, yayinda abokinsa muktar yake tuƙa motar, dan dama shine yaje ya ɗauke shi a airport bayan ya sauƙa a kano, idanunsa sanye da wani sun glasses, ya boye kalar ƙwayar idansa data koma ja tunda safe, duk da muktar yasan halin dayake ciki amma baya san ya ɗagawa kowa hankali.
Ya ɗora hannunsa akan bakinsa yana nazari, nazarin abinda zai iya faruwa a hadejia, yanzu ya shiga cikin wani irin hali da baƙin ruhin dake cikinsa yake tashi akai-akai, a da sai yayi wata da wattani bai tashi ba, amma a kwanakin nan abun ya ta'azzara.
muktar ya d'an kalleshi da gefen ido
"tunanin me kake ?"
a hankali ya sauke hannun daya ɗora akan bakinsa ya juya yana kallon window, sai ya lura da har sun shigo ƙofar garin hadejia ta farko
"babu komai..."
"aa tafeedah, akwai wani abun"
hakane, kamar yanda muktar ɗin ya faɗa akwai wani abun, jikinsa ne ke bashi cewar akwai wani abu dazai faru, to amma taya zai faɗa masa cewa jikinsa na bashi cewar wani abu zai iya faruwa.
Bai amsa shi ba, sai hannu dayakai ya cire sun glasses ɗin dake idonsa, a lokacin suka karaso dai-dai round about ɗin na malam zangi, babban round about ɗin hadejia.
Tun daga ganin lambar motar matasa suka gane cewa TAFEEDAH ya shigo gari, tun bayan daya dawo daga india, aka naɗa shi akan sarautar mahaifin sa ta TAFEEDAH, yayi hawan doki matasan garin dama ƴan mata suka ganshi, shikenan suka samu abun magana, kaf ƴan matan garin haɗejia babu wadda bata san tafeedah ba, samari na matukar sansa, hakan tasa a duk lokacin da za'ayi hawan sallah ko na kilisi dakarun tafeedah sunfi na kowa yawa, sbd rabi da kwatan matasan had'ejia suna sansa, Allah ya masa wannan farin jinin, ga kuma tarin ƴan matan da zaka gani a wajen idan har yayi hawa, kowa zaka tambaya zai baka labarin tafeedah a haɗejia.
Juyowa yayi ya kalli muktar da jajayen kwayoyin idonsa, muktar ɗin ma ya jiyo ya kalleshi, saida gabansa ya faɗi yayinda yayi arba da kalar idon nasa, duk da ya saba ganinsa da idan kwayar idon nasa ta sauya, amma na yau yafi ja, jan har yayi yawa.
"tafeedah kayi addu'a"
yayi murmushi me ciwo yana kawar da kai
"itace abun da ako yaushe nake sanyi, amma kuma daga zarar na shiga irin wannan halin bana iya yinta, bakina nakeji yamin nauyi, hatta da harafi ɗaya na larabci bana iya furtashi"
muktar ya girgiza kai cike da tausayin abokin nasa, wata iriyar rayuwa yake me cike da ban tausayi.
Hannunsa ya mika baya, ba tareda ya ta6a bottle ɗin ruwan dake kan kujerar baya ba, bottle ɗin ta taso da kanta zuwa cikin hannunsa, ya dawo da hannun nasa gaba riƙe da bottle ɗin ya buɗe ya kafa kai yana sha, zuwa yanzu sun shigo cikin kofar garin had'ejia, kuma sun hau titin fada, so yake ya samu yayi yaƙi da sheɗanin ruhin nasa kafin su karasa fada.
Bottle ɗin ya aje a gaban motar, ya dafe kansa da hannuwansa, da muktar yaga haka sai ya shiga tofa masa addu'a duk wadda tazo bakinsa, bayan ɗan wani lokaci ya jiƙe sharkaf da gumi, har ya jiƙa rigar yadin dake jikinsa.
A hankali ya ɗago ya jingina da jikin kujera, yanajinsa ya dawo dai-dai, shed'anin ruhin nasa ya tafi, ƙwayar idansa ta dawo ainihin blue ɗinta.
Da haka suka karasa katafariyar fadar garin hadeji, hadejia ginsau birnin doki, ta ɗan abubakar sarki babba. Inji ja'e haɗejia.
