YADDA KADDARA TA SO 22

28 3 0
                                    

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Wannan naki ne Lilin Mama*

*BABI NA ASHIRIN DA HUƊU (24)*

HANAM POV.
“Wai yanzu ke miye mafitar auran nan ?”
Falaq ƙawarta ta tambaya, Suna zaune ne a office ɗin falaq ɗin, ita mawaƙiyace kuma yar kasuwa. Hanam ta gyara riƙon Arya dake hannunta sannan tace.
“Ban sani ba Falaq, ban sani ba, tun bayan faruwar auren nan ban ƙara samun damar magana da Abba ba, bamu samu wani zama ba”
“Ai kuwa ya kamata ace kije ki sameshi kuyi magana, dan bazai iyu ba, taya za'ayi ki ci gaba da zama da auren Cristian, yau kusan wata ɗaya fa!”
“Hakane, ba matsala zanje na same shi ɗin, amma kinsan me Falaq?, da ace Uche musulmi ne da ya morewa rayuwa”
Falaq ta gyara zama tana faɗin
“A'a fa Hanam, karfa ki faɗa, tam”
Hanam ta watsa mata harara
“Ban gane kar na faɗa ba, kinji nace ina sansa ?, kawai halayensa masu kyau ne suke burgeni, he is very kind wallahi”
Falaq ta gyaɗa kai.
“Gaskiya kam dama Uchenna ba daga nan ba, kinga fa tun muna makaranta yafi mazan class ɗinmu amma ya mayar dasu abokai, kuma sam bashi da abokin faɗa”
“Falaq bari na tashi na tafi, gobe zanje na yi magana da Abba”
Ta ƙarashe maganar tana miƙewa, itama Falaq ɗin miƙewar ta yi, suna hira har suka fita daga ƙaton mall ɗin falaq ɗin.
Bayan ta koma gida ta yiwa Arya wanka sannan itama ta yi, ta kawo shi parlo ta aje sannan ta koma kitchen dan ta samamusu abin da zasu ci, har yanzu bata fara girki da Uche ba, amma kuma Aryaan ya kama abinci a kwanakin nan.
Tana ɗora tukunya akan stove ɗin gas taji Arya ya ƙwalla ƙara, ko gas ɗin bata samu damar kunnawa ba ta futo a ruɗe, ta sameshi zaune kusa da socket ya ɗaga hannunsa sama yana kuka, hakan ke tabbatar mata wuta ce ta ja shi.
Da sauri ta ƙarasa inda yake a zaune ta ɗauƙeshi tana rarrashin sa, amma yaƙi hin shiru.
“Me kika masa ne ?”
Taji muryar Uche daga bayanta, ta juya bakin ƙofar ta kalleshi, kallo ɗaya zaka masa kasan cewa ya gaji, dan dawowarsa daga aiki kenan.
“Wuta ce ta ja shi”
Wata uwar zabura Uche ya yi sai ganinsa ta yi a gabanta, briefcase ɗin ma daya shigo da ita ya cillar a bakin ƙofa, yanda yake jin ɗan nan a ransa Allah ne kaɗai ya sani.
Kuma tun da ma yana san yaron bare yanzu da suka haɗa gida ɗaya. Wuta ya ja yaron amma shine take wani ce masa wai wuta ta ja shi, babu ma wata damuwa a tare da ita.
Fincike yaron ya yi a hannunta ya shiga dudduba jikinsa yana faɗin
“To wai duk kina me kika bari wuta ta ja shi ?!”
Cikin faɗa-faɗa yake maganar ga kukan Aryaan na tashi kamar da ake zigashi, Hanam ta tsaya tana kallonsa ganin duk yanda ya ruɗe, ko ita bata ruɗe haka ba, har wata zufar tashin hankali yake.
“Mstwwww, asibiti zamu tafi”
kuma yana kaiwa nan bai tsaya jiranta ba ya fice.
Kitchen ta koma taci gaba da girkinta, a kai-akai take murmushi, tana jin daɗin yanda Uche yake kula da su ita da ɗanta, yana nuna dumuwarsa a kansu, wani abu da ya yi ƙaranci a rayuwarsu ita da Aryaan ɗin, bayan Abba da Baabaa ko Baba bata jin akwai wani me san su bayan shi.
Tana parlo tana cin jallof ɗin taliyar data dafa ta ji ƙarar tsaiwar motar Uche, tana zaune a gun suka shigo, ta juya ta kallesu ba tare da ta amsa sallamar Uche ba.
Mutumin da aka fita dashi yana kuka wiwi shine ya dawo hannunsa rike da chocolate ga wasu kayan wasa a hannunsa se dariya yake.
Uche ya ƙaraso ya miƙa mata Arya sannan ya zube akan kujera yana meda numafashi, Allah ya sani yau ba ƙaramar gajiya ya yi ba, ga yunwar da yake ji, kamar daga sama ya ji muryar Hanam.
“Kaje kitchen ka ɗauki abincin ka”
Wani abu da be tab'a faruwa ba a zamansa da ita gaba ɗaya, yau sun kusa wata ɗaya da aure amma bata tab'a dafa abinci da shi ba sai yau, ɗagowa da kansa ya yi ya kalleta, ba shi take kallo ba, Arya ma take  cirewa riga, yasan de ba za tayi wa Arya magana haka ba, kenan dashi take.
“To nagode”
Miƙewa ya yi ya tafi ɗakinsa saida ya yi wanka sannan ya sauƙo ya ɗauko abincin ya ci, wani abu sabo, wanda bai tab'a samu ba a zamansa da Hanam.

YADDA KADDARA TA SOWhere stories live. Discover now