A gate ɗin farko wanda aka tanada domin aje motoci muktar yayi parking, suka fito a tade, muktarb ya ɗauka masa jakar dayazo da ita, gaba ɗaya harabar fadar a cike take fal da jama'a, sbd bikin da za'a gudanar na yar sarki gimbiya amina,isarsa ba jimawa labari ya karaɗe fada akan tafeedah ya shigo garin.
Kofa ta biyu suka zo wucewa dogarai da hadimai sai kwasar gaisuwa suke, duk da shi tafeedahn baya san hakan sam, shi baya d'aukan kansa daban da kowa, gani yake shi dai-dai yake da kowa, amma haka ƙa'idar take, dan haka babu yanda zaiyyi face ya amsa, su kuma suna gaisheda shine sbd suna sansa, dan yafi yarima ɗan uwansa halin arzik'i.
Daga wannan gate na biyu suka shiga soro na farko a fadar wanda ya kasance soron masu gadi da tsaron fada a da, amma yanzu babu kowa a wajen sai masu wucewa, daga soron farko sai na biyu wanda shi kuma ya kasance soron malamai a zamanin da, wanda shima a yanzu babu kowa, sai kuma soro na uku wanda shi kuma ya kasance na ƙoramai, sai soro na huɗu wanda yake d'auke da wata babbar karaga ta sarkin hadejia, daga kasan kujerar wani lallausan yashine zube, sannan kujera a samansa, a duk lokacin da sarki ya sauko daga sallar jumu'a yakan tsaya a wajen ya zauna ayi fadanci sannan a tashi, daga shi kuma sai soron bayi, wanda kuma a yanzu yake ɗauke da tsofaffun bayi na da, wanda har yanzu akwai sauransu, gaba ɗaya saida tafeedah yabisu ya gaisar sunata saka masa albarka sannan ya wuce, daga nan kuma wani tamfatsetsen filine, wanda ya kunshi hanyoyi hud'u, daya wadda zata sadaka da 6angaren matan sarki da kuma turakar sarkin, ɗaya kuma wadda zata kaika ai nahin majallisun sarki, sai kuma wadda zata kaika 6an garen bayi da kuyangu na fadar, Sai ta murin dominan sarki.
Nan ɗin ma a cike yake da jama'a haka suka yanki hanyar da zata sadasu da 6an garen matan sarki, wata uwar doguwar tafiya suka yanka kafin suka iso ainahin inda bangarorin matan sarkin suke guda uku, wanda yafi kowanne girma suka nufa, kowanen gini akwai beni, amma kuma kuma irinsu ɗaya sai na tsakiyarsu daya yafi girma.
Aminttaciyarta suka samu tana fitowa daga ƙofar shiga, ta gaishe su tareda faɗi bari tai musu iso, muktar sai ya tsaya yana faɗin
"na gama nawa aikin, na kawoka gida lafiya, dan haka sai anjima idan ka samu fitowa"
tafeedah ya juyo yana kallonsa, sai kuma ya ta6e baki cikin ɗaga kafaɗa, dan muktar ba balo bane, shi ɗan gidane, ya karbi jakar tasa sannan ya saka kai cikin kofar parlon, tuntuni an masa iso wajenta, dan haka ya saka kafarsa cikin parlon kai tsaye daga parlon farko ta wuce na biyu, a nan yayi birki, kamshin turaren wutane ya fara ziyartar hancinsa, kafin a hankali ya fara bin parlon da kallo, baiga kowa ba sai himilin tarin kayan abinci akan coffee table, wanda yake da tabbacin nasa ne, yayi murmushi yana juya kai kafin a hankali ya ƙaraso cikin parlon saida ya shiga ya zauna, sannan ya lura da ashe bai rufe kofar ba, dan haka yayi nuniga kofar ya motsa hannunsa nan take kofar ta rufe kanta tareda motsawar hannun nasa.
A lokacin ne kuma ta shigo cikin parlon, bakinta ɗauke da sallama, ya ɗaga kai ya kalleta yana mata murmushin me tsada, wanda ba a ko yaushe yake irinsa ba, dan har hakwaransa na bayyana, itama murmushin take har ta ƙaraso ta zauna a kujera kusa dashi, cike da girmamawa ya gaishe ta, sannan suka ɗan ta6a hira kaɗan, dan ita izzar mulki ta mayar da ita muskila, shi kuma jinin mulki dake yawo a jikinsa yasa baya zantuka barkatai, abici ta fara gabatar masa sannan ta tashi ta bashi waje yaci abinci.
Fulani khadija kenan, matar sarkin hadejia alh Abdullahi abubakar masu (c.o.n) shugaban hukumar sarakunan jahar jigawa, itace matarsa ta farko,bayan ita yanada wasu matan har guda biyu, fulani sadiya itace me bi mata sai kuma fulani usaibatu, fulani khadija sau ɗaya ta ta6a haihuwa, itama kuma bayan sun shafe shekaru samada ashirin ita da me martaba da aure, tukunna ta samu, inda ta haifi ƴarta mace me suna Nadra.
Ita kuma fulani sadiya yaranta huɗu a gidan, habibu shine na farko, kuma shine babba a cikin ƴaƴan me martaba, wanda yake riƙe da sarautar galadima a yanzu, hakan tasa ake kiransa da sunan, ko kuma ace yarima, sai maimun wadda tayi aure suna zaune da mijinta a buja, sai amina da za'ayi aurenta yanzu, sai autansu nabil wanda ya kasance karamine bai wuce 10 yrs ba.
Fulani usaibatu kuwa yaranta biyu, abbas da kuma amra, suke nan iyalan gidan me martaba alh Abdullahi abubakar masu (c.o.n).
Abincin ya buɗe ya ɗan ɗiba kaɗan domin baya jin yunwa, idan kuma yace bazai ci ba fulani bazataji daɗi ba.
Nadra ce tayi sallama tana shigowa cikin parlon, wani uban tsalle ta saki haɗi da ihu yayinda tayi arba da tafeedah zaune a parlo yanacin abinci.
Bata san da Labarin zuwan sa ba, yanzu haka tana garden ne taji wasu bayi suna hirar wai tafeedah yazo, shine tace bari tazo ta ganewa idonta, kansa tayi da gudu ta rungumeshi, ya aje plate ɗin dake hannunsa shima ya riƙeta yana murmushi me kama da dariya
"hamma yaushe ka zo ?"
ta faɗi tana sakinsa tareda zama a gefensa
"jiya na zo"
Tayi dariya, inda sabo ta saba da wannan halin na tafeedah, ya iya mannawa mutum magana, idanta ne sauƙa akan ƴar hadejian dake kwance a gefen fuskarsa, kusa da kunnensa gefen sajensa, ƴar hadejia tsago ukune sirara da haifaffun haidejia kanyi a gefen fuskarsu, kusa da sajensu wajejen kunnensu, hakan tasa aka sanya mata 'yar hadejia
"laa hamma kalli 'yar hadejan ka, ta kusa bacewa, dama nice, allah ba karamin cutar mutane suke ba da suke musu wannaan ƴar hadejan"
tafeedah ya kai abincin bakinsa yana murmushi, kowani ɗa dake fadar inhar ya haɗa jini da fadar walau mace ko na miji to sai ka sameshi da wannan zane, kuma bama fada kawai ba har mutanen gari.
Hannunsa ya kai ya tura sumar kansa baya, bawai dan ta sauko masa kan goshi bane, saide dan hakan ta zama ɗabi'arsa a duk lokacin da kansa yake babu hula.
"to ko zamuyi changing face ?"
"aa hamma rabani, ni da irin fuskarka ai duka samarin hadejia dawowa zasuyi suce suna sona, kamar yanda kaima kaf ƴan matan hadejia ke sanka"
maganar tata ta bashi dariya, amma kawai sai yayi murmushi
"au haba ?, ni ɗin suke so kuma ?"
"eh mana, akwai wata class mate ɗina ma datake yawan damuna da zancenka, tace tafeedah kaza, tafeedah kaza, har cewa tayi idan tazo bikin nan dan Allah na haɗaku ku gaisa, nace mata kanajin hausa ta ƙaryata ni, wai aikai indian ne taya zaka iya hausa"
"kaimin jakata bangarena pls, i am tired of wannan surutan naki"
nadra ta miƙe tana jan jakar tasa dan ta sani yayan nata baya san surutu dayawa, hakama mumzzy, gashi kuma ita allah yayita da magana.
🌸-SAI KASKA CE-🌸

YADDA KADDARA TA SOWhere stories live. Discover